Showing posts sorted by relevance for query Muh'd Captain. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Muh'd Captain. Sort by date Show all posts

Tuesday, 10 September 2024

Kalaman Soyayya Na Rabuwa Da Masoyiya Cikin Yanayi Na Damuwa

Kalaman Soyayya Na Rabuwa Da Masoyiya Cikin Yanayi Na Damuwa

Na so a ce Allah ya ƙaddara rayuwarmu a tare a matsayin miji da mata, yadda zan nuna sakayyata a gare ki da kulawata, da soyayya ta  girma.


Rabuwa Da Masoyiya Cikin Yanayi Na Damuwa
Hoto: Zella life

Marubuci:- Muh'd Captain 


Ina jin kaina  kamar ba ni ba, tabbas ban san ya rayuwata za ta kasance ba tare da ke ba.


Ke ce burina a duniyar soyayya amma na rasa ki me ya sa haka? Wanne irin laifi na yi wa soyayya ne?


Na koyi abubuwa masu girma na rayuwa a tare da ke. Ta musamman ce ke, na yi kukan zuciya wanda ya fi komai ciwo.


Tabbas ba ni da ikon canza ƙaddara amma da ke ce zaɓina, zan sadaukar da wasu ababen da na mallaka nawa a kanki.


Ba na jin zan iya sake soyayya a cikin rayuwata, ciwon da ke zuciyata ba zai warke ba har abada,  ke ce a raina da zuciyata, ina son ki har ƙarshen numfashina.


Ina fatan Allah ya ɗaukaka dajararki a cikin jinsin mata, amma ina tausayin kaina, rayuwa babu ke akwai ciwo a gare ni.


Na bar ki lafiya, Ubangiji ya yi miki albarka, ya kuma albarkaci rayuwar ki.


Tabbas soyayya ta fi komai sa farin ciki.


Kuma ta fi komai sa baƙin ciki a zuciya.


Ina da-na-sanin fara soyayya a cikin rayuwata a yanzu.


Me yasa? Me yasa za ki min haka a soyayya?

Wednesday, 9 July 2025

Yadda Ake Kula Da Mace A Soyayya

Yadda Ake Kula Da Mace A Soyayya

Kuskuren da mace ta yi ma a soyayya ka tausaya mata kar ka yi abun da zai sa fitar hawaye a idonta. Ka duba rauninta kasancewarta mace.


Yadda Ake Kula Da Mace A Soyayya
Hoto: Business insider

Marubuci:- Muh'd Captain


Dukkan soyayyar da babu tausayin mace a zuciya tabbas soyayyar gangan jiki ake mata ba na ruhi ba.


Mace tana son mutum ne da zuciya ɗaya koda a ce shi mutum mai cutarwa ne a gurin ta.


Zuciyar mace da rayuwarta akwai rauni a ciki dole duk namiji ya koyawa kansa tausayawa mace.


Ita mace al'umma ce ba ta kulawa dole ce a gurin mu, tabbas masu girma ne mata, mu tausayawa raunin su.


Kuɗi, gida, kayan alatu ba su ne kawai abin da mata ke buƙata a soyayya ba, kulawa, tausayawa da kuma samun lokacin masoyi su fi buƙata.

Ita soyayya aba ce mai girma wadda take son kulawa da tausayawa.

Sunday, 22 September 2024

Sababbin Gajerun Sakonnin Soyayya Na Musamman

Sababbin Gajerun Sakonnin Soyayya Na Musamman

A kan so komai daidai ne, zan yi yaƙi a kanki don cikar burina. Zan so ki tamkar irin son da uwa ke wa 'yarta.


Sababbin Gajerun Sakonnin Soyayya Na Musamman
Hoto: Westend61

Marubuci:- Muh'd Captain 

Ina numfashi da burin kasancewa da ke ne, zan yi kukan rashin ki idan har Allah ya ƙaddara min rabuwa da ke.


Son ki abu ne mai girman gaske wanda babu kalaman da za su iya bayyana shi, ke ta musamman ce.


Na koyi son ki da ƙaunarki tun ban san mene ne so ba? Ke ce kika nuna mini ya so yake har na tabbatar da ƙaunarki a cikin zuciyata.


Babu wacce za ta so ni kamar ke, kin ba ni kulawa da farin ciki, irin ki ke ɗaya ce.


Ke ce inuwar da nake son zama cikin ta har zuwa ƙarshen rayuwata.


Annurina, ki min uzuri idan saɓani ya shiga tsakanin mu, ki duba girman soyayyar ki da ƙaunar ki a cikin zuciyata.


Ke ce abin alfaharina a duniyar masoya.


Ni ne sarki don na samu tauraruwa mafi haske da girman matsayi. Ina son ki.

Tuesday, 17 December 2024

Gajerun Kalaman Kara Dankon So Da Kauna Ga Budurwa

Gajerun Kalaman Kara Dankon So Da Kauna Ga Budurwa

Ina son rayuwa da ke har zuwa lokacin da numfashina zai ƙare, sarauniyar mata abin alfahari ne a ce an samu irinki a duniyar masoya.


Gajerun Kalaman Ƙara Dankon So Da Kauna Ga Budurwa
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Muh'd Captain


Ina son ki zaɓin raina, ke ce muradin zuciyata, ke  ta musamman ce a gurina.


Fatana Allah ya ba ni ikon samun ki na ba ki dukkan wata kulawata da komai nawa.


Soyayya na buƙatar kyautatawa haka zuciya ke son ba ki farin ciki. Na zaɓi rayuwa da ke cikin daɗi ko wuya, murmushin ki da kalamanki suna sanya ni farin ciki. Ina alfahari da ke tawan.

Saturday, 28 September 2024

Gajerun Sakonnin Soyayya Masu Taba Zuciyar Masoya

Gajerun Sakonnin Soyayya Masu Taba Zuciyar Masoya

Idan wani yana yabon ki sai na ji daɗi, kasancewar ki mai girma ce, sai kuma kishi da haushi su cika zuciyata domin dukkan yabon ki zai fi dacewa a ce ni nake furta su ba wani ba.


Sakonnin Soyayya Masu Taɓa Zuciyar Masoya
Hoto: Scme


Marubuci:- Muh'd Captain


Idan na ji an kira suna irin naki, sai na juya tunanina ke ce zan gani.


Zan kula da ke fiye da ma kaina, domin ke ce ni.


Zan ba ki farin ciki da komai nawa. Ina son ki kamar yadda nake son mahaifiyata.


Dukkan lokacina naki ne, tabbas na sani kuɗi ba zai ba ni ke ba, ina tausayawa kaina idan na rasa ki a rayuwa.


Mutum ba ya rayuwa dole sai da numfashi, ke ce numfashina.


Babbar ni'ima ce na samun mace kamar ki a cikin rayuwata.