Sunday 1 October 2017

Shin ko Kasan Jerin Sunayen Mutane 9 da zasu iya maye gurbin Kujerar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari???

Tura Wannan Zuwa Ga

Duk da dai akwai sauran lokaci kafin zuwan
zaben 2019 amma tuni masu fashin baki kan
harkar siyasa suka fara hasashen 'yan siyasan
da ka iya maye gurbin shugaban kasa
Muhammadu Buhari.

A wata rubutu da Fola Ojo ya yi wanda jaridar
Punch ta wallafa, ya lissafo 'yan siyasa da ke da
buri kuma suka cancanci maye gurbin kujeran
shugabancin kasa da Buhari ke kai a yanzun idan
zabe ya kewayo.

Ga jerin sunayen 'yan siyasan a kasa

1. Goodluck Jonathan
Duk da cewa tsohon shugaban kasan bai fito filli
ya bayyana ra'ayinsa na yin takarar ba, magoya
bayan sa sunyi imamin cewa akwai sauran aikin
da bai karasa ba a Fadar ta Aso Rock.

2. Rabi'u Musa Kwankwaso Sanata daga Jihar Kano kuma tsohon Gwamnan
Jihar. Rabiu Musa kwankwaso dai tun da dadewa
yana da burin zama shugaban kasa, yayi takaran
fida gwamani a jam'iyyar APC a shekarar 2014
tare da shugaba Buhari amma baiyi nasara a
wannan lokacin ba.

3. Aminu Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto kuma tsohon Kakakin
Majalisar Tarayya. Akwai rade-radin cewa tsohon
kakakin majalisan wakilan yana da sha'awar
takarar shugabancin kasar

4. Sule Lamido
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon
minstan harkokin kasar waje a zamanin mulkin
Obasanjo yana da gwarjini da zai iya zama
shugaban kasan a jam'iyyar PDP, a hasashen
Ojo, abin zai zo masa da sauki idan Atiku
Abubakar yayi nasarar samun tikitin takara a
karkashin jam'iyyar APC

5. Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasar dama ya
dade da bayyana ra'ayinsa akan takarar
shugabancin kasar. Amma a halin yanzu yana
jiran yaga matakin da shugaba Buhari zai dauka
kafin ya san matsayinsa.

6. Bola Ahmed Tinubu
Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a
jam'iyyar APC yana da dimbin magoya baya da
suke son yayi takarar shugabancin kasar.
7. Ayodele Fayose
Gwamnan Jihar Ekitin ya bayyana ra'ayinsa na
tsayawa takarar shugabancin kasar Najeriya duk
da matsalar da ke tsakanin sa da shugabancin
jam'iyyar PDP. Yayi alkawarin zaiyi aiki tukuru
idan aka zabe shi.

8. Nyesom Wike
Gwamnan Jihar Rivers dan siyasa ne wanda ke
da farin jini a idanun talakawa, wasu ma suna
masa lakabi da zakin Neja Delta. Duk da yafi
maida hankalinsa akan siyarsa yankin su wasu
masu hasashen sunce ba abin mamaki bane ya
tsaya takarar shugabancin kasar.

9. Rochas Okorocha
Gwamnan Jihar Imo yayi takarar fidda gwani a
jam'iyyar APC a shekarar 2014 inda ya zamo na
3, masu hasashe suna ganin idan dai za'a samu
shugaban kasa daga kabilar Ibo cikin yan
shekarun nan toh babu mamaki Rochas din ne
yafi dacewa.

NAIJ.com ta bada rahoton cewa za'a gudanar da
zaben shugaban kasa da na 'yan majalisan
dattawa nan da kwanaki 505 kasancewar
Hukumar zabe ta INEC ta fitar da ranar yin
zaben.

Shugaban Hukumar zaben wato Farfesa Yakubu
Mahmood ya sanar da cewan za'a gudanar da
zaben ne ranar Asabar 16 ga watan Febrairu ta
2019.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Aminu Ibrahim

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: