Tuesday 24 October 2017

Hausa Film: Ko Kadan Bazan Dawo Hausa Films ba-Mansura Isah

Tura Wannan Zuwa

Tsohuwar jarumar fina-finan Kannywood Mansura
Isa ta ce ba ta kewar rashin fitowa a fina-finan
saboda sai da ta kai kololuwar ganiyarta kafin ta
daina yin fim.

"Ina ganin ba na kewar fitowa a fim. Na kai
karshen ganiyata kafin na bar Kannywood.

Na
samu nasarori da dama; na gina gida na kaina,
na sayi mota, na je Umra, hasalima na auri
jarumin Kannywood.

"Me zan ce bayan haka idan ba godiya ga Allah
ba", in ji Mansura a hirar da ta yi da jaridar
Premium Times wacce ake wallafawa a intanet.

Tsohuwar jarumar, wacce ta ce ita ce edita ta
farko a masana'antar Kannywood, ta kara da
cewa ta daina fitowa a fina-finan ne lokacin da
ta yi aure saboda ta kula da iyalinta.

A cewarta, yanzu ba ta kallon fina-finan na
Kannywood saboda ba ta da isasshen lokaci na
yin hakan.

"Ina kallon fim ne kawai idan yana da matukar
inganci.

Amma ina kallon fina-finan series da ake
nunawa a gidajen talbijin", in ji Mansura.

Ta ce zai yi wuya ta koma fitowa a fina-finai
saboda yanzu tana gudanar da wata gidauniya,
"ko da yake ana biya na na rubuta fina-finai na
bai wa mashu shirya fina-finai su yi fim a
kansu".

Mansura ta ce jaruman yanzu sun fi na da irinta
kokari saboda akwai tsaro mai kyau kan yadda
ake yin fina-finai a yanzu.

"Mun sha wuya matuka lokacin da muke fitowa a
fina-finai; babu tsari mai kyau, babu ci gaban
fasaha, muna fitowa a fina-finai ne kawai domin
debe kewa.

Ina so na gaya maka cewa na sha
fitowa a fina-finan da ba a rubuta ba.

Mai shirya fim ne kawai zai gaya min abin da zan
fada da baki.

Amma yanzu ana bai wa jarumai
rubutaccen fim din da za su fito domin su yi
bitar abin da za su fada wata da watanni kafin a
soma nadar fina-finan", in ji tsohuwar jarumar.

A yanzu dai Mansura ta fi mayar da hankali ne
wajen kula da iyalinta da kuma kula da wata
kungiyar agaji mai zaman kanta da ta kafa mai
suna Today's Life Foundation.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: