Sunday 24 September 2017

Maganar cewa ana lalata da mata a masana'antar Kannywood Karya ne, inji sabuwar jaruma A'isha Muhammad

Tura Wannan Zuwa Ga

Jaruma Aisha Muhammed ta bayyana cewa jita-
jitan dake yaduwa na cewa sai anyi lalata da
mata ake basu damar fitowa a shirin fim na
masana’antar shirya fina-finai na kannywood
karya ne kuma babu kamshin haka a
masana’antar.
Ta fadi haka ne yayin wani hira ta musamman da
tayi da Daily nigeria, Tana cewa;
“Tunda na shiga kannywood har na samu damar
damawa da gummain masana’antar ban taba
gani ko inji inda aka yi lalata da wani domin
samun damar fitowa a wani shiri, maganar banza
ce”.
Ni dai ban taba ganin inda haka ya faru tsakanin
jaruman masana’antar. Kowa yana aiki shi yadda
ya kamata kuma ma’aikatan suna bada nasu
taimakon kamar yadda ya kamata. Babu wanda
ya nemi ni da haka kuma ban taba gani da ido na
cewa ana ma wata haka.”
“Wasu yan hana ruwa gudu masu aikata ire-iren
haka ke neman gurbatar da wannan
masana’antar”.
Aisha wadda ta shiga masana’antar kannywood
cikin 2016 ta fara fitowa cikin fina-finai da dama
ciki har ma da wadda ta shirya da kanta.
Masu sharhi suna ganin cewa nan gaba Aisha
zata yi kakara cikin masana’antar da ire-iren su
Nafeesa Abdullahi, Rahama Sadau, Halima Atete
da dai sauran su.
Jaruma mai neman ficewa haifaffen yar garin
Jos dake jihar Filato ce amma tayi karatun
firamari da sekandere a garin Tafa dake jihar
Kaduna. Tana aji 5 a sekandere iyayen ta suka yi
mata aure.

Bayan fitowar ta daga gidan miji kasancewa
auren bai tafi yadda ya kamata shine ta nema
yadda zata fara harkar fim don tun tana yar
karama take da burin yin fim. Ta cinma burin ta
yayin da Usman Mu’azu na kamfanin express
media arts ya gabatar da ita cikin masana’antar
kuma shirin da ta fara fitowa a cikin shine
“safara” tare da fitaccen jarumi Adam A.Zango.

“Abun ya bani mamaki sosai da aka bani damar
fitowa tare da Zango, ban taba tunanin haka.
Kawai a waje na dauke shi cewa kaddara ce
daga Allah” inji Aisha.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Arewaloaded

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: