Saturday 16 September 2017

MUHIMMANCIN GOOGLE ACCOUNT (GMAIL) GA MASU WAYAR ANDROID

Tura Wannan Zuwa
Tabbas nasan Duk wanda ya mallaki wayar
Android, takan bukaci google account kafin ta
fara aiwatar da komai na daga gareta.
Wanda wannan gmail account yana da
muhimmanci ga masu wannan waya.
Domin kuwa GMAIL ACCOUNT Yana da sirrika da
kuma amfani sosai

GA KADAN DAGA CIKIN AMFANIN DA GMAIL
YAKE GA MASU RIKE WAYAR ANDROID

Da gmail Account ne zaka i,ya dawo da duk
kanin abinda ka goge ko ya fita misali wani
matsala ya faru da wayar ka wanda wannan
matsala takai ga har kayi ma wayar taka
RESTORE, ko PLASHING to matuqar kana da
wannan GMAIL din a wayar ka akwai hanyoyin da
xaka bi ka dawo da komai cikin wayar ka.

Da GMAIL ACCOUNT ne zaka i,ya bin diddigin
wayar kada aka sace koda kuwa barawon ya cire
sim card din ka ya jefar GMAIL account xai iya
taimaka wa wajen ganin duk inda barawo yake |
wannan hanyar munyi muku bayanin ta idan baku
manta va ta yadda xaka bi diddigin wayar ka da
aka sace ta wayar abokinka abinda

Da GMAIL Account ne zaka iya kulle wayar ka
da aka sace ta xamto barawon da ya sata wayar
baxa tai masa amfanin komai ba | idan kuma
kaga dama kayi FORMAT din wayar ta koda
wayar tana hannun barawon da ya sata wayar ne
Da wannan gmail account ne zaka samu damar
sauko da applications, videos, photos da wakoki
daga play store ko Market place na wannan
waya.

Da wannan gmail account ne zaka samu damar
juya sauran applications din data zo dasu.
Da wannan gmail account ne zaka bude
wayarka Android, yayinda ta kulle, wato idan
kasa ta acikin wannan key, sannan kuma wani
yazo ya danna maka ba dai-dai ba, zata bukaci
gmail account, to wannan wanda kasa mata shi
take bukata.
Rashin saka mata gmail account, zaisa kayi
asarar wayarka yayinda ta shiga wannan hali na
bukatar gmail account.
 karka manta password naka ka ajiyesu suna da
muhimmanci agareka, karka dauka kamar ko dole
ne akayi maka, tabbas ajiye tarihin wannan email
naka, da password naka, ka ajiyesu da kyau suna da rana.

Abinda ake nufi da google account shi ne gmail
account misalin google account
zeetown32@gmail.com
nafiukg@ gmail.com
nafiu3213@gmail.com
Wannan shi ne misalin Google account ko Gmail
account, ko Gtalk account.
ME ZAI FARU IDAN KA MANTA GMAIL DA
PASSWORD NAKA?

Idan kana amfani da Android phone, sannan
kuma ka manta gmail naka, da password naka
zai dawo idan ka san alternate email address
naka. Rashin sanin wadannan abubuwa zai baka
matsala akan wayanka, domin bazata dannu ba,
babu wani abu da zatayi, naga amfani dole saika
cire wannan google account da take bukata.

IDAN HAKA TA FARU ANA FLASHING?

Idan kana amfani da android sannan kuma ta
tambayeka wannan code nata kasa, kuma ka
manta shi, to karkayi mata flashing domin yimata flashing
bazai haifar da da mai ido ba, domin zaka rasa
wasu abubuwa nadaga wannan wayan naka,
domin wani applications din zasu fita kuma
bazasu dawo ba, sannan kuma zata samu matsala bangaren
browsing nata.

HIKIMAR AMFANI DA GMAIL AKAN ANDROID
Kamfanin da suke yin android sun kwaikwayi, kamfanin Apple ne
akan yadda suka tsara computar su da
wayoyinsu, dansu gane mai wayar da wanda ba
mai wayar ba, ta yadda da zarae ta shiga key, To mai itane kadai zai iya budeta, inkuma ya
kasa saidai aje kamfaninsu.

Amma akan samu matsala wajen sa wannan
email, idan kasa ba dai-dai ba, har tsawon sau goma ajere zasu gargadeka, da
cewar ka tsaya haka, amma idan ka ci gaba har
auwa 15, to imbakai wasa ba zatayi format na
komai nata, nan take zata kashe kanta. Ta mutu
kenan ko kuma kaje kamfaninsu dan samun
mafita.
Masu saida wayar Android, kuna iya kokarinku
wajen budewa duk wanda ya sayi wannan waya
daga gareku, amma ku kara kokari, wajen
fahimtar da mutum muhimmancin wannan gmail
a wurinsa, da wayarsa. Sannan ku bashi
bayanansa ya ajiyesu na email nasa, saboda
faruwar matsala gaba.

Da fatan wannan dan bayani zai muku amfani
domin neman karin bayani sai ku neme ni ta
[ 0814084h10290]

Source: NAFIU KG BAZAZZAGE
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user