Tuesday 26 September 2017

KARANTA LABARIN DABBOBI DA MUGUN SARKI

Tura Wannan Zuwa Ga
Wasu kwadi ne suke zaune a cikin wani tabki
cikin jin dadi da walwala, ba abin da suka nema
suka rasa, idan sun gaji da wasansu cikin ruwa
sai su tsallaka kan tudu su sha iska. Ba su
damuwar kowa, kuma babu wani abu da yake
damun su.

Da Mugun Sarki


MarubuciBukar Mada

+2348021218337

Suna nan haka sai wasu daga cikinsu suka ce,
ina amfanin zamanmu haka babu wani Sarki da
zai rika mulkinmu, ba mu da wasu dokoki da za
su tafiyar da tsarin rayuwarmu.

Allah kuwa ya
amshi addu'arsu!

Ana nan wata rana sai wani dan guntun reshen
bishiyar da take bakin tabkin ya karye, ya fado
kwatsam a gefen tabkin. Kwadi suka tsorata
suka fada ruwa da gudu. Sai wasu daga cikinsu
suka ce ai Sarkin da suke roko a turo musu ne
Allah ya turo musu..

Kwadi na cikin ruwa suna jira su ji irin dokokin
da Sarki zai shata musu, suka ji shiru, su kuma
suna jin tsoron su matsa kusa da shi. Ana nan
dai har wani mai karfin hali daga cikinsu ya
matsa kusa da reshen itacen nan da ya fado,
sannu-sannu har ya kai ga taba shi, icce bai
motsa ba, har ya hau kansa, yana rawa, itace
dai bai motsa ba. Da saura suka ga haka, sai
duk suka fito suka haye kan reshen itace. Sai ya
kasance koyaushe nan ne wurin zaman kwadi
tare da sabon Sarkinsu.

Sai dai kwadi ba su yi murna da wannan Sarki
da aka turo musu ba, suka nuna sun fi son Sarki
mai rai, mai motsi, wanda zai rika shata musu
dokoki, kuma ya shimfida mulkinsa.

Wannan buri na kwadi ya sa Allah ya yi fushi da
su. Kwaram ran nan sai ga wani zalbe zai wuce
ta wurin, sai ya ga kwadi da yawa bakin tabki,
shi ke nan abin nema ya samu, dama wurin
neman abinci zai tafi. Sai ya tsaya bakin tabkin
nan ya rika kama kwadi yana cinyewa.

Da kwadi suka ga zalbe ya dame su da kisa
haka, ya hana su sakat, sai suka ce wannan
wane irin Sarki ne aka turo mana. Mu dai mun fi
son zamanmu na da.

DA MULKIN ZALUNCI
GWAMMA ZAMA BABU SARKI!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user