Monday 25 September 2017

Shin ko Kasan Tarihin Hadiza Gabon???

Tura Wannan Zuwa

Hadiza Aliyu wacce aka fi sani
da “Hadiza Gabon” wata Jaruma ce a
masana’antar fina finan Hausa na
Kannywood a Najeriya. An haifi Jaruma
Hadiza Gabon a ranar 1 ga watan Yuni
na shekara ta alif dari tara da tamanin
da tara (1 June 1989) a garin Libreville
na kasar Gabon.
Yawan chin mutanen kannywood da ma
wajen ta baki daya kan kalli Hadiza
Gabon a matsayin “Sarauniyar Mata” . Ta
kasance mace mai kamun kai a
masana’antar gami da girmama na gaba
da ita. Bugu da kari ba’a taba samun ta
da wani ashararanci ba irin wanda akan
zargi fitattun Jarumai mata da shi.
Hadiza kan yi shiga irin ta mata a
addinance. Sannan kuma bata nuna
al’aurar ta a waje. Wajen tafiyar ta
al’amura kuwa na rayuwa, Hadiza
Gabon ba’a bar ta a baya ba, inda shima
ta kasance daya tilo.
Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo
masu yawa a masana’antar Kannywood.
Sannan ta kasance Jakadiya ta kamfanin
MTN a Najeriya. Bugu da kari ta kasance
mace ta farko da ke tafiyar da gidauniya
mai zaman kanta a masana’antar
Kannywood mai suna Gidauniyar HAG
(HAG Foundation) wanda kan bayar da
tallafi ga yara kanana da mata marasa
galihu a fannin ilimi, ciyarwa, lafiya da
dai sauran su.

Jaruma Gabon haifaffiyar garin
Libreville ce na kasar Jamhuriyar
Gabon. Mahaifinta Malam Aliyu ya
kasance dattijo dan asalin Gabon. Ta
bangaren mahaifiyar ta kuwa ta kasance
Bafulatana daga jihar Adamawa a kasar
Najeriya. Tayi karatun piramare gami da
sakandare a kasar Gabon inda tayi
jarrabawar gaba da sakandare da
sha’awar zama lawya inda ta fara
karatun digirin ta na farko a kan fannin
lauyanci. Hadiza ta fice daga neman
ilimin lawyanci a shekarar farko saboda
wadansu dalilai da suka hana ta cigaba.
Amma daga bisani ta samu kammala
karatun difloma a harshen Faransanci
wanda kuma hakan ya bata damar
koyarwa a wata makaranta cikin
harshen na Faransanci.
Hadiza Gabon na da ‘yan uwa wadan da
suka hada da Malam Aliyu (mahaifi)
, Hajiya Halima (mahaifiya), Muhammad
Umar (dan uwa), Aisha Umar (dan uwa)
, Zakari Ali (dan uwa), Issa Ali (dan uwa)
, Hamidou Ali (dan uwa), Hachimu
Ali (dan uwa),Muhammad Ali (dan uwa),
Dahirou Ali (dan uwa) da kumaAdam
Ali (dan uwa).
Kasancewa Jaruma
Hadiza Gabon ta tsinci kanta a cikin
masana’antar Kannywood a yayin da ta
shiga garin Kaduna daga jihar Adamawa
bayan samun sha’awa da tayi a citin
masana’antar ta Kannywood tare da
wata ‘yar uwarta. A wannan lokaci ne ta
samu haduwa da Jarumi Ali Nuhu inda
ta nemi taimakon sa gami da hadin kai
domin zama Jaruma. Hadiza ta samu fita
a shirin fim ta farko a rayuwar ta a
cikin fim din Artabu a shekara ta 2009.

Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo
dana girma kala kala a masana’antar
Kannywood. Ciki harda Fitacciyar
Jaruma a masana’antar Nollywood a
shekara ta 2013 a fim din ‘Babban
Zaure’ da kuma Jaruma a taron ban
girma na biyu a masana’antar
Kannywood wanda akayi a shekarar
2014 a fim din ‘Daga Ni Sai Ke’ . Mai
Girma Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa
Kwankwaso shima ya samu baiwa
Jaruma Hadiza Gabon lambar yabo a
shekara ta 2013.
Jaruma Hadiza Gabon ta dauki lambar
girmamawa daga Kannywood AWA 24
Film & Merit Award a shekarar 2015 a
fim din ta na ‘Ali Yaga Ali’ . Sai kuma
taron African Hollywood Awards shima
data samu na fitacciyar Jaruma a
shekara ta 2016 a fina finan Hausa na
nahiyar Africa a cikin yaren Hausa.
Hukumar Gidan Malamai da aka fi sani
da Kano State Senior Secondary Schools
Management Board ita ma ta samu
karrama Hadiza Aliyu Gabon a shekara
ta 2016 a bisa gudummawar da ta kam
bawa ilimi a Jihar Kano karkashin
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sai kungiyar Start Up Kano ina ta
karrama Hadiza a shekara ta 2016 a bisa
babbar gudummawa akan bayar da jari
ga marasa aikin yi.
Aikin Gidauniyya
Hadiza Gabon ta fara aikin kafa
gidauniya a shekara ta 2015 wanda
kuma a cikin shekara ta 2016 tayi mata
ragista. Gidauniya mai suna HAG
Foundation anyi ta ne domin tallafawa
mata da kananan yara marasa galihu a
fannin ilimi, lafiya da abinci. Hadiza
Gabon ta kasance mace ta farko a
masana’antar Kannywood da ta fara
bayar da irin wannan gudunmawa.
A watan Maris na 2016, Hadiza Gabon ta
ziyarci gidan ‘yan gudun hijira a Jihar
Kano wadanda rikicin Boko Haram ya
ritsa dasu inda ta raba kayayyaki da
suka hada da kayan abinci da sutura
dama sauran ababan more rayuwa.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Arewaloaded

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: