Friday 22 September 2017

Hadiza Gabon ta fara fitowa a fina-finan Nollywood

Tura Wannan Zuwa

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood
Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan
Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.

Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya
cewa ta fara gwada sa'arta a fina-finan
Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da
ita ta yin fina-finai a bangarori daban-daban.

A cewarta, "Ba wannan ne karon farko da na
soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je
Amurka, na fito a wani gajeren fim na turanci,
amma wannan ne karon farko da na fito a fina-
finan Nollywood.

"Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne
ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna
'Lagos real fake life'.

"Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a
matsayin 'yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta
bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a
fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a
wannan fim".

Hadiza Gabon ta kara da cewa "Tun da ya gaya
min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida
masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba
zan fito a matsayin da zai saba da addini da
al'adata ba".

Jarumar ta ce babu wani "bambanci tsakanin
yadda ake yin fina-finan Kannywood da na
Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don
haka na ji dadin soma fitowa a fina-finan
Nollywood".

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: