Wednesday 27 September 2017

RAYUWA KENAN TARIHIN FULANI: Nasabar Toronkawa

Tura Wannan Zuwa Ga

(Daga Littafin Tarihin Fulani na Wazirin Sokoto
wanda kamfanin ɗab'i na NNPC ya wallafa a
shekarar 1956)

Ana ce Musu Toronkawa ne saboda sun zauna a
kasar Toro. Ita Toro Kasa ce a can yamma maso
kudu na Afirka ta yamma. Sun taso ne daga
wajajen 'ɗurisina' cikin kasar Sham (syria), sun
biyo daga gefen arewa ta Afirka ta yamma har
suka sadu da Toro suka Zamna wurin.

Suka yi  yawa kwarrai, har lokacin da aka aiki
ukubatu yaki Afirka, ya sadu dasu. Sai suka shiga
addinin islama ba tare da anyi faɗa ba. Ukubatu
ya auri ɗiyar Sarkinsu, sunanta Bajju Mangu. To
su Toronkawa jinsi ne da suka fito daga zuriyar
Ramo, ɗan Isa, ɗan Ishaku, ɗan Annabi Ibrahim
(AS)..

Bajju Mango ta haifi ɗiya huɗu da ukubatu,
sune:- 1. Delta 2. Woya 3. Roruba da 4. Nasi.
Waɗannan sune asalin dukkan fulani da suka
fara magana da fulatanci.
Toronkawan dauri, harshensu wakuru ne.

Daga baya zuriyar Ukbatu ta yawaita.

1. Daga ɗiyan Delta kabilar songhay ta fita.
2. Daga ɗiyan Nasi dangin ba'awina da wolorɓe
suka fita.
3. Daga ɗiyan Woya dangin Furɓe suka fita
4. Daga ɗiyan Rorube dangin woloɓe suka fita.

Bayan sunyi yawa, sun zauna a wuri mai suna
Falgu, sai suka rabu da sauran Toronkawa na
Futa-Turo.

Lokacin da sukayi karfi, sai suka ɗauki yaki
babba. Suka tasar ma Futa sukaci amanar Sarkin
Futa suka kasheshi yana sallar Idi. Suka kama
kasar futa suka zauna suna ɓarnace-ɓarnace.
Sannan sai wani malami daga cikin Toronkawa
ya tashi yayi Jihadi dasu, ya rinjayesu, ya gyara
kasa ya zuba adalci, ya kyautata zaman
toronkawa.

To bayan Rasuwarsa sai Fulani Jinin Ukubatu
suka sake kawo yaki ga Toronkawa, suka koresu
daga Futaƴ, suka sake kama kasa tare da shiga
ɓannace-ɓannace..

Bayan haka kuma sai fulani Toronkawa sukayi
shirin yaki da Fulani jikokin Ukubatu, suka taho
da yaki, sukayi faɗa dasu mai tsanani har suka
rinjayesu mugunyar rinjaya. Saboda haka sai
fulani ɗiyan ukubatu suka kasu uku.

- Kashi ɗaya suka saduda sukabi Toronkawa

- Kashi na biyu suka koma Falgu inda suka soma
zama da fari

- kashi na uku suka yo gabas suka tsammaci
zasu riski 'yanuwansu Larabawa saboda Ubansu
balarabe ne. Wasu cikinsu sun iya komawa kasar
larabawa, wasunsu kuma sun kasa basu karasa
ba. Sunan babban su Dunurundi.
To waɗannan da basu karasa ɗinba, daga cikin
sune zuriyar Beni yalalɓe, da sissilɓe, da
walanɓe, da gumborawa da gwalankwa'en da
fulanin Adamawa suka fito.

Waɗannan sune dangogin da suke daga cikin
zuriyar da suka taho daga Naskanga tare da
Dunurundi.
Su waɗancan sunfi toronkawa yawa. Domin an
samu kashin farko da suka koma Falgo daga
baya sun kara kawowa Toro yaki suka cinyeta
tare da sake komawa ɓarna, har sai da aka samu
wani daga toronkawa mai suna Sulaiman yayi
yaki dasu ya koresu ya watsasu, ya naɗa sarki
Abdulkadir. Bayansa kuma sai anka naɗa
Muhammadul Amin, anka zamna lafiya,
Toronkawa suka amince da filani ɗiyan ukubatu.

Bayan waɗannan al'amura da muka faɗa,
lokacin nan Musa Jakollo kakan Shehu Usmanu
ya taso da jama'arsa don gudun fitina, ya
fuskanci gabas har ya karaso 'K'wanni' a shekara
ta 500AH. Shikuma ɗiya nai sai suka warwatsu...

Kaso ɗaya sune ɗiyan Ali, na biyu ɗiyan ɓininga,
sai ɗiyan Kogga, sai ɗiyan ɓaleni da ɗiyan
Raneni. Diyan ɓininga ne suka tashi daga kwanni
sa'ar da Sarkin kwanni Damka ya zambace su ya
karkashe su, ya kama ɗiyansu ya yasashe
dukiyar su. Diyan Ali sun sauka a wani wuri da
ake kira Kuluba.

DANGANTAKAR SHEHU ZUWA MUSA JOKOLLO

Abinda ma'anar fodio shine Malami, kuma wanda
malami ya haifa. Shine Fodio ɗan Usmanu ɗan
Salihu, ɗan Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo ɗan
Jaɓɓo ɗan Mamman Samba ɗan Masirana ɗan
Ayuba ɗan Baba fan Abubakar ɗan Musa Jakolli
wanda yake da ɗiyan Imamu Demba. Intaha.
Idan har Ingancin wannan Tarihin ya tabbata,
muna iya kallonsa a matsayin sabuwar fuska
saɓanin wanda ake yaɗawa mai cewa Fodio
Aljana ce kuma itace ta haifi shehu Usmanu..

Koda Yake, har yanzu na lura dacewa Fulani da
yawa suna ji a ransu cewar Asalinsu gamin
gambiza ne tsakanin Larabawa da Aljannu.
Watakila dai, abinda yake akanmu bai wuce
binciko tarihin silsila ko ace rarrabuwar kabilun
fulanin ba, kamar misalin Sulluɓawa, Danejawa,
Natirawa, Agalawa, Holma, Bongwa, Naturɓe,
Ba'awa (anfaɗi silsilar su a sama), Rudunnawa,
Magawa da dai sauransu.

Zamu cigaba Insha ALLAH
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Sources By  ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: