Friday 15 September 2017

Korar da aka yimin a Kannywood Gaba takai Ni-Rahama Sadau

Tura Wannan Zuwa Ga

Fitacciyar jarumar nan ta wasan
kwaikwayon Hausa da turanci wato ta
Kannywood da Nollywood Rahama
Sadau ta bayyana cewa korar da aka yi
mata daga masana’antar shirya fina-
finai ta Kannywood ta daga ta zuwa
mataki babba sannan kuma ta budo
mata kofofi na alkairi.
Jarumar wacce ta bayyana haka a wata
hira da tayi da jaridar Guardian inda ta
bayyana cewa duk da dai abin bai yi
mata dadi ma, hakan kuma ya kara
haska ta a idon duniya.
“Kawai daga na taba wani a yayin
gudanar da shiri sai ace na karya doka.
A tunanina koma mene kayi ai kai da
ubangijin kane. Duk abinda nake yi ai
ina kokarin kiyaye hakkokin addinina
da kuma al’adar yankin da na fito.
Saboda haka bana tunanin na cancanci
hukuncin da aka yi mun a matsayin da
nake. ”
Jarumar ta bada dan takaitaccen
tarihin rayuwar ta ta baya inda ta
bayyana cewar ta kasance tana sha’awa
tare da yin rawa tun lokacin da take a
matakin karatu na primary har ya zuwa
matakin karatu na sakandire.
Ta kara da cewar ba’a irin kowanne
film take fitowa ba inda ta bayyana
cewar ta sha kin karbar roles da yawa
da take ganin sun ci karo da al’adar
yankin da ta fito. Daga ciki akwai inda
aka taba yi mata tayin ko zata iya
fitowa a matsayin yar madigo(lesbian)
wanda ita taki karba don kare
mutuncinta.
An tambaye ta shin ko akwai bambanci
a yanayin gudanar wasan kwaikwayo
tsakanin Kannywood da Nollywood?
Jarumar wacce ta fito a cikin wasu fina-
finan Nollywood kamar su The Light
Will Come, and Sons of the Caliphate.
Ta bayyana cewa kusan duk tsarin daya
ne sai dai yan bambance-bambance da
ba’a rasa ba ta bangaren al’ada da
kuma yanayin mutanen gurin da ake
gudanar da harkar wasan kwaikwayon.
Wannan shine dan abinda
Arewamobile.com ta dan tsakuro muku
daga cikin hirar da jaridar Guardian
tayi da jaruma Rahama Sadau
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: