Showing posts sorted by relevance for query Abba Rabi'u Matallawa. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Abba Rabi'u Matallawa. Sort by date Show all posts

Friday, 20 December 2024

Wasikar Fatan Alkhairi Tare Da Neman Afuwar Masoyiya

Wasikar Fatan Alkhairi Tare Da Neman Afuwar Masoyiya

ZUWA GA KYAKKYAWAR MASOYIYATA



Ina yi miki fatan alkhairi, mafi daraja daga  kowanne da na taɓa yi miki a tsawon tarayyar soyayyar mu. Na turo wannan ne don neman afuwar laifina wanda dalilin sa ne idanuwana ke jin kunyar kallon ƙasaitacciyar fuskarki.


Wasikar Fatan Alkhairi Tare Da Neman Afuwar Masoyiya
Hoto: Freepik

MarubuciAbba Rabi'u Matallawa

Ina sanar da ke cewa ban janye daga gare ki don tsoro ko ƙiyayya ko waninsu ba.


Ran ki ya daɗe ki tuna fa ke ce mace ɗaya tilo, haka kuma macen farko da ta mallaki soyayyata ta gaskiya.


Sannan kuma macen da nake kwana da wuni da tunaninta, ashe kuwa ba zai yiwu na guje ki don ƙiyayya ba. Ke ce zaɓin zuciya a jiya da yau da gobe.


Fatana shi ne ki amshi uzurina a lokachin da kika kammala karanta saƙona. Ki kasance lafiya.


Daga naki Abba Rabi'u Matallawa.

Monday, 17 June 2024

Nagartattun Hanyoyi 5 Na Sace Zuciyar Budurwa Ko Bazawara

Nagartattun Hanyoyi 5 Na Sace Zuciyar Budurwa Ko Bazawara

A gaskiya sace zuciyar mace abu ne mai sauƙi ga wanda ya gane sannan kuma abu ne mai wuya ga wanda bai gane ba.


Hanyoyi 5 Na Sace Zuciyar Budurwa Ko Bazawara
Hoto: Create Vista 


MarubuciAbba Rabi'u Matallawa


Tabbas idan dai har kana so ka yi wa mace satar zuciya dole ne sai ka bi dokoki kamar haka:


1. Jan-Aji: ka sani fa mace ba za ta iya mallaka maka kanta haka nan kawai ba, dole ne sai ta ja maka aji don ta gane halayenka da haƙurinka, sannan kuma za ta so ta gane ko da gaske ne kake sonta ko ba da gaske ba, saboda mata sun tsani duk wani saurayin dake shirin yaudararsu, idan har ka ga ka zo wa mace kaitsaye ta amince da kai ba tare da jan aji ba, to fa ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiyar gogaggiyar mace ce to za ta ja maka aji sosai har sai ka kusan yin kuka tukunna.


2. Haƙuri: Tabbas dole ne sai ka zamo mai haƙuri idan ba haka ba ba za ka samu damar lashe jarabawar da mace za ta yi ma ba saboda za ka ga ababe da dama masu gasa zuciya, idan har ba ka zamo mai haƙuri ba; to kai da yin soyayya da mace sai dai a hankali.


3. Gaskiya: mace ta fi son saurayin da ke gaya mata gaskiya kai-tsaye, idan har kai maƙaryaci ne to ina mai tabbatar ma da cewa idan har ta zo ta gane sirrinka za ka sha kashi, don haka ake kwatanta gaskiya daidai gwargwado.


4. Kulawa: dole ne idan dai har kana son zamanka da mace ya ɗauki tsawon lokaci kuma yasa ta soka sosai fiye da kima to lallai kuwa dole ne sai ka kula da ita tamkar yadda za ka kula da kanka a lokacin da kake cikin rashin lafiya. Kulawa yana ɗaya daga cikin siffofin abin da mata suke so.


5. Rarrashi tare da girmamawa: Mace ta fi so idan har ka sanyata yin fushi to ka rarrasheta tamkar yadda za ka rarrashi jaririya.


Kuma mace za ta ji daɗi sosai fiye da kima idan dai har kana girmamata, ta fannin yabon halayenta na kirki tare da nuna mata cewa babu wadda ka fi so a duniya tamkar ita saboda tana da halin kirki.


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Mazaje 10 Da Mata Su Fi Kauna A Rayuwar Su Fiye Da Kowa

Mazaje 10 Da Mata Su Fi Kauna A Rayuwar Su Fiye Da Kowa

Irin namijin da zai yi wuya mace ta manta da shi koda a ce sun rabu da juna.


NAMIJIN DA MACE TA FI SO
Hoto: Istock photo


MarubuciAbba Rabi'u Matallawa


1. Namiji wanda ya san kimar mace, da darajar ta.


2. Namijin da yake yabon mace da riritata da ɗaukar ta da muhimmanci.


3. Namiji mai riƙon amana wanda ba ya juyawa matar sa baya, komai tsawon shekarun da suka ɗauka, da kowacce irin larura da ta gamu da ita.


4. Namiji da yake ba wa mace cikakken lokaci, domin sauraronta da jin ra'ayinta.


5. Namiji mai kyauta.


6. Namijin da yake ba wa mace haƙuri kuma ya lallashe ta idan ya ɓata mata rai ko ta shiga wata damuwa.


7. Namijin da ya tseratar da mace daga wani haɗari da ta fuskanta a rayuwa.


8. Namijin da mace ta san zai iya mutuwa saboda ita.


9. Namiji mai fara'a da murmushi da sakin fuska, da tafiye-tafiye da mace.


10 Namiji Mai tsafta da kwalliya, da lafiyar jiki, musamman wajan biyan buƙatar iyali (jima'i).


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Monday, 9 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Na Yamma

Gajerun Kalaman Soyayya Na Yamma

Ina fatan ba za ki zarge ni ba, ko kuma ki damu idan na kira ki da likitar zuciyata ba, wadda ke ba ta kulawa ta musamman a duk lokachin da ta kamu da cututtukan so. Ina son ki.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Yamma
Hoto: Oligo22/Freepik

MarubuciAbba Rabi'u Matallawa


Zan sanar da ke ke kuma ki taya ni isarwa zuwa ga duk wani wanda ke tantamar soyayyarmu cewa ni da ke tamkar jiki da ruhi ne ɗayansu ba zai yi cikakkiyar rayuwa ba sai da ɗayan, soyayyarmu kuwa kamar zanen dutse take.


Dukkanin kalmomin da nake faɗa miki a yanzu da kuma sauran lokuta na baya su ne zahiri, baɗininsu yana can cikin fadar zuciyata sai na zama ke ke ma kin zama ni sannan za ki fahimce su. Ke ta musamman ce a gare ni.


Ni da ke matafiya ne waɗanda tafiyarsu ke gudana cikin gungun 'yan adawa, ki kau da kai daga dukkanin maganganun maƙiyanmu a kaina. Kowanne matafiyi akwai wajen da ya nufa, ni da ke muna kan hanyar zuwa dandalin masoya ne domin cika ƙudurin mu na shiga ɗakin aure.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Sunday, 16 June 2024

Halaye 4 Da Ya kamata Saurayi Ya Guji Yin Su A Gaban Mace

Halaye 4 Da Ya kamata Saurayi Ya Guji Yin Su A Gaban Mace

Akwai wasu halaye da ya kamata ka daina lokacin da za ka je wajen mace domin neman soyayyarta da kuma lokacin da ka zama wanda take so.


Halayen da mata ba su so
Hoto: Natural Sciences 


MarubuciAbba Rabi'u Matallawa


1. Yawan tambaya, mai wannan halayya ya kan fita daga zuciyar mata.


2. Ka sani dole ne ka ɗan yi wa wadda kake so hidima koda kuwa ba aurenta za ka yi ba, mata ba su son marowacin saurayi, kai da kanka ma tuni ka san kyauta na jawo shaƙuwa, shaƙuwa kuwa tana saka so.


3. Idan ka tabbata ka zama wanda take so sosai to kai ma sai ka ɗan ja naka ajin, ƙilan ka ce me yasa? To ka lura ko abinci ne kake ci kullum, isar ka zai yi ita ma mace ai haka take.


4. Yana da kyau ƙwarai ka zama gwani wajen furta KALAMAN SOYAYYA su ma suna taka muhimmiyar rawa, ka zama mai matuƙar tsafta, domin kuwa kamar yadda kake ganin 'yam mata idan sun ɗau wanka ka ji sun birge ka, haka su ma matan kalar waɗannan samarin ke birge su.

Hanyar Sace Zuciyar Kowacce Irin Mace Duk Girman Kanta A Haɗuwar Farko

Hanyar Sace Zuciyar Kowacce Irin Mace Duk Girman Kanta A Haɗuwar Farko

FARKON HAƊUWAR KU


Yanzu lokaci ya canza an daina furtawa 'yammata kalmar so a haɗuwar farko, lallai ne idan kana so ka samu karɓuwa wajen mace to ka samu wata hanya wadda za ku ringa haɗuwa kuna fira/hira, a cikin firar kada ka kuskura ka nuna mata alamomin So ka ƙyaleta zuwa gaba za ta sani.


HANYAR DA AKE SACE ZUCIYAR MACE
Hoto: Vijesti


Marubuci: Abba Rabi'u Matallawa


Ka yi ƙoƙarin saka ta dariya a lokacin da kuke tare.


Idan kuka fara shaƙuwa, ka ringa nuna mata duk duniya ba ka ga macen da ta tsaru ba kamar ta amma kada ka zaƙe a wannan fannin.


Sannu a hankali sai ka fara aika mata text ta ido, kuma zuwa lokachin ka ɗan ringa tambayarta cewa "Wai wanne mai tsananin sa'a ne ya mallaki zuciyar wannan tsadaddiyar yarinyar?".


Idan har ta basar da zancen to fa ka ci gari ko kuma ta ce ma "Wani ne". Kuma ta ƙi faɗa maka sunansa to kai ɗin take nufi.


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Sunday, 4 May 2025

Sakon Soyayya Ga Budurwar Shafin Sada Zumunta

Sakon Soyayya Ga Budurwar Shafin Sada Zumunta

Ina fatan kin kasance lafiya kamar yadda nake a yanzu, na ji dukkanin saƙonnin zuciyarki zuwa ga tawa zuciyar. Ki sani tuni na daɗe da ganin wannan saƙon a cikin rubututtukan ki na baya gare ni.


Sakon Soyayya Ga Budurwar Shafin Sada Zumunta
Hoto: Move me quotes

MarubuciAbba Rabi'u Matallawa


Da a ce kin ɗora sashen saƙonnina gun ki kan mizani da kin gano makamancin hakan a cikin su.


Manufar nawa saƙon gare ki domin na tonawa tawa zuciyar asirin da take ɓoyewa, amma fa ki sani ɓoyon ya faru ba don tsoro ba sai domin kwarjinin da wannan kyakykyawar fuskar taki ke yi mini.


Ina sanar da ke na daɗe da kamuwa da soyayyar ki fiye da yadda zan faɗa miki  yanzu.


Na rantse miki da iyakar gaskiyata ina san ki fiye da yadda kifi ke son ruwa. Idan da babu soyayya tsakanina da ke babu dalilin da zai saka na nemi hoton ki har kala biyu, amma fa ba anan matsalar take ba idan muka tsunduma soyayya ina za ta kaimu? Na barki lafiya.

Saturday, 15 February 2025

Kyakkyawan Sakon Gaisuwa Ga Budurwar Nesa Mai Daɗi

Kyakkyawan Sakon Gaisuwa Ga Budurwar Nesa Mai Daɗi

Amincin Allah ya tabbata ga wannan da ruhi ke yi wa matsananciyar ƙauna wadda ta zarce ta uwa da ɗan ta. Ita ce wadda zuciya ba ta taɓa dakon soyayya mai nauyi ba kamar ta ta.



Kyakkyawan Sakon Gaisuwa Ga Budurwar Nesa Mai Daɗi
Hoto: GCShutter/Getty Images




Na rubuto miki wannan saƙon ne don na gaishe ki, irin gaisuwar da ake yi wa sarauniya mai cikakken iko.


Lokuta sun tafi ba tare da idanuwan mu sun sake yin arba da juna ba, tun bayan haɗuwar farko, sai dai fa ki sani a kowanne lokaci ƙaunar ki na hauhawa a cikin zuciya, ta yanzu ta zarce ta ɗazu, kuma ba ta kai ta gobe ba.


Fatana wanzuwa a matsayin mijin ki.