Friday 20 October 2017

KARANTA SALON SARRAFA MURYA A SOYAYYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Wata babbar ka'idace da take kara
inganci da
tasirin kalaman bayyana soyayya
tsakanin
masoya ita ce, yanayi da sigar da kalaman
ke fita su isa kunnen mai sauraren su.

Dole sai masoya sun rika sarrafa murya wajen
bayyana shaukin kaunarsu ga juna;
kowane kalami da irin sigar muryar da tafi
dacewa
da
shi:

 Kalaman nuna so da kauna ana furta su
gauraye da shaukin bege, cikin
bayyanannun kalmomi, wani sa'in ana iya furta
su cikin
yanayin wake, ko a siririntar da murya ko
a
nauyaya ta don ta yi daidai da lokaci da
kuma
yanayi.
Kalaman tausayawa, suna bukatar a
tausasa murya wajen furta su, a cakuda
murya kafin a bayyana jimamin abin da
ake
tausayawa dominsa.

Kalaman ban hakuri na bukatar a nauyaya
su da muryar da-na-sani, nadama da
marairaicewa.

Kalamana godiya na bukatar a kawata
furucinsu da farin ciki da jin dadin abin
da ake godewar.

Kalaman wasa da zaurance kuwa sai a
surka muryarsu da jin dadi da nishadi.

Kalaman sha'awa, ko dai a sa murya ta
yi
taushi yayin furucinsu, ko a sanyaya ta, ko a
siririnta murya, ko a sa murya ta yi kasa-
kasa,
ko a rika fitar da kalaman cikin rada, ko a
rika
fitar da su dai-dai cikin yanayi na jan hankali;
abin nufi dai, masoya su yi kokari su rika
karya murya cikin siga mafi dacewa da
lokaci
da kuma yanayi.

Kalaman sha'awa ba
lallai sai sun yi ma'ana ba wata sa'in, ana iya
caccakuda wasu kalmomi a fitar da su da
wani irin karin muryar sha'awa wadanda
zai
sa su yi tasiri sosai.

Kalaman neman alfarma sai a gauraya su
da muryar kwantar da kai da
marairaicewa.


Source: ©Fadila M. Idris
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user