Saturday 23 September 2017

Za a fara koyar da ilimin jihadi a makarantun Turkiyya

Tura Wannan Zuwa

Makarantun Turkiyya sun fara sabuwar shekarar
karatu ta bana cike da takaddama sakamakon
gabatar da sabuwar manhajar karatu mai cike da
ce-ce-ku-ce, wacce aka cire koyar da ilimin
cewa halittar dan adam ta sauya ne daga dabba
zuwa mutum wato (Evolution), inda a madadin
sa aka gabatar da ilimin jihadi.
A ganin gwamnati mai kishin Islama ta Turkiyya,
an yi hakan ne domin sabbin dabi'un ilimi.

Masu suka sun yi tir da sabbin littatafan
makarantun a matsayin masu wariya kan jinsi da
kuma masu adawa da kimiyya, sun kuma sun yi
korafi cewa hakan koma baya ne ga tsarin ilimin
da ba ruwansa da addini.

Dan jam'iyyar hamayya ta CHP, Bulent Tezcan
ya ce: "Suna kokarin gurbata tunanin yara ne ta
hanyar saka karatun jihadi (a manhajar karatun
yara) tare da irin fahimtar da ta tsunduma Gabas
Ta Tsakiya cikin kashe-kashe."

Amman gwamnatin kasar ta soki 'yan hamayya
da kokarin yada bakar farfaganda a wani yunkuri
na raba al'ummar Turkiyya gabannin zabukan
shekara 2019.

"Idan muka ce dabi'u, suna fahimtar wani abu ne
daban. Muna alfahari da ra'ayinmu na 'yan
mazan jiya masu bin tafarkin dimokradiyya,
amman ba ma son kowa ya zama kamar mu," in
ji ministan ilimi Ismet Yilmaz.

Kwato jihadi daga masu jihadi
Ana bayar da littattafan da ke bayanai kan jihadi
a makarantun koyon sana'a na Turkiyyya,
wadanda aka fi sani da sunan makarantun Imam-
Hatip. Daga nan kuma za bai wa 'yan makarantar
sakandare zabin darasin nan da shekara daya.

An ware wani littafi mai suna 'Rayuwar Annabi
Muhammad (SAW)' domin yin tsokaci akai, kan
zargin cewa an tabo batun wariyar jinsi da kuma
bayanin kan jihadi da ya yi.

Kamus din cibiyar koyar da harshen Turkiyya ya
bayyana jihadi a matsayin "yakin addini." Amman
jami'an ma'aikatar ilimi sun ce kungiyoyin da ke
ikirarin jihadi irin IS mai da'awar kafa daular
Musulunci suna bata ma'anar jihadi domin cimma
wasu bukatunsu.

Ministan ilimin ya ce ya kamata a shigo da sunan
jihadi a matsayin wani bangare na addinin Islama
a mahangar "kaunar kasa".

Ministan ya ce: "Jihadi wani bangare ne na
addininmu. Nauyin da ya rataya a kanmu shi ne
mu koyar da ko wanne abu ta yadda ya kamata
tare da gyara abubuwan da aka yi wa mummunar
fahimta".

Har wa yau littafin mai cike da ce-ce-ku-ce ya
bayyana cewar mace ta yi wa mijinta "biyayya"
wani nau'i ne na "ibada".

Amman jami'an gwamnati sun ce wannan ba
abun mamaki ba ne tun da littafi ne na addinin
Islama kuma ya ambato ayoyi daga Alkur'ani.

"Allah ne ya fada, ba ni ba. In yi masa gyara ne,
ko mene ne?" in ji Alpaslan Durmus, wanda yake
shugabantar hukumar ilimi.

Amma an gudanar da manyan zanga-zanga biyu
a karshen makon da ya gabata, inda maudu'an
#NoToSexistCurriculum da
#SayNoToNonScientificCurriculum da kuma
#DefendSecularEducation suka yi ta jan hankulan
mutane a shafukan sada zumunta a Turkiyya.

Wani shugaban wata kungiya ya yi kira ga masu
zanga-zanga su ce"tir da sabuwar manhajar da
ta hana kimiyya a karni na 21".

'Yan hamayya sun zargi jam'iyyar AKP mai mulki
ta Shugaba Recep Tayyip Erdogan da maye
gurbin ginshikin jamhuriyar Turkiyya mara addini
da dabi'un Islama da na masu tsattsaruran
ra'ayi.

Kalaman da suhgaban kasar ya furta kan samar
da wata al'umma saliha sun janyo fargaba a
zukatan wasu.

Ma'akatar ilimin ta kuma ce masu suka "jahilai
ne" domin sun yi da'awar cewar an cire ilimin
cewa halittar dan adam ta sauya ne daga dabba
zuwa mutum wato (evolution) gabadaya daga
manhajar karatu.

Ministan ya ce za a karantar da wasu sassa na
ilimin rikidar halittar (evolution) a matakin
sakandare, amma ba da sunan na evolution ba.

Amman Aysel Madra daga cibiyar garambawul ga
Ilimi a Turkiyya na ganin yin hakan zai rudar da
yara ne kawai.
Kawunan kungiyoyin malamai ma sun rabu kan
muhawarar jihadi.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: