Friday 20 October 2017

Za'a Hukunta duk Masu Yada Hadisai na 'Karya-Saudiya

Tura Wannan Zuwa

Gwamnatin Saudiyya za ta kafa wata sabuwar
cibiyar addini wacce za ta hana masu
tsattsauran ra'ayin Musulunci da kuma 'yan
ta'adda jirkita wasu Hadisai domin aikata
danyen aiki.

Mahukunta a kasar sun ce ''yan ta'adda" na
gurbata fassarar hadisan Annabi Muhammad
(SAW), domin kafa hujja da su wajen munanan
ayyukan da suke yi.

Sarki Salman ne ya sanya hannu kan wani
kudurin dokar wanda ya bayar da damar kafa
wannan cibiya.

Kuma jami'an sun ce cibiyar za ta kasance ne a
birnin Madinah mai tsarki.

Za a dauki Malamai kuma masana addinin
Musulunci daga sassan duniya daban daban
wadanda za su jagoranci cibiyar.

Za kuma su rinka aiki tukuru domin zakulo da
kawar da duk wani Hadisi da ke da alamun kage
ko wanda aka sauyawa ma'ana domin kafa
hujjojin tayar da fitinah.

Mata za su fara ba da fatawa a Saudiyya
An hana malamin Saudiyya wa'azi saboda cin
fuskar mata

An dade ana zargin kungiyoyin masu tayar da
kayar baya kamar su Al'Qaeeda da IS wajen
sauya ma'anar ayoyin Al'Kur'ani da Hadisai
domin kafa hujja kan ta'asar da suke aikatawa.

Wannan mataki na zuwa ne watanni kadan bayan
ziyarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya
kai kasar ta Saudiyya, inda mahukunta suka yi
masa alkawarin kawo gyara a yadda suke
tunkarar batun tsattsauran ra'ayi.

Wasu dai na zargin cewa wadannan sauye-sauye
ba za su rasa nasaba da matsin lambar da
Amurka ke wa kasar ba, na ganin ta sauya yadda
take tafiyar da al'amuranta na addini.

Sai dai jami'an Saudiyya sun musanta irin
wadannan zarge-zarge.

Akwai dubban Hadisai da Annabi Muhammad
(SAW) ya bari, da musulmai ke ci gaba da
amfani da su wajen kara fahimtar addinin.

Baya ga Al'Qur'ani mai girma, Hadisin Annabi
(SAW) shi ne mafi muhimmanci a tsarin shari'ar
addinin Islama, amma ana samun wasu Hadisan
da ake jirkita ma'anarsu, ko kuma wadanda ba su
da asali.

A don haka ne Saudiyya da sauran kasashen
musulmi suka ci gaba da nuna damuwa.

Sheikh Abdulrazak Ibrahim, Limamin Masallaci
Unguwar Seven Sisters a arewacin London, ya ce
dokar za ta iya yin tasiri sosai.

Ya shaida wa BBC cewa "Tana da muhimmanci"
ganin yadda aka ce malaman da za su kula da
cibiyar za su fito ne daga kasashen Musulmi da
dama..

Sai nan gaba ne za a bayyana cikakken tsarin da
za a bi wurin aiwatar da cibiyar da kuma lokacin
da za ta fara aiki.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source: ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: