Friday 22 September 2017

Kamata yayi Buhari ya maida albashi mafi karanci N145,000 - Sanata Shehu Sani

Tura Wannan Zuwa

Dan majalisar dattawa mai wakiltar
mazabar tsakiyar jihar Kaduna Sanata
Shehu Sani, ya bayyana takaicinsa dangane
da halin kuncin da ma’aikata suke ciki
musamman na rashin biyansu albashi mai
kyau.

Shehu Sani, ya kuma bayyana cewa
hatta kudin da ake kashewa karnukan
‘yan siyasar kasar nan a duk karshen
wata ya fi yawan albashin ma’aikacin
gwamnatin na Dubu 18 da ake ta kira
da gwamnatoci su aiwatar, inda yace
abin kunya ne ace ma’aikacin
gwamnati Yana amsar naira Dubu 18
Wanda a cewarsa, ya kamata ace
ma’aikacin gwamnati yana karbar
karancin naira Dubu 100 bisa irin
gudummawar da suke bayar wa wajen
ci gaban kasa.

NAIJ.com ta samu labarin kuma Sanata
Shehu, ya bayyana haka a jawabin da
ya gabatar a taron ranar ma’aikata na
bana wanda ya gudana a dakin taro na
otel din malamai na NUT dake kaduna.

Yace kudaden da masu rike da madafun
iko na siyasa kudaden da gwamnatin
take basu ya wuce misali, yana mai
cewa yay idan da za’a rage kudadan da
antayawa Sanatoci da ‘yan majalisun
wakilai da gwamnoni da shugaban kasa
ya Isa ace babu wani ma’aikacin
gwamnatin da zai koka akan Albashi
saboda mu kawai muka San kudin da
ake bamu.

Da yake bayani akan ma’aikatan jihar
Kaduna cewa "ina tausaya muku
dangane da halin da kuke ciki saboda
haka ina jinjinawa kungiyar kwadago
bisa jajircewa da tayi akan hakkin
Ma’aikatan”.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Hausa.naij.com

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: