Friday 15 September 2017

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai kai Ziyara America a ranar Lahadi mai Zuwa

Tura Wannan Zuwa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je
birnin New York na Amurka a ranar Lahadi,
domin halartar taron kwamitin koli na Majalisar
DInkin Duniya, MDD, karo na 72, tare da sauran
shugabannin kasashen duniya.
Abu mafi muhimmanci a ziyarsa tasa shi ne
jawabin da zai gabatar yayin muhawarar, inda
zai bayyana matsayar kasar.

A wata sanarwa da mai bashi shawara kan
harkar yada labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce
babban dalilin halartar taron da shugaban zai yi
shi ne gabatar da bayani a kan
Taken taron muhawarar na bana shi ne: 'Mayar
da hankali kan mutane: Kokarin samun zaman
lafiya da kuma Rayuwa mai kyau ga kowa da
kuma duniya mai cike da nutsuwa.'
Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin
duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio
Guterres, zai karbi bakuncinsa.
Haka kuma, shugaban zai gana da Shugaba
Trump a yayin cin abincin rana, tare da sauran
takwarorinsa na sauran kasashen duniya.
Daga cikin manyan tarukan da Najeriya za ta
halartar a yayin babban taron, har da wanda zai
tattauna hanyoyin hana sa mata karuwanci da
cin zarafinsu.

A lokacin taron, shugaba Buhari da 'yan
tawagarsa zasu yi kokarin nuna Najeriya a
matsayin wata mai kima, wadda ta san inda
kanta ke mata ciwo, cikin jerin kasashen duniya.
Haka nan za a kara jaddada kokarin da Najeriyar
ke yi wajen tabatar da dorewar zaman lafiya, da
tsaro da kuma ci gaba a duniya, haka kuma idan
bukatar hakan ta taso, a nemi karin hadin kan
kasashen duniya a yaki da cin hnaci da rashawa

Sauran batutuwan da Najeriya za ta fi mayar da
hankali kansu har da karfafa hukumomin kare
hakkin dan adam da bin doka da kare 'yan gudun
hijira sakamakon ayyukan ta'addanci da
ambaliyar ruwa da kuma sauyin yanayi.
Cikin tawagar da za su yi wa shugaban rakiya
har da gwamnonin jihohin Zamfara da Ebonyi da
Ondo da kuma wasu manyan ministocinsa.

A kan hanyarsa ta dawowa, shugaban zai tsaya
a Landan.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: