Monday 25 September 2017

4. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa Ga

Na ce uwargidan Sarki ta aiko mini da rago
gasasshe. Daga ciki na yi kokarin in aika wa da
maigidan nan nawa na fari da rabi. Na sami wani
yaron makiyaya wanda zai tafi can dutse, na ba
shi ya kai masa. Yaron ya yi alkawarin ba zai ci
a hanya ba. Shi ke nan ya kama hanya ya tafi.
Ya ketare kogi ke nan sai na hango shi ya kai
naman bakinsa. Na kuwa tabbata kafin ya bace
wa idona sai da ya cinye duka. Ga shi kuwa ba
abin im bi shi ba, nisan da ke tsakanimmu ya yi
yawa. Dole na hakura, na dauki dutse na jefe shi,
na zuba masa bakaken maganganu, amma ba
wanda ya kai gare shi.
BABI NA 3
Na Zama Barawo
Ana nan dai har na sami fin shekara a hannun
‘yam fashin nan. A lokacin nan kuwa na zama
aminin Alhasan Sultan, har ya kan nemi
shawarata in wani abu ya same shi, ko ya sami
mutanensa. Da ya ga yanzu na zama dan gida,
za a iya gaskata ni, sai ya yi shirin ya dauke ni
zuwa wata tafiya da za a yi zuwa Farisa. Da dai
na ga Wannan tafiya za ta ba ni zarafin gudu, sai
na yarda nan da nan. Na ce im ban gudu ba a
lokacin, to lalle kuwa im mun dawo zan gudu,
don zan san hanya sosai sosai.
Da lokacin tafiya ya matso, Alhassan ya tara
manyan mutanensa duka, wadanda suka kware
cikin sana'ar fashi, ya ce dalilin wannan tafiya,
shi ne su isa Isfahan da dare. Bayan sun isa za
su tafi dakin saukar baki su wawashe su. In kun
tuna wannan dakin yana nan kusa da dakin askin
ubana ne. Alhassan shi zai bi da wannan tafiya
har Isfahan. In an kai kuma ya ce ni ne zan biyad
da su cikin garin, don ni dan garin ne, na san
hanyoyin zuwa ko ina. Amma fa mutane biyu za
su sa ni a tsakiya im mun isa, don in na nuna
alamar zam bashe su, su kashe ni. Bayan da aka
kare kintse kintse sarai, aka dibi makamai da
guzuri, aka shirya tafiya. Na dauki kudin nan
nawa, sa’an nan na yi wa Usman Aga alkawarin
im mun isa Isfahan zan fada wa abokansa ko sa
fanshe shi. Dukammu har da Alhassan mu
ashirin da daya ne.
Ga mu nan muna tafiya har muka iso Isfahan. Ko
da ma an kulla im mun zo mu shiga garin ta
wata hanya ce wadda ba wani mai tsaro. In
kuma dare ya yi mu tafi dakin saukar bakin nan
mu washe su duk, in kuma zai yiwu mu kame su
duka, mu rufe bakunansu mu kama hanyar gida.
Da dai na ga abin ya cika hadari sai na ce
Alhassan ko gwadawa kada mu yi. Tun da ya
zaro mini idanu, ya yi muzurai, ban sake ta da
maganar ba. Tun daga lokacin nan ne aka sa ni a
tsakiya. Da na dan kauce a kashe ni.
Mu uku muka ci gaba sauran na biye da mu a
baya. Da muka shiga garin muka sami wuri mai
kyau, muka sauko daga dawakimmu muka daure
su, sa'an nan muka bar mutum biyu mu kuwa
muka wuce a hankali, don kada mu ta da
mutane. Sai ga mu daf da dakin askin ubana.
Muka wuce zuwa masaukin bakin, na kwankwasa
kofa na kira mai tsaron kofa. Na ce, “Ali
Mohammed, bude kofa, ga ayari ya iso.”
Ya tashi a gigice ya ce, “Wane ayari ?" Na ce,
“Ayari daga Bagadaza." Ya ce, “Daga Bagadaza?
Ai wannan ya zo tun jiya. Karya ka ke yi." Da dai
na ga ba shi da alamar bude kofa, sai tilas na yi
amfani da sunana, na ce, “Wannan ayarin Alhaji
Baba ne wanda ya tafi da Usman Aga. Ina da
labari, maza bude kofa.”
Ya ce, “Alhaji Baba? Shi wanda ya saba yi mini
askin nan mai kyau ? Kai, maraba, shigo."
Bude kofarsa ke da wuya, sai ya ji wani ya shake
shi, sauran kuwa suka auka dakin. Nan da nan fa
aka shiga satar zinariya da azurfa. Aka kama
wadansu 'yan kasuwa su uku suna kwance a bisa
gadaje masu kyau, kayan gadajen kuwa sai
wanda ya gani don kyau. Aka tafi da su can
bayan gari, inda aka shirya wurin boyo. Ni kuma
da ya ke maigidana na fari a wannan masauki ya
ke, nan da nan na lababa inda na san a ke ajiye
kudi. Na yi sa’a na sami wani akwati na yi waje
da shi. Na bude na ga wata jaka mai nauyi, na
dauka na boye. Kafin mu kare kome dukan garin
yana kammu, amma ba wanda ya kuskura ya
matso inda mu ke. Wadansu suka hau rufin
dakin, wadansu duk sun daburce, sun rasa abin
da za su yi. Can sai ga ’Yan Sanda da
shugabansu sun zo. Su ma sai suka hau rufin
daki suna ta ihu, “Ku buge su! Ku kama su! Ku
kashe su !" Ina! Ba wanda ya matso, sai ’yan
wadansu masu karfin hali suka yi ta harbin iska
kawai da bindiga, ka san da dare ne.
A lokacin da a ke cikin wannan ribibi sai wata
zuciya ta ce mini in gudu. Na dai tsaya ina
gardama da kaina. Ina cikin wannan hali sai na ji
hannu ya rike ni. In juya sai ga Alhassan Sultan.
Ya ce in na kuskura na ba da shi zai kashe ni a
wurin. Da jin haka, sai na kama wani mutumin
Farisa wanda ya yiwo kammu, na ka da shi, na
rarumi gemunsa na yi ta ja, ina cewa im bai
yarda na kama shi ba zan kashe shi. Sai fa
maganganu ke fitowa daga bakinsa, wai in kyale
shi. Da jin muryarsa sai na gane ashe ubana ne!
Da na gane shi ne sai na sakam masa gemu,
saura kadan ma in cire shi, amma ina tsoron
raina. Muka yi ta kica kica da shi, na yi ta kai
wa wani sirdi da ke kusa da mu naushi, wai shi
na ke bugu. Muna cikin halin haka sai na ji
ubana ya ce, “Kash, da Alhaji na nan da bai
yarda an wulakanta ni haka ba.“ Da na ji haka sai
jikina ya yi sanyi, na tashi daga kansa na ce wa
’yanuwana, mafasa. “Wannan mutum ba zai yi
mana wani amfani ba, wanzami ne kawai.” Shi ke
nan duk muka watse, na hau dokina, na sukwane
shi sai maboyar da muka yi bayan gari.
Da muka kai maboyarmu sai duk muka sauko
daga dawakimmu don mu huta, su kuma su huta.
Kai, abinka da barayi, ashe lokacin da a ke ribibin
nan a Isfahan sai da wani ya sato rago! Kafin a
ce haka, aka yanka rago aka kyafe, mu kuwa
muka hau masa da ci sai kace angulai sun sami
gawar dabba, ba mu rage kome ba sai kasusuwa.
Bayan da ciki ya dauka muka natsa, sai kuma
muka shiga binciken bayin da muka kamo, don
mu tabbatar wa kammu ko za mu sami kudin
fansarsu da dama. Daya daga cikinsu dogo ne
mai shekara wajen hamsin. Daya kuma dattijo ne
gajere kakkaura, ya yi kama da Dan Sanda. Na
uku kuma shi ma kakkaura ne gargasa ya sha
dauri kankan, don lokacin da za a kama su shi ya
fi tsaurin kai. Dogon aka fara kira. To, da ya ke
ni kadai ne na iya harshen Farisa, sai aka sa ni
tafinta. Alhassan ya ce masa, “Kai wane ne ?"
Dogon ya ce, “Ni matalauci ne.” Alhassan ya ce,
"Wane irin aiki ka ke yi ?" Ya ce, “Ni mawaki ne.
Me zan yi maka?" Sai wani dam fashi ya ce,
“Mawaki! Ina amfanin wannan?"
Alhassan ya juya wajen dam fashi ya ce, “Ba
wani amfani. Wannan kam kudin fansarsa ba su
kai £7 ba, don duk mawaka matalauta ne. Wa ma
zai fanshe shi." Ya sake juyawa ga mawaki ya
ce, “Amma ka ce kai matalauci ne. To, ina ka
samo wadannan riguna masu tsada?” Ya ce,
“Wadannan rigunan daraja Sarkin Shiraz ya ba ni
don na yi masa waka ta yabo." Nan take aka
kwace rigunan aka ba shi wadansu na fata.
Sai kuma aka kira na biyu. Alhassan ya ce masa.
“Kai wane ne? Wace sana'a ka ke yi ?" Na biyun
ya ce, “Ni Alkali ne matalauci.” Alhassan ya ce,
“In kai matalauci ne, me ya sa ka ke kwance a
gado mai kyau ? In ka yi mini karya yanzu zan sa
a sare wuyanka. Ce kai mai arziki ne.”
Ya ce, “Ni Alkalin Galadoun ne. Gwamnan
Isfahan ne ya yiwo kirana, don a bincika maganar
kudin hayan kauyen da na ke ciki.” Alhassan ya
ce, “Ina kudin hayan ?" Ya ce, “Shi ne na zo in ce
ba ni da kudin, don fari sun bata mini duk
amfanin gonata, kuma an yi karancin ruwa." Aka
yi ta bugawa dai har aka ce in dai shi Alkalin
kirki ne, laIle mutanensa za su fanshe shi da
kudi masu yawa.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, da karfe
tara na dare (9:00PM), in sha Allah.
Allah ya kai mu.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: