Thursday 21 September 2017

Abin Kunyane Babba Ga Dan Musulmi: Bayani akan Sabuwar Shekarar Musulinci

Tura Wannan Zuwa

Abin mamaki a wannan zamanin sai kaga an
tambayi mutum yau nawa ga wata sai kawai kaji
yace "yau 21 Semtember 2017" da ka ce masa
a'a na Musulunci kake nufi sai kaji yace "ban
sani ba" wannan gaskiya abin kunya ne ga
dukkan Musulmin da za'a tambaye shi kwanan
watan turawa ya fadi amma ya kasa fadin na
Hijrar Musulunci.

TARIHIN HIJRAR MUSULUNCI

Asalin faruwar Kalandar Hijrar Musulunci, abu ne
mai fadi da dogon tarihi, amma dai ta samu
asalinta ne lokacin Khalifancin Sayyadina Umar
Bin Khaddab (A.S.) a sakamakon wani abu mai
muhimmanci daya faru a cikin watan Sha'aban
wanda Sahabbai suka yi kokarin tantance wane
Sha'aban ne amma abin ya faskara. Wannan
dalili ne yasa Sayyadina Umar (A.S.) ya tara
Sahabbai inda ya nemi shawarar yadda za'a rika
tantance tarihin faruwar al'amura a Musulunci.
Don haka shawara ta tsaya akan fara lissafin
kalandar Musulunci daga lokacin da Manzon
Allah (S.A.W.) yayi hijra daga Makkah zuwa
Madinah, kuma aka sanya watan Muharram ya
zama shine watan farko a cikin jerin watannin
kalandar Musulunci (Hijrah).

WATANNIN HIJRAR MUSULUNCI

Shekarar Musulunci (Hijrah) tana da watanni
goma sha biyu 12 wadannan watanni sune:-
(1) Muharram
(2) Safar
(3) Rabi'ul Awwal
(4) Rabi'ul Thani
(5) Jumada Ula
(6) Jumada Thani
(7) Rajab
(8) Sha'aban
(9) Ramadan
(10) Shawwal
(11) Zhul Qi'idah
(12) Zhul Hajj

WATANNI HUDU MASU ALFARMA

A cikin watanni Hijrar Musulunci guda 12 Allah
Madaukakin Sarki ya kebance guda hudu masu
Alfarma, sune:-
Muharram wata na (1)
Rajab wata na (7)
Zhul Qi'idah wata na (11)
Zhul Hajj wata na (12)

A KARSHE

Shawara ga dukkan Musulmi ya dage ya ke sa
kwanan watan Hijrar Musulunci a dukkan
harkokimu na yau da kullum.

Allah ya daukaka Addinin Musulunci da
Musulmai, Ya kare mu daga sharrin makiya
Manzon Allah (S.A.W) ameen.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Filin Tunatarwa da Fadakarwa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: