Friday 22 September 2017

Allah yasa darajar mai ta kara karairayewa - Inji Dangote

Tura Wannan Zuwa Ga

Mashahurin dan kasuwar nan kuma
shugaban rukunin kamfanonin Dangote
watau Alhaji Aliku Dangote yayi kira ga
al'ummar kasar nan da su dukufa wajen
yin addu'a Allah ya kara karairaye darajar
farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Babban dankasuwar wanda kuma dan
asalin jihar Kano ne ya bayyana hakan
ne a wajen wani taro da yayi da yan
kasuwa a lokacin da shugabannin
kasashen duniya ke taron su a majalisar
dinkin duniya.

NAIJ.com ta samu cewa Dangote dai ya
bayyana cewa idan farashin na Danyen
man ya ragu ne kadai kasar Najeriya
zata maida hankali ta yi mulki mai
inganci da kuma ci gaba.

Mashahurin dan kasuwar dai ya kuma
yi Allah wadai da yadda yan Najeriyar
suka zama cima zaune ta yadda ba sa
iya noma abincin ma da za su ci balle
har su fitar.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Hausa.naij.com

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: