Showing posts with label Filin Tunatarwa Da Fadakarwa. Show all posts
Showing posts with label Filin Tunatarwa Da Fadakarwa. Show all posts

Sunday, 24 August 2025

Gaskiya Magana Kan Kalmar Zafin Nema Ba Ya Kawo Samu

Gaskiya Magana Kan Kalmar Zafin Nema Ba Ya Kawo Samu

Idan ana so a kwantarwa mutum hankali, sai ana masa wannan karin magana: “Zafin nema ba ya kawo samu.” Amma idan ka tsaya ka yi tunani, za ka tambayi kanka, “to, me yasa Allah ya ce tashi in taimake ka?”


Gaskiyar magana kan kalmar zafin nema ba ya kawo samu
Hoto: Ridofranz/Getty images

Marubuci:- Dahiru Aliyu Musa


Gaskiya ne akwai lokaci, akwai rabo, kuma Allah yana ba wa wanda ya ga dama a lokacin da ya ga dama. Amma hakan ba yana nufin ka haƙura da ƙoƙari ba, ko ka zauna jiran abin ya faɗo maka daga sama. Sau da yawa, hanyar da Allah ke amfani da ita wajen kawo maka abin da aka rubuta maka ita ce ƙoƙarinka.


Samu yana zuwa ne ga mai neman sa, kamar yadda nasara take zuwa ga mai jurewa wahala da dagewa.


Ka duba manoma. Suna shuka iri da kyau, suna yin aikin noma daga safe har yamma. Su ba sa cewa “idan rabonmu ne za mu girba.” Sun san aikin su shi ne shuka, Allah kuma shi ne mai sa amfanin ya fito.


Ka duba ɗalibai. Ba su zauna a gida suna addu’a kawai su ce “idan rabona ne zan ci jarabawa.” Suna karatu, suna nema, sannan su dogara da Allah don ya sa musu albarka.


Ko ’yan kasuwa. Ba su zauna suna jiran kasuwa ta kawo musu kuɗi ba. Suna tashi da safe suna neman dama, suna jurewa, sannan suna sa ran Allah ya saka musu nasara a neman su.


Don haka, wannan karin magana tana da ma’ana, amma ba cikakkiya ba ce. Abin da ya dace shi ne ka dage, ka nema, sannan ka bar sakamakon a hannun Allah.

Saturday, 15 March 2025

Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba

Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba

1. Kada ka raina iyayenka. Ba za su dawwama ba, ka kula da su matuƙa.


2. Idan ka gyara kanka, kamar ka  gyara iyalinka. Idan ka gyara iyalinka, kamar ka gyara al’umma ne, idan ka gyara iyalinsa kai ma ka gyara ni ma na gyara sai al'umma ta gyaru.


Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba
Hoto: Getty Images

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


3. Namijin da ya iya fin ƙarfin  sha’awarsa yana da cikakken iko kan rayuwarsa.


4. Kunya ta ɗan lokaci ce, amma nadama tana dawwama. Ka fi son fuskantar kunya da wuri a kan ka yi nadama daga baya. Ka yi aiki tuƙuru kada ka ji junyar wulaƙancin jama'a kan sana'arka.


5. Namiji mara manufa yana rayuwa ne kawai don shagaltuwa da abubuwan banza. Kamar zuwa fati, shaye-shaye da neman mata.


6. Ka guji mutanen da ke ƙin jinsin da suka saɓa da nasu; suna da matsala a zukatansu.


7. Ka saurari tsofaffin da suke farin ciki, sun san abin da suka gani a rayuwa.


8. Ɗa’a (hazaƙa) ta fi ƙwazo (motsi zuciya). Ka dinga yin abin da ya dace, koda ba ka jin daɗin aikata shi a ranka.


9. Idan kana jin buƙatar burge kowa, to kai bawa ne gare su.


Duk lokacin da kake son burge mutane za ka zama kamar bawansu . Duk abin da suke so shi za ka aikata ko ba daidai ba ne. Hakan ya sa malamai suka zama karnukan 'yan siyasa.


10. Mafi yawancin baƙin ciki a cikin maza na faruwa ne sakamakon rashin manufa a rayuwa.


Kaso 90 na maza suna faɗawa wahala ne da ƙunci da talauci saboda rashin manufa da gina kasuwanci ko aiki tun suna ƙananu.


11. Idan namiji yana rashin kunya ga uwarsa, kada ki amince da sh, ba zai girmama ki ba.


12. Namijin da ya saba da jin daɗi mara amfani yana lalacewa. Dole ka saba da wahala don ka bunƙasa.


13. Halayen mace suna ƙarfafa namiji, haka nan kuma halayen namiji suna ƙarfafa mace.


Idan namiji ya samu mace mara manufa sai ta rage tasa manufar da kaso 70 haka idan ya samu mai manufa sai ta cike shi ya zama mai  ɗari bisa ɗari.


14. Rayuwa ba za ta sauƙaƙa ba, kai ne kawai za ka ƙara ƙarfi don fuskantar ta.


15. Babu wanda ya taɓa zama babban mutum ta hanyar zama kan kujera yana kallon fina-finai da tsalle tsakanin facebook da tiktok tsawon wuni/yini.


16. Namiji yana samun mafi yawan farin ciki ne lokacin da yake gina abin da zai bari bayan ya tafi.


17. Kada ka saurari marasa fata da ke cewa rayuwa tana muni idan shekaru suka kai 40. Idan ka dage, kana inganta ta fiye da matashin ɗan shekara 20.


18. Kasance namijin da ke da nutsuwa lokacin da kowa ke firgice aka rasa mene ne mafita. Yi ƙoƙari ka nemo mafita.


19. Gwamma ka yi kuskure a kokarinka fiye da ka zauna ba ka yi komai ba.


20. Yin dariya da mai kiba a dakin motsa jiki kamar yin dariya da marasa gida ne don yana neman aiki. Wannan rashin tunani ne.


21. Zama cikin yanayin wajen da yake shiru da shan iska yana rage damuwa fiye da shan magungunan maye da giya.


22. Koyi yadda za ka karɓi suka ba tare da ka fusata ko ka mayar da martani da zafi ba.


23. Daina kallon batsa, za ka ji daɗin rayuwa kuma ka fi zama namiji nagari.


24. Ka nemi abin da kake so ta hanyar aiki da ƙoƙari, kada ka yarda da son cin banza da neman alfarma.


25. Ka tuna cewa wasu maza suna da kirki ba don suna da hali mai kyau ba, sai don sun kasa tsayawa tsayin daka wajen kyautatawa mata har matan ke juya su kuma suke ganin mazajen nasu masu kirki ne.

Sunday, 26 January 2025

Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya

Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya

Idan kana fama da damuwa ko rashin walwala a zuciyar ka, ka yi abubuwan nan guda 3.


Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya
Hoto: Dilok Klaisataporn

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


1. Idan kana da 'yan uwa ko aboki na ƙwarai a wani gari daban, ka kai masa ziyara.


Ma'ana dai ka yi tafiya yadda za ka canja muhalli na wani lokaci.


2. Idan akwai wani abu da ka sa a gaba, kuma ya gagara samuwa, ka watsar da wannan buƙatar, ka haƙura da ita.


Ka kuma yadda ba kowacce buƙata ce take samuwa ba.


Idan kana da hali na wasu 'yan kuɗaɗe, ko kuma wani abu mai amfani, ka farantawa wani rai, da wata kyauta mai ban mamaki.


Insha Allah waɗannan matakai idan ka bi ɗaya daga cikinsu, ko duka ukun, za ka samu sauƙi da maslaha a zuciyar ka.


Allah ya magance mana dukkan damuwar mu, ya kawo mana sauƙi da rangwame Amin.

Saturday, 18 January 2025

Nasarar Dare Daya

Nasarar Dare Daya

Akwai wani kuskure da muke yi, Matashi yana fara samun kuɗi, ko wata dama, maimakon ya yi amfani da wannan damar wajan ƙara gina sana'a ko kasuwancin da yake yi, a'a, sai ya fara tarawa kansa maƙiya na babu gaira babu dalili, shi ne kullum habaici a status; "sun ƙi, Allah ya so.", "Lokacin mu ne, yen yen yen yen....", Kwarai! Lokacin ka ne, amma na faɗuwa, domin da wannan halin babu inda za ka je.


Nasarar Dare Daya
Hoto: Pixel

Marubuci:- Abdulfatah Yakubu


Kada nasarar dare ɗaya ta ruɗeka, rayuwa mataki mataki ce. Idan Allah ya yi niyyar buɗe mana ƙofofin alkhairi dubu, ba lokaci ɗaya yake buɗe mana su duka ba, zai buɗe mana ƙofar farko ne, alla bashshi mu kuma sannu a hankali ta hanyar inganta kai, da alaƙar mu da jama'a sai mu buɗe ragowar ƙofofin.


Kowace dama, dama ce ta samun wata damar. Kowane taku, taku ne zuwa ga wani takun. A kasuwa, dubu ɗarin ka ta farko, dama ce ta samun miliyan ɗin farko.


Iya karanta baƙaƙen kowane yare, dama ce ta fara koyon haɗa baƙi.


Iya zama, dama ce ta fara koyon tsayuwa, tsayuwa kuma dama ce ta fara koyon tafiya, haka dai lissafin yake a kowane ɓangare na rayuwa.


Kai da ka fara yanzu, ina kai ina yi wa waɗanda suka daɗe a ciki habaici?  Yanzu aka fara, kada nasarar dare ɗaya ta ruɗe ka.

Friday, 10 January 2025

Kalaman Karfafa Gwiwa Na Sabuwar Shekara

Kalaman Karfafa Gwiwa Na Sabuwar Shekara

Wuta ita take raba dusar ƙarfe da ƙasa, ta tsarkake shi tare da ƙara masa karfi da daraja. Wuta ita take narka zinare ta raba shi da dukkan datti, har ya zamo mai daraja kuma abun kwalliyya.


Kalaman ƙarfafa gwiwa na sabuwar shekara
Hoto: Rawpixel/Getty Images

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Haka kuma ƙalubalen rayuwa yana inganta ruhin Ɗan Adam, ya saita tunanin sa, ta yadda mutum zai ƙara fahimtar hikimar rayuwa da ma'anarta.


Ma'aiki sallallahu alayhi wasallam cikin Hadithi yake cewa;


"Idan Allah (S.W.T) ya so bawa, sai ya jarrabce shi, idan ya jure kuma ya jajurce, sai ya sami mafita da rabo. Abun da ya biyo baya na ƙaiƙayin zuciya kuma, idan aka yi haƙuri, kankarar zunubi ce ga mumini."


Manufa anan shi ne kada mu karaya a kowanne hali, mu kasance masu fata nagari, tare da kyautata zaton samun sauƙi daga kowanne tsanani, domin bayan dukkan tsanani sauƙi ne yake biyo baya.


Marigayi BASHIR OTHMAN TOFA, cikin talifin sa "TUNANIN KA KAMANNIN KA,, Ya ce "Wahala ita ke matso ƙwazo, shagwaɓa kuma kashe shi take yi."


Jarumi DENZEL WASHINGTON, yana cewa; sauƙi ya fi zama barazana ga ci-gaba sama da tsanani.


"Ease is more threat to progress than hardship".


Ba ma fatan tsanani ga kawunan mu, ko ga 'yan uwan mu, sai dai gaskiyar magana shi ne, ba za mu iya kaucewa ƙalubale ba matuƙar muna raye, sai dai mu yi tanadi, kuma mu yi komai cikin hankali da nazari.


Sannan mu yi haƙuri da rayuwa a kowanne hali da lokaci.


Mu sani tsanani ba ya dawwama, kamar yadda sauƙi da jin daɗi su ma ba su da tabbas.


Mu yi ƙoƙarin samarwa kanmu da kanmu farin ciki yayin yalwa ko rashi, mu ƙaunaci juna, mu yi afuwa da uzuri ga juna.


Tabbas ƙauna da soyayya wani sinadari ne da yake maganin cututtukan zuciya da yawa, ya ba ta salama, ya kuma amintar da makusantan mai ita.


Fatana gare mu duka shi ne mun shiga sabuwar shekara da sabon tunani, da sha'awar koyo da saurare tare da fahimta kafin yanke hukunci akan komai da kuma kowa.


Mu sani kowa da yadda yake kallon rayuwa, kuma tunanin kowa zai iya kasancewa mai amfani a wani lokaci.


Mafi muhimmanci shi ne mu gane lokacin da ake buƙatar komai da sa'adda ake buƙatar kishiyarsa.


Mu mutunta juna da ra'ayin juna.


Mu sani Allah (S.W.T) yana ganin mu a cikin kowanne al'amari, kuma shi ne Mai hukunci, daidai da dacewa a wajensa take.


Allah ya kawo mana ɗauki ya tsayar da zuciyar mu akan imani, ya sa mu kasance masu amfani ga kawunan mu da al'ummar mu.


Kada mu cutar kada a cuce mu.


Allah ya sa mun shiga sabuwar shekara cikin ƙaunar juna da taimakon juna da afuwa ga juna, tare da kare harshen mu daga miyagun kalamai na sukar juna Amin.