Sunday 24 September 2017

Kun san wanda ya mallaki kuɗin da EFCC ta gano a Lagos?

Tura Wannan Zuwa

Batun makudan kudin da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta gano a wani gida a birnin Lagos a farkon wannan makon, na cigaba da jan hankalin 'yan kasar.
Kudaden, wadanda suka kai N13b da EFCC ta ce jami'anta sun gano a unguwar Ikoyi bayan wani ya tsegunta musu cewa an jigbe su a gidan a nau'in dala da fam da kuma naira, sun sanya 'yan kasar na ta fadin albarkacin bakinsu, musamman a wannan lokacin da ake cikin matsin tattalin arziki.
Sai dai babban abin da ya fi jan hankalin 'yan Najeriya shi ne yadda aka 'rasa' masu wadannan makudan kudin.
Jim kadan bayan EFCC ta gano kudin ne dai, wasu rahotanni suka ce babbar jami'ar kamfanin mai na NNPC wacce aka kora a farkon mako, Mrs Esther Nnamdi-Ogbue ce ta mallake su.
Sai dai nan da nan ta fitar da sanarwar da take nisanta kanta da su.

Shi ma tsohon Shugaban jam'iyyar PDP, Alhaji Ahmadu Adamu Mu'azu, wanda aka ce gidan da aka kama kudaden nasa ne, ya ce ba shi da alaka da kudin.
Ahmadu Mu'azu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce gidan nasa ne amma ya sayar da shi kamar yadda ya saba, kasancewarsa dan kasuwar gidaje tun ma kafin ya shiga harkokin siyasa.
Ba su da uba
Tuni dai wata babbar kotun tarayya da ke birnin Lagos ta bayar da umarni a mika kudin ga gwamnatin tarayya a matsayin wucin gadi, kafin wani ya fito ya ce nasa ne sai a dauki mataki na gaba.
Hakan ne ya sanya 'yan kasar da dama, musamman a shafukan sada zumunta, ke yin kira ga EFCC ta tuhumi mutumin da ya tsegunta mata inda kudin suke.
Wani fitaccen mai sharhi a shafukan na zumunta, Japeth Omojuwa, ya ce babu yadda za a yi mutumin da ya tsegunta wa EFCC wadannan makudan kudade ya kasa sanin mutumin da ya mallake su.
Hasalima, a cewarsa, ta kwana gidan sauki tunda EFCC ta ce wanda ya tsegunta mata inda kudin suke, ya ce wata mata ce sanye ka tufafi marasa kyau ta rika ajiye kudaden.
Kudinmu ne
Sai dai wasu rahotanni na cewa kudin na hukumar tsaron ciki ce, National Intelligence Agency, NIA, wadanda tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya ba ta domin ta gudanar da wasu ayyukan tsaro cikin sirri.
A cewar rahotannin, tun ma lokacin da jami'an EFCC suka je gidan, shugaban NIA ya buga wa shugaban EFCC waya inda ya sanar da shi cewa kudin hukumar ne, amma Ibrahim Magu ya yi burus da hakan, inda ya bukaci jami'ansa su kama kudin.
Na yi kokarin jin gaskiya ko akasin wadannan rahotanni daga kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, amma bai amsa kiran wayar da na yi masa ba, sannan bai aiko min da amsar sakon da na aike masa ba.
Amma wani abu da ya kara cakuda wannan batu shi ne zargin da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi cewa kudin na jiharsa ne wanda tsohon gwamnan jihar kuma ministan sufuri na yanzu, Rotimi Amaechi ya sace a lokacin da yake mulki.
A wata hira da ya yi da manema labarai ranar Juma'a da daddare a birnin Fatakwal, Gwamna Wike ya ce kudin, wani bangare ne na kudin gas din da aka sayar lokacin mulkin Amaechi amma ya sace su.
Sai dai tun ma kafin Mr Wike ya yi wannan zargi, mai magana da yawun Mr Amaechi, David Iyofor, ya musanta cewa kudin na mai gidansa ne bayan wani mai magana da yawun gwamnan jihar Ekiti ya zargi tsohon gwamnan da mallakar kudin, yana mai cewa sokiburutsu ne kawai.
Mr Iyofor, a wata hira da muka yi da shi ta wayar tarho, ya kara da cewa za su yi wa manema labarai karin bayani kan batun nan ba da dadewa ba.
Da alama dai za a ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan wadannan kudade har lokacin da kotu za ta yanke hukunci a kan batun

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: