Friday, 29 November 2024

Makomar Rayuwar Ku A Hannun Ku

Tura Wannan Zuwa Ga
A can wani gari an yi wani tsoho ma'abocin hikima da ilimi, duk tambayar da aka yi masa ya kan bayar da amsarta kaitsaye babu wata tantama, hakazalika manyan mutane da 'yan siyasa, attajirai da kowa kan je gare sa da buƙatar shawarwari ko tambaya ya kuma ba su amsa yadda ya kamata.

Makomar Rayuwar Ku A Hannun Ku
Hoto: Read the tale


Marubuci:- Ibraheem Aleeyu


To da akwai wasu yara guda uku masu matuƙar ƙiriniya, hatsabibin cikin su shi ne sani, kullum su kan ɗauki lokaci suna tunanin yadda za su ƙure wannan tsoho ta yadda zai gaza wajen ba su amsar tambayar su, amma sai su gama tunanin su tare da samar da tambaya mafi wahalar amsa su nufe shi da ita amma sai su ji ya ba su amsa yadda ya kamata.

Wata rana suna zaune sai sani ya ce "Ai kuwa yau na gano yadda za mu ƙure wannan tsoho ba makawa yau ba zai tsira ba."

Suka tambaye sa me kuwa ya gano, ya ce "Abin da zan yi shi ne zan samu ƙaramin tsuntsu na riƙe shi a hannuna, idan amsar sa ta zama a raye sai na damƙe hannun tsuntsun ya mutu, idan kuma ya zama amsarsa ita ce a mace sai na sake shi ya tashi."

Suka aminta da wannan dabara ta sani suka samu tsuntsu suka nufi wannan tsoho, tun kafin su isa wannan tsoho ya gansu, kuma ya ga yadda fuskokin suke ƙawace da zaƙuwar isowa gare shi sai ya fahimci lallai da akwai wani abu a ransu, ya jira har suka iso.

Sani ya dube shi ya ce "Wannan tsuntsu ne a hannuna, shin a raye yake ko a mace?".

Tsoho ya yi murmushi ya ce "Sani ai amsarka a hannunka take."

Me ka fahimta da wannan labari ɗan uwa? 

RAYUWAR KA A HANNUWAN KA TAKE

Rayuwarka da yadda za ta kasance a gaba tana hannunka, kai ne za ka yankewa kanka kasancewa wanda ya yi nasara ko akasin haka, ba wai iya nasarar duniya ba kaɗai, har nasararka a gobe ƙiyama.

Kai ne za ka shiryar da kanka ta hanyar barin wasu munanan halayenka ba wai jira za ka yi har sai Allah ya shirye ka ba.

Abin da ya kamace ka a kodayaushe shi ne tunani da nazartar halin da kake ciki, shin hanyar rayuwar da kake kai hanya ce mai ɓillewa ga nasara ko akasin haka? Ya za ka canza zuwa ga halaye da za su isar da kai ga nasara? Me kake son zama kuma ta ya za ka samu nasara? Wanne tsari ne zai kai ka ga nasara (Plan)? Da sauran makamantan irin waɗannan ne ya kamata su dinga yawo a zuciyarka a kodayaushe domin dai na sani kowa ya na son tsintar kansa a yanayin farin ciki, da jin daɗin rayuwa duk kuwa waɗannan kai da kanka za ka samar da su ga kanka, walau kai talaka ne ko akasin haka.

Allah ya taimake mu Amin.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user