Wednesday 18 October 2017

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.

Tura Wannan Zuwa

Kashi na Uku

Can da Yammaci, sai suka aika manzonsu zuwa
ga Mai unguwa Mallam Na-marwa, da cewar "Mu
turawa da muka zo wannan birni ayau, muna son
ka sanar da dukkan larabawa mazauna birnin nan
naku cewa muna son su hallara a gabanmu
manyansu da k'ananunsu har da bayinsu baki
ɗaya suna masu biyayya ga umarnin mu".

Ai kuwa koda mai unguwa ya labarta musu
umarnin turawa, sai suka ce "munji kuma munyi
biyayya." Nan take kuwa suka fara taruwa a
kofar fadar kano.

Da larabawan nan suka gama hallara, sai turawa
suka fito a garesu, suka zauna reras akan kujeru
suna fuskantar larabawan da suma suke a zaune.

Shugaban turawa ya kira tafintansa wanda bamu
san sunan saba, sannan yace ya tsaya a tsakiya
domin soma aikinsa. Daga nan sai akace masa
ya tambayi larabawan nan cewa iya su kaɗai
kenan mazauna wannan birni?

Tafinta ya sauya harshe gami da tambayar
larabawa kamar yadda aka umarceshi. Take sai
larabawa auka amsa da cewar "Iya mu kaɗai
kenan, in banda matayenmu da kananun yara da
muka bari a gida."

Nan ma tafinta ya fassarawa turawa abinda suka
faɗa.

Sai kuma turawa suka kara cewa ku faɗawa
waɗannan mutanen cewa "Yaku bak'i mazauna
wannan kasa, babu damuwa da zata riske ku. Ba
muzo domin kuba, ko kuma domin wanin kuba.

Ba kuma kusan dalilin zuwan muba, ko kuna da
masaniya game da haka?"

Da larabawa suka ji haka sai suka amsa da cewa
"Ya shugaba, mu fatake ne kurum waɗanda
kaduwanci ya kawo mu wannan kasa don haka
Ɓbamusan komai game da harkar (sarauta)
gwamnati ba"

Sai shugaban Turawa ya sake cewa "kuyi sani
yaku larabawa, zuwan mu wannan kasa yana da
sila da kuma dalili. Mu mutanen yammaci ne,
kuma muna da wani ɗan uwa da ake kira Bature
mai Launi. Shi ya kasance shugaban mune
wanda ya zauna a wani gari mai suna 'Kafin-
Yamusa'.. Ko kuna da masaniyar haka?"

Sai larabawa suka amsa da cewar "kwarrai munji
labarin haka".

Sai shugaban turawa ya cigaba da cewar
"Hakika, ɗanuwanmu yazo wannan kasa ya samu
sarkin kasar Mai suna Magaji ɗan Yamusa wanda
ya karɓeshi cikin girmamawa da kulawa tare da
martabawa. Ya zauna tare dashi da alkawarin
zasu taimaki junansu. Watarana, marigayi
ɗanuwanmu yana zaune, shi bai san cewa
magauta sun shiga tsakaninsu da magaji ɗan
Yamusa ba, sai kurum Magaji ɗan Yamusa ya
shigo gareshi tare dayi masa kisan gilla ba tare
da ɗanuwanmu ya aikata masa wani kuskure ba.

Bayan haka, sai Magaji ɗan yamusa ya rugo
izuwa ga sarkin kano Ali alokacin da yaji muna
nan tafe domin neman mafaka.

Shikuma Sarkin
kano Ali sai ya bashi mafaka tare da ɗaukaka
darajarsa, har ya bashi muhalli mai kyau, da kuɗi,
da bayi da dawakai na hawa.

Munji wannan labari ne daga mutane dangane da
abinda Sarki Ali ya yiwa wanda yayi mana laifi,
kuma mun kamu da matsanancin ɓacin rai
dangane da haka.

Don haka muka zo nan da fatan mu kama Sarki
Ali da abokinsa Magaji ɗan Yamusa. Gashi munzi
kuma bamu tarar dasu ba".

Shugaban Turawa yaci gaba da cewa " yaku
larabawa ku sani cewar bani da labarin Sarki Ali
yayi tafiya izuwa sokoto. Kuma ina rantsuwa
gareku da cewar idan da mun san haka, kuma
mun tabbatar da hakan, da babu abinda zai kawo
mu wannan gari. Ina muku rantsuwa guda uku
abisa haka (wallahi, Tallahi, Billahi kamar yadda
yake a al'adar su larabawan wajen tabbatar da
abu na gaskiya).

Kuma Tabbas mun samu labarin sirri akan
hanyarmu ta zowa nan cewar Sarki Ali ya tafi
sokoto amma ban baiwa labarin amanna ba.

Amma da ace na gamsu dashi, da sokoto na nufa
ba nan ba.

Munzo nan ne kurum ta dalilin Sarkin Ali da
abokinsa Magaji, don haka ku kwantar da
hankalinku a game damu. Kada kuji tsoro, tabbas
ba zaku tozar taba, ba kuma zamu firgita kuba."

Daga nan sai turawa suka sake cewa "A yanzu
zamu tafi neman Inda Ali da Magaji suke. Idan
kuna da saye da siyarwa kuna iya cigaba dayi da
abokanan hurɗarku. Amma a tare damu da akwai
hatsi da zamu so ku nik'a mana shi a matsayin
abincin mu bisa son ranku ba bisa tilastawa ba".

Larabawan nan suka ɗauka baki ɗayan su cewar
"Munji kuma munyi biyayya da hakan, muna
muku marhaban lale tare da duk abinda kuka zo
dashi"

Shikenan, abinda akayi kenan. Daga nan sai
turawa suka fito da buhuna saba'in na hatsi, suka
umarci masu yi musu dakon kaya su ɗauka subi
larabawa dashi izuwa gidajensu.

Sukuwa larabawa, sai suka rarraba hatsin ga
iyalansu, suka umarcesu da su nika tsabar hatsin
nan da gaggawa.

Ai kuwa da yammacin wannan rana suka soma
aikin, kuma gari baiyi duhu sosai ba suka
kammala, a inda larabawan suka harhaɗa garin
tare da aikawa ga turawa suna sanar nusu da
cewa an kammala aiki.

Kwana biyu bayan haka, sai turawa suka sake
aikowa larabawa da buhunan hatsi guda dari
biyu, suna masu neman a nika musu su.

A wannan karon ma, iyalan larabawan sun
kammala aikin a yini guda.

Ai kuwa turawa sunyi matukar murna gami da
farin ciki da hakan, sun kuma yi godiya sosai ga
larabawan.

Bayan haka, sai turawa suka yanke shawarar fita
domin neman Sarkin Kano Ali da abokinsa Magaji
ɗan Yamusa.

Bayan sun gama shiri sai suka fita daga kano,
amma sun bar wasunsu waɗanda zasu tsare
gari. Su kuwa sai suka nufi sokoto.

Akan hanyar sune sukayi kiciɓus da wasu
dakarun Kano waɗanda suke dawowa daga
sokoto (Ainihinsu tare suke da Sarki Ali, amma
saboda yaji labarin turawa sai ya sulale ya
barsu. Zakuji labarin su a gaba).

Waziri Amadu ne ke jagorancin wannan tawaga,
anyi wannan haɗuwa ne kuma a wani daji da ake
kira 'Dajin Rubin' (Tana kuma iya yiwuwa turawa
ne suka sanyawa dajin wannan suna saboda
mutuwar ɗanuwansu Reuben a dajin)
Da gamuwar su sai faɗa ya kaure a tsakani.

Aka
soma fafatawa, dakarun waziri Amadu suna
afkawa turawa da sara da suka, yayin da suma
turawa suka mayarwa da dakarun martani da
harbi.

Sai dai cikin abinda baifi awa ɗaya ba, turawa
suka karya lagon wanna tawaga suka kuma
watsa ta.

Ya zamana an kashe wasu, wasu kuma
suna zube a kakkarye harsashi yayi misu lahani,
yayin da saura suka shige daji da gudu suna
masu neman tsira da rayukansu..

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: