Monday 25 September 2017

Macen 'da ta fi kiba a duniya Eman Ahmed Abd El Aty ta mutu'

Tura Wannan Zuwa

Macen nan 'yar kasar Masar da aka yi ammana
ta fi kowa kiba a duniya ta rasu a Hadaddiyar
Daular Larabawa.

A farko shekarar nan ne aka kai Eman Ahmed
Abd El Aty kasar Indiya domin a yi mata tiyatar
rage kiba.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce an rage mata
kilogiram 300 cikin kilogiram 500 na kibar da
take da ita, amma ta rasu sakamakon
tabarbarewar da halin da take ciki ya yi.

Wata sanarwa da asibitin ya fitar ta ce macen,
'yar shekara 37, ta yi fama da ciwon zuciya da
na koda.

"Muna yin jaje ga 'yan uwanta," in ji sanarwar
asibitin.

Tun a watan Mayu ne aka kai Ms Abd El Aty
birnin Abu Dhabi bayan an yi mata tiyata a wani
asibiti da ke birnin Mumbai na kasar Indiya.

Kafin a yi mata tiyata, iyayenta sun ce ta kwashe
shekara 25 ba ta fita ko da kofar gida ba.

An dauke ta a wani jirgi da aka yi hayar sa zuwa
Mumbai domin yi mata tiyata bayan 'yar uwarta
ta nemi a tallafa mata a shafukan intanet.

Amma an dauke ta daga asibitin bayan danginta
sun samu rashin jituwa da hukumomin asibitin.
Dangin nata sun nuna shakka kan adadin kibar da
asibitin ya ce ya rage daga jikin 'yar uwarsu.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: