Sunday 24 September 2017

KUNDIN MASU TUBA (012)

Tura Wannan Zuwa

ABU LUBABAH BN ABDIL MUNZIR (RA) : Wannan
Sahabi mai girma yana daga cikin Mutanen
Madeenah, ta bangaren Qabilar Ausu. Kuma yana
daga cikin yardaddun Manzon Allah (saww).
Alokacin da Allah ya Umurci Anmabinsa (sallal
Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa yaje ya
Yaqi Yahudawan Banu Qurayzah saboda karya
alkawarin da sukayi, Sai aka fita zuwa Qauyen da
suke. Su kuma Yahudawan tuntuni sun shiga
cikin garinsu wanda ke zagaye da doguwar
katanga, Kuma sun kulle Qofofin garin babu
damar shiga.
Don haka Manzon Allah (saww) ya umurci
Jaruman Sahabbansa (Allah ya yarda dasu) suka
zagaye garin babu shiga ba fita har tsawon
kwanaki goma sha hudu (14).
To yayin da Yahudawan na Banu Qurayzah suka
ga cewa lallai hallaka tazo garesu babu makawa,
sai suka aiko zuwa ga Manzon Allah (saww)
cewa sun mika wuya amma suna so a turo musu
Abu Lubabah (ra) zasuyi shawara dashi.
Da Abu Lubabah ya shiga cikin garin nasu sai
suka tattaro 'Ya'yansu da Matansu suna ta kuka
agabansa sannan suka ce masa "Hakika wannan
tsarewar da akayi mana ta tsananta garemu
kuma mun hallaka. Gashi kuma Muhammadu
(sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) ba zai
rabu da gefen Katangunmu ba, har sai mun
sauko bisa Hukuncinsa. Yanzu da zai kyalemu da
sai mu tafi zuwa Qasar Sham ko Khaybara.
Kuma ba zamu sake taimakon wasu su Yaqeshu
ba, Har abada.
"Shin me kake gani? Gashi mun za'bi muyi
shawara dakai Maimakon waninka. Kuma gashi
Muhammadu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa
sallam) ya qi yarda har sai mun sauko bisa
hukuncinsa".
Sai Abu Lubabah yace musu "Eh ku sauko bisa
hukuncinsa, (Yana fa'din haka sai yayi ishara
zuwa Makogoronsa, wato Yanka, ko kuma Kisa
shine hukuncin nasa).
Abu Lubabah yace "Ina gama gaya musu haka,
sai nayi nadama, nace "INNA LILLAHI WA INNA
ILAIHI RAJI'UN!".
Sai Ka'abu 'dan Ashrafu (Shugaban Yahudawan)
yace "Me ya faru gareka Ya kai Abu Lubabah?".
Sai nace "Ai na ha'inci Allah da Manzonsa ne
(saww)".
Sai na sauko daga garesu, gemuna ya jike da
hawaye. Mutane suna jiran dawowata alhali ni
kuwa nabi ta bayan katangar na koma garin
Madeenah na shiga Masallaci na 'daure kaina.
Nayi rantsuwa cewa ba zan sake cin abinci ko
shan ruwa aduniya ba, har sai Allah ya yafe mun
laifina ko kuma in mutu ahaka".
Yayin da labarina ya iske Manzon Allah (saww)
sai yace "KU KYALESHI HAR ALLAH YA
HUKUNTA ABINDA YASO GAME DASHI. AMMA
DA ACHE YAZO GARENI DA NA NEMA MASA
GAFARA. AMMA TUNDA BAI ZO BA, YA RIGA YA
TAFI, TO KU KYALESHI".
Ibnu Shihab Azzuhriy ya ruwaito cewa "Abu
Lubabah ya daure kansa acikin Tsananin zafin
rana (acikin Masallacin Manzon Allah saww)
babu ci babu sha har tsawon kwanaki bakwai.
Kuma yace "Ba zan gushe ahaka ba, har sai na
bar duniya ko kuma Allah ya karbi tubana".
Bai gushe ahaka ba, har sai da ya fara
numfarfashi (Saboda tsananin yunwa da wahala)
Annabi (saww) yana kallonsa safiya da maraice,
Sannan Allah ya karbi tubansa.
Sai aka ce masa "Hakika Allah ya gafarta maka".
Kuma Annabi (saww) ya aiko domin a kunce
masa 'daurinsa amma sai ya qi. Yace Shi babu
mai kunceshi daga daurinsa in banda Manzon
Allah (saww).
Sai Manzon Allah (saww) yazo shi da kansa ya
kunceshi.
Ibnu Shihab ya ruwaito daga Hindu bintul Harith
daga Nana Ummu Salamah (ra) tace "Naga
Lokacin da Manzon Allah (saww) yake kunceshi
daga daurin nasa, yana gaya masa cewa Allah ya
karbi tubansa amma ba ya fahimtar maganar
saboda tsananin wahala da kuma raumin jiki".
Acikin wata riwayar kuma ance yayi hakan ne
saboda yaqin Tabuka da bai je tare da Manzon
Allah (saww) ba.
DAGA ZAUREN FIQHU (07064213990). Domin
Qarin bayani game da wannan Qissar Aduba :
- TABAQATUL KUBRA ta Ibnu Sa'ad juzu'i na 3
shafi na 456.
- ALMAGAZIY na Imamul Waqidiy shafi na 101.
- KITABUT TAREEKH na Ibnu Ma'een juzu'i na 2
shafi na 723.
- AL ISABAH ta Ibnu Hajr, Tarjamah ta 10,471.
- SEERAH ta Ibnu Hisham juzu'i na 2 shafi na
255.
- TAHZEEBUT TAHZEEB Juzu'i na 12 shafi na
214.
- TARIKHUL KABEER juzu'i na 3 shafi na 322.
- ALBIDAYAH WAN NIHAYAH Juzu'i na 7 shafi na
223.
Fatanmu shine Allah yasa wannan Qissar ta
amfanar damu daku, da dukkan wanda ya
karanta.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By © ZAUREN FIQHU

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: