Saturday 23 September 2017

Ba na zaton za mu shawo kan Koriya ta Arewa-Donald Trump

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya
ce bai da tabbacin shawo kan Kim Jong-Un,
balantana ya warware matsalar Koriya ta
Arewa.
Trump ya furta wannan kalamin a yayin
wani taron siyasa da 'yan jam'iyyar
Republicains suka yi a yankin Alabaman
kasar Amurka.

Da yake jawabi a gaban mahalartan wannan
taron, shugaban na kasar Amurka ya ce :"
Shugabannin da suka gabata a kan karagar
mulkin wannan kasar,Clinton da Obama ne,
ya kamata a ce sun kwace makamin
nukiliya daga hannun 'Malam mai roka'
wato Kim Jong-Un.Amma sai suka yi wa
lamarin daukar sakainar kashi.A yanzu
nauyin warware wannan matsalar ya rataya
a wuyana.Ya kamata mu gaggauta magance
wannan tashin hankalin".

Trump wanda ya ci gaba da jawabinsa a
gaban 'yan jami'ayyarsa,ya tabo matsalolin
ciki da wajen kasar Amurka,inda ya ce :
"Matsalar Koriya ta Arewa abu ne da ya
kamata a ce an magance shi tun da
dadewa, fakat 'yan jami'ayyar Democrats ba
su tabuka komai ba".Mu dai mun yi abin da
muke iya yi,.Watakila za'a yi nasara,
watakila a'a.A gaskiya, ni a nawa ganin, ba
na zaton za mu shawo kan Kim Jong-Un,
balantana mu warware matsalar Koriya ta
Arewa.

Amma ku san da cewa, duk yadda
lamarin ya zama, za ku kasance a cikin
tsaro.

Daga bisani Trump ya tabo batun Sanatan
yankin Arizona,John McCain wanda ya
sanar da cewa zai jefa kuri'ar a'a, a yayin
yunkurin yi wa tsarin kiwon lafiya mai
rahusa na Obamacare kwaskwarima,inda ya
ce: "Dole ne mun sauya tsarin
Obamacare.Amma idan ana bin gaskiya,
amfani da kuri'ar a'a, abu ne mai matukar
razanarwa.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Trt Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: