Wednesday 18 October 2017

Karanta Kaji Sirrin:: Abinda Sharif Momoh yayi wa Umma Shehu to Babu Wanda Zai kuma Amsa Gayyatar Arewa24-TV A Kannywood-Cewar Masu Kallon Hausa Films

Tura Wannan Zuwa Ga

A kwanakin nan ne, na ci karo da wani batu da
yake yawo a farfajiyar shirin finafinan Hausa ta
Kannywood, wanda a yanzu ya bazu ko’ina a
cikin al’ummar Hausawa.

Batun dai na wani faifan bidiyo ne da Babban
Jarumi kuma Dan Jarida Aminu Aliyu Sharrif
(A. A. Sharrif), wanda aka fi sani da Momoh ya
yi tare da jarumar mai tsashe Umma Shehu.

Aminu Momoh yana gabatar da wani shiri kan
finafinan Hausa a gidan Talbijin na ‘Arewa-24’
da yake hira da jaruman ‘yan fim. A wannan
karon Jaruma Umma Shehu ce bakuwarsa a
cikin shirin. A yayin da suke tattaunawa ne
kwatsam Momoh ya jefo mata wasu tambayoyi
da suka shafi tarihin addinin Musulunci, wanda
daga nan ne kallo ya koma sama, inda jarumar
ta kasa amsa su yadda ya kamata.

Tambayar farko da Momoh ya yi wa Umma,
kamar yadda bidiyon mai tsawon sakan 30 ya
nuna, ya nemi jarumar da ta fadi sunan matar
da ta dauki dawainiyar renon Fiyayyen Halitta
Annabi Muhammadu (SAW), bayan da
mahaifiyarsa Nana Amina (as) ta yi wafati.

Maimakon a ji cikakkiyar amsa daga bakin
jarumar, sai ta daburce, aka ji ta tana fadin:

‘Yaya za mu zo nan kuma? Yaya za ka yi mani
haka? Sai ta tintsire da dariya…

Dan jarida bai tsaya nan ba, ya kalle ta cikin
idanunta kana ya ce, “Kamar yaya zan miki
haka? Ai magana ce ta addini…,” in ji shi.

“Ai wannan… ka bar wannan maganar. Don
Allah ka bar ta,” cewar jaruma Umma Shehu.

Momoh ya kara kallonta, “Kin sauke Alkur’ani?”

Ta daga hannuwanta sama, tare da nuna
tsananin mamakin irin tambayoyinsa, “Ban
sauke ba.”

Har ila yau Momoh ya cira kai ya kalle ta,
“Izufinki nawa?”

“Aaa mu ba izufi ba suke koya mana ba, mu
dai ana mana Alkur’ani…”

“Gaba daya a yi ta tafiya kawai,” in ji Momoh a
daidai lokacin da ya katsi hanzarinta.

“E, za dai a buda Alkur’ani dai,” Umma ta
tabbatar.

“Hadda ko a karatu ko kuwa…?” in ji shi.

“E hadda din ma haka ne,” ta bayar da amsa.

A lokacin da faifain Bidiyon ya fada a dandalin
sadarwar ‘WhatsApp’ cikin Soshiyal Midiya,
kafin kiftawa da Bisimillah aka rika ce ce ku-ce
a kai, don kuwa Bidiyon ya shiga kowane lungu
da sako a tsakanin al’ummar Hausawa.

Har ma
sai da wasu suka fassara hirar a cikin harshen
Ingilishi, suka rika tura wa ko’ina a dandali. A
nan ana tafka muhawara a zauruka da dama
na intanet.

Mafi akasari kamar yadda binciken da aka
gudanar ya nuna shi ne ana bayyana takaici da
yin tir da abin da jaruma Umma Shehu ta
aikata.

Wasu na cewa ta bayyana kanta a matsayin
jahila tibis, wadda ba ta ma san usulin
addininta ba, balle ma ta san tarihin fiyayyen
halitta Annabi Muhammadu (SAW).
Hakan kuwa bai tsaya a kanta kadai ba, da
dama wasu jama’ar na kara yi wa dukkanin
jaruman finafinan Hausa musamman mata
kudin goro. Ana mu su kallon marasa ilmin
addini, kai hatta na zamanin ma ana ganin
suna da nakasu a wuare da yawa.

Wasu kuma ganin babu abin da ‘yan fim suka
sani illa fitsara da yada alfasha a cikin
al’umma.

A gefe daya kuma, binciken ya nuna yadda
dandalin Soshiyal Midiya din ya cika makil da
jinjina gami da marhabin da shirin da Aminu
Aliyu Sharrif Momoh yake gabatarwa a tashar
talbijin din. Da dama suna yabawa da
bajintarsa wajen dora Umma Shehu a tsaka
mai wuya.

A hakikanin gaskiya dai al’umma ta yaba, tana
kuma ci gaba da yabawa bajinta da kwarewar
dan jarida Momoh a kan wannan batu.

Sai dai kuma ba a rasa wasu kuma da ke ganin
rashin dacewar abin da dan jaridan ya yi ba.

Kana suka nuna damuwarsu kan halin da
jaruma Umma Shehu ta tsinci kanta a ciki.

Za mu iya fitar da abubuwa masu yawa a kan
wannan baragadar da ke faruwa a kullum a
cikin masana’antar finafinan Hausa.

Amma a wannan karon za mu dan takaita
tattaunawar tamu ne kacokan a kan faifan
Bidiyon Momoh da Umma Shehu, wanda a
yanzu shi ne ya dauke hankula a Soshiyal-
Midiya.

Kafin mu kalli irin kwafsawar da jarumar ta yi
a hirar, ya kamata mu yi fashin baki dangane
da bangaren shi kuma dan jarida.

Bisa adalci da kyakkyawar nazari dai, shakka
babu za mu iya cewa a kaikaice, dan jarida
wato Momoh ya yi wa wannan jarumar cin
fuska, domin bai dora tambayoyinsa a cikin
muhallinsu ba.

Dalili shi ne duk lokacin da za
ka gabatar da shiri, kana da iyaka daidai inda
shirin ya kunsa.

Tilas ka fayyace wa masu karatu ko kallo, ko
kuma sauraren abin da shirinka ya kunsa kuma
ka tsayu a kai. Misali, idan kana gabatar da
shiri a kan harkar zamantakewar iyali, ba daidai
ba ne bayan ka gayyaci magidanci, kuna
tsakiyar hirarku a kan maudu’in zamantakewa,
sai a ji kwatsam ka jefa masa tambaya a kan
harkar siyasa, ko nemi jin wane ne shugaban
wata jam’iyya… Ko ka gayyaci babban malamin
addini, kuna tattaunawa sai ka tambaye shi
wane ne ya mallaki kungiyar Aresenal ko Real
Madrid da sauransu?

Ka ga dai na farko, ba zai taba tsammanin za
ka yi masa irin wannan tambayar ba, saboda
ba wannan ne ya kawo shi cikin shirin naka ba.
Tilas ya rikice har ma kwakwalwarsa ta kasa
daidaituwa a kan abin da kake bukata a take a
lokacin.

Don haka tambayar farko da za mu yi wa
Momoh ita ce; Me ya sa ya kawo tambayoyin
addinin Musulunci tsantsa irin wadanda ya yi
wa jarumar, a cikin shirin hira da taurarin
Kannywood?

Duba da cewa shirin bai kunshi abin da
masana ke kira hatsin-bara ba, ma’ana tabo
kowane irin abu na bangaren rayuwar yau da
kullum, misali: Siyasa, harkokin mulki, addini,
wasanni da sauransu ba, Don haka sam bai
kamata dan jaridan ya yi amfani da damarsa
wajen tadiye kafar bakinsa a cikin shirin da ya
gabatarwa ba.

Hakan za ta iya sa taurarin ko wadanda ya
kamata su rika shiga shirin daga cikin masu
ruwa da tsaki a harkar fim su kauracewa shirin
kwata-kwata.

Ba don komai ba, sai gudun irin hakan.

Kafin ka gayyaci mutum zuwa Situdiyo don
tattaunawa, dama ya san maudu’in da za ku
zauna da shi a kai.

Sannan ka’idar aikin jarida ta nuna cewa ka
mutumta bakonka, ko wanda kake neman
bahasi a gare shi, domin ya samu sukuni, kana
ya ji dadin ba ka dukkanin bayanan da kake
bukata.

E, kwarai Momoh zai iya mayar da shirinsa ya
koma ‘Tsaka mai wuya’ sannan ya tallata cewa
zai iya yi wa bako kowace irin tambaya, kama
daga harkar siyasa, addini, fim, kasuwanci da
sauransu.

Hakan zai iya ba wa duk wanda aka gayyata
damar fadada tunaninsa game da kowane
bangarare, sabanin irin wannan sabi-zarcen da
ya yi wa jaruma Umma Shehu.

Ta gefen ita kuma jarumar kuwa, sai mu ce
rikicewar da ta yi a lokacin da aka yi mata
tambayoyin ne suka haifar mata da matsaloli
da al’umma.

Amma da ta tsayawa kyam ta yi, ta ajiye
hankalinta waje guda, da ba za ta fuskanci
wannan kalubalen da ta samu kanta a ciki ba.

Maimakon hakan da ta yi, da ta mayar da
tambayar ga dan jaridan, sai ta nuna masa
cewa ba halarci shirin taurarin fim don ta yi
fashin bakin abin da ya shafi tarihi a addinin
Musulunci ba. Kun ga kenan da za ta iya daure
dan jarida igiyar wuyarsa.

Kada mu manta kidimewa da rudewa su na sa
mutum ya rasa gane hakikanin abin da ake so
ya gane a cikin dan kankanin lokaci.

Ga wani
babban misali nan, a shekarun baya a kasar
nan, mun shaidi wani abu da ya faru, da har
wani shugaba ya kasa kawo Suratul-Fatiha. Sai
mu tambayi kanmu, shin kwatakwata ne bai iya
karatun Suratul-Fatihar ba? Ko bai taba zuwa
makarantar Islamiyya a rayuwarsa ba?

Amsa ita ce, Alkur’ani wato littafi mai Tsarki
yana tattare da manyan mu’ujizozi, wadanda
da wahalar gaske dan adam ya iya riskarsu a
zama daya, face wadanda Allah Ya zaba a
cikin Manzani da kuma fitattun Salihan
bayinSa.

Ko kai kanka ma za ka iya tabbatar da hakan,
don ba abin mamaki ba ne wani lokacin ka
kasa kawo wata ayar daidai yadda take, ba
kuma don ba ka haddace ta ba, a’a sai domin
za ta iya shige maka duhu sai ka sake yin
tilawa ko muraja’a.

Shakka babu dan jarida ya tafka babban
kuskure wajen yi wa shirinsa gamin-gambiza,
sannan ya so ya tozarta ‘yar’uwarsa ‘yar fim,
sai aka yi rashin sa’a ya rufta cikin ramin! Tun
da har ta kasa bada amsar da ake bukata,
kenan ba ita kadai ce al’umma za ta kalla ba,
dukkanin ‘yan fim din ne za a iya cewa ba su
da ilimin addini, ciki kuwa har Aminu A. Sharrif
Momoh!

An wallafa wannan makalar a jaridar
Leadership A Ranar JUMA’A a shafina da ke
fitowa duk ranar Jumma’a, wato BULALIYA

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Al-Amin CiromaA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: