Tuesday 26 September 2017

SHIN KO KASAN TAKAITACCEN TARIHIN ATTAJIRI NA DAYA A AFIRKA, ALHALIKO DANGOTE Tare da Zafafan Hotunan Sa???

Tura Wannan Zuwa Ga
Daga Littafin Kano cibiyar Kasuwanci wanda
Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo (Allah
yajiqansa) ya wallafa
.
Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo

Shine Aliko ɗan muhammadu Gote ɗan Aliyu,
dukkaninsu fulanin Kura ne ta jihar kano.
An haife shi a shekarar 1956 miladiyya a
unguwar Kududdufawa ta cikin birnin kano,
sannan Kakansa na wajen Uwa marigayi Alhaji
Sunusi Dantata ne ya yaye shi, domin tunda ya
ɗauko shi sai ya danka shi a hannun shakikiyar
mahaifiyarsa mai suna Hajiya Ammami, ita ce ta
raine shi har girmansa, wanda sai daga baya ne
Alhaji Aliko ya gane cewar Hajiya Mariya ce
mahaifiyarsa.
Bayan ya soma karatun muhammadiya a gida, sai
aka sanya shi a makarantar boko, inda daga
bisani ya samu damar karatu a makarantar
sakandare dake Birnin Kudu, sai dai kafin ya
kammala sai kakansa Alh Sunusi ɗantata ya
ɗaukeshi daga makarantar, yace kasuwanci ya
kamata yayi ba karatun boko ba.


A wannan lokaci, wani gidan bulo aka buɗe musu
a Unguwar kurnar Asabe, suka rinka kula dashi,
amma shi Alhaji Aliko, yafi son karatun boko a
zuciyarsa.

Ance ya taɓa samun yayansa mai suna Alh
Ummaru Gote domin ya taimaka a faɗawa
kakansa a maidashi makaranta, amma abin ya
faskara a lokacin. Sai daga baya ya samu
nasarar kammla sakandare tare da tafiya jamiar
Azhar ta Misra don yin digiri.

Sannu a hankali sai Alhaji Aliko ya shiga
kasuwancin sai da kayayyakin keken hawa,
sannan ya ya faɗaɗa harkar kasuwancinsa izuwa
Kwangiloli.

Ance wata makarantar primary ya fara ginawa a
garin Takai, daga nan sai wasu makarantun a
birnin kudu, sai wani ɓangane na gidan gajiyayyu
a mariri..

Shi da kansa ya taɓa faɗin cewar da rancen
Naira dubu ɗari biyar ya soma kasuwanci, wanda
ya karɓa daga hannun ɗan uwan Mahaifiyarsa da
sharaɗin zai biya a tsawon shekara, amma cikin
nasara ya biya kuɗin a watanni shidda kachal
saboda sa'ar daya samu a kasuwancinsa.
A wajejen shejara ta 1972 miladiyya kuwa sai ya
koma Legas inda ya shiga harkar Siminti a
karkashin kawunsa Alhaji ƳUsman Dantata wanda
akafi sani da 'A Makkah'.

A wannan lokacin, ance Alhaji Aliko ya rinka
safarar manyan Motoci daga kasar Amurka zuwa
nan gida Nigeria, yana kuma shigo da kayyakin
sufuri misalin sukari shinkafa da fulawa tare da
fitar da kayayyaki irinsu coco, qaro ka kashu
daga nan gida Nigeria zuwa waje.

Daga nan kuma sai ya soma siyen hannayen jari
daga manyan masana'antu. Inda ya soma da
siyen hannun jari na kamfanin MTN, dana
kamfanin Gishiri na jihar Ogun wanda daga baya
aka siyar masa dashi kachokan.

Haka kuma ance ya kafa bankin kasuwanci mai
suna Liberty Merchant Bank wanda daga baya ya
siyar dashi, ya kuma siyi hannun jari mafi tsoka a
tsohon Bankin Gamji, sannan daga bisani a
hankali ya buɗe kamfanin ɗangote cement a jigar
Lagos. Tare da kafa kamfanonin fulawa a jihohin
kano da calabar, da kuma kamfanin yin Taliya
dana yin buhhuna a Lagos. Sai kuma kamfanin
hako siminti a jihar kogi, da wani gagarumi
wanda babu irinsa a Afirka dake Obajana.
Haka kuma, ya shiga ɓangaren sufuri, wanda
ance a kalla zuwa yanzu yana da Jirgin ruwa mai
masa zirga zirga tsakanin kasashe, da kuma
motocin tirela sama da dubu biyar.

Babban darasin ɗauka a rayuwar Alhaji Aliko
Dangote shine fafutika wajen neman arziki.

Shi mutum ne mai faɗi-tashi, wanda yasanya
lissafta hanyoyin shigowar dukiya a gareshi tana
da wahala.

Sannan kuma an sanshi da hangen nesa, domin
ance a lokacin dazai kafa babban kamfaninsa na
Obajana, sai daya siyar da kadarorinsa dake
Ingila da wasu anan Nigeria, amma duk da haka
kuɗin basu isa ba. Don haka daga baya sai ya
nemi bashin Bankuna, yana mai rokonsu dasu
tallafeshi ya samu nasarar kammala aikin daya
faro, idan ba haka ba kuwa zai dulmiya ne baki
ɗaya..

Ai kuwa sai akayi sa'a suka sanya dukiyarsu
acikin aikin saboda sun sanshi yana da kokari da
hangen nesa a kasuwanci.

A fagen kyauta kuwa shi gawurtacce ne, tunda
an bayyana shi a Matsayin mutum mai matukar
biyayya ga mahaifigarsa. Duk kuwa wanda yasan
Hajiya Mariya Sunusi Dantata yasanta da ciyar
da gajiyayyyu da taimakon marasa karfi a kullum.
Wanda ance ita ke sanyawa yana bada dukiyarsa
domin gudanar da waɗannan ayyuka na alheri.
Sannan kuma sam baya mancewa da tsoffin
aminansa.


Akwai wani labari ma da wani abokinsa na
yarinta ya taɓa bayarwa, inda yace akwai wani
lokaci da yaso ya haɗu da Alh Aliko a lagos
amma sai ya kasa saboda uzurorrika da sukai
masa yawa.

Sai wani direbansa na Tirela yace kazo ranar
kaza, Maigida yana ganawa damu direbobinsa,
anan zaka iya haɗuwa dashi.
Hakan kuwa akayi, da ranar tazo sai mutumin ya
kusanci Alhaji Aliko, ai kuwa da ganinshi sai
Alhajin ya shaidashi. Bayan sun gaisa sai ya
haɗa shi da masu kula da lafiyarsa, yace a
sanyashi a tawaga zai neme shi daga baya. Daga
nan Alhaji Aliko yaci gaba da harkokinsa.
Mutumin yace bayan Alhaji Aliko Dangoye ya
kammala aikinsa a wannan waje, sai suka
ɗunguma har dashi ɗin a motoci izuwa wasu
wuraren ya duba wasu aiyuka, sannan zuwa dare
suka isa filin jirgin sama inda suka hau Jirgi
mallakin Alhaji Alikon, wanda ya kaisu wata kasa
ta turawa.

Amma fa duk abinnan da ake, bai gana da Alhaji
Alikon ba, domin ko acikin jirgin wurin da yake
zaune daban, shikuwa Alhaji yana can nashi
wurin daban.
Mutumin yace sai kashe gari da dare, bayan an
saukeshi a wani hotel an bashi abinci mai kyau
ya huta, sannan akazo akace masa Alhaji nason
ganinsa.
Daga nan aka shigar dashi wani ofishi, inda yaga
Ahaji Aliko zaune a kujera, a gabansa ga wayoyi
nan burjik na amsa kira.

Mutumin yace nan take Alhaji Aliko yayi masa
maraba, sannan yace masa zasu gana na tsawon
mintuna kaza, babu daɗi babu ragi.
Ai kuwa nan take suka shiga firarrakin tsoffin
abokanansu da ana tuno tsuhuwar rayuwa da
yadda rayuwa ta canza. Alhaji Aliko ya rinka
tambayarsa ina wane, ina wane, ya wane yake?
Wani yaji ance ya mutu, wani kuma ace masa ba
lafiya da dai sauransu.
Da lokaci ya cika, sai Alhaji Aliko yacewa abokin
nasa to yanzu za'a mai dakai gida, sannan za'a
kawo maka tirela kaza ta abinci, ina so ka baiwa
wane da wane da iyalan wane.. Kai kuma abu
kaza da kaza ne naka.

Mutumin yace ya nemi Alhaji Aliko ya bashi
lambar wayarsa, amma sai Alhajin ya karɓi tashi
yace yaje kurum zai nemeshi da kansa.
Ai kuwa yace a ranar da ya kammala rabon
kayayyakin da aka bashi bisa amana, da dare sai
kurum yaga kira da lambar kasar waje. Yana
amsawa yaji Alhaji Aliko yana masa godiya bisa
yadda ya rike amana..
Mutumin yace babban abin daya bashi mamki
shine yadda har Alhaji Aliko Dangote yabi
diddigin aikin daya bashi..

'Ya'yayen Alhaji Aliko Dangote sune:-
Hajiya Mariya, Hajiya Halima da Hajiya Fatima...

Dafatan Allah yayiwa dukiya albarka, ya kara
masa tausayi da taimakon talakawa amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng 

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user