Friday 20 October 2017

Umarnin Shugaba Muhammadu Buhari: A dakile tashe-tashen hankula da ake samu a wasu sassan jihar Jos-Muhammadu Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga

Rundunar sojin saman Najeriya ta tura jiragen
yakin sama da jami'anta zuwa Jos, babban birnin
jihar Filato domin tallafa wa rundunar tabbatar
da zaman lafiya da ke aiki a jihar.

Sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce hafsan sojin
saman kasar, Air Marshal Siddique Abubakar ne
ya bayar da umarnin tura jiragen yakin a wani
mataki na bin umarnin Shugaba Muhammadu
Buhari na cewa a dakile tashe-tashen hankula da
ake samu a wasu sassan jihar.

Rundunar sojin saman ta tura jirgin sama
samfurin L-39ZA da kuma jirgi mai saukar angulu
samfurin EC-135, wadanda za su bayar da kariya
ga rundunar da ke aikin tabbatar da zaman lafiya
a jihar.

Wannan dai ba shi ne lokaci na farko da rundunar
sojin saman Najeriya za ta tura jiragen yaki wani
bangare na kasar domin tallafa wajen tabbatar
da zaman lafiya ba.

Wannan na zuwa ne sakamakon tashe-tashen
hankulan da ake samu na baya-bayan nan, inda
aka kashe a kalla mutum 35 aka kuma jikkata
wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu
kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato
a ranar Lahadin da ta gabata.

Tun a lokacin ne kuma Shugaba Muhammadu
Buhari ya nemi sojojin kasar a kan su tashi tsaye
wajan daukar matakan dakile tashen-tashen
hankula da suka dawo a jihar ta Filato.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: