Tuesday 24 October 2017

Siyasar Kano: Ina taya Kwankwaso Murnar Cika Shekaru 61-Dr Umar Ganduje

Tura Wannan Zuwa

Duk da sa-toka-sa-katsin da ke ƙara ƙazanta
tsakanin Limamin Kwankwasiyya Sanata Rabi’u
Musa Kwankwaso da kuma Na’ibinsa Gwamna
mai ci a yanzu Dakta Abdullahi Umar Gnaduje,
hakan ba hana jagoran Gwamnatin Kano a halin
yanzu taya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
murnar cikarsa shekara 61 a duniya ba.

Wannan
ya biyo bayan wayar gari da aka yi da ganin
tallan wannan taya murna a wasu Jaridun ƙasa
na ranar Lahadin nan.

A madadin ni kaina da iyalaina da al’ummar Kano
muna taya tsohon Gwamna Kano kuma Sanatan
Kano ta tsakiya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Murnar cika shekara 61 da haihuwa, muna fatan
Allah ya ƙara lafiya tareh da juriyar yin abubuwan
da zai amfani al’ummar Kano da ƙasa baki ɗaya,
muna ƙara jadadda taya ka murnar cikar ka
shekara 61 kamar yadda sanarwa ta nuna.

Wannan sanarwa ta zama wani abin tattaunawa
a tsaknin al’umma, kasancewar tukunyar siyasa a
Jihar Kano ta fara tafasa musamman zafafan
kalamai da aka sha ji daga bakin magoya bayan
fitattun ‘yan siyasar biyu kuma aminan juna a
baya.

Ko shakka babu wannan sanarwar taya murna
zata bar jama’a da tambayoyi masu yawa,
musamman ganin har yanzu Gwamna Ganduje
duk da kalaman da aka sha ji waɗanda ke
bayyana raba hanya tsakanin aminan junan biyu,
domin anji daga bakin Gwamnan na nunacewa ba
zasu yarda da ayyukan Ƙuniyar Kwankwasiyya ba,
harma a wani lokaci aka ji yana korar wasu da
kalmar yadda ake korar Kaji da Kalmar as-as.

Yanzu sai dai a jira a ga abin da zai ture wa
Buzu naɗi.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Leadership Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: