Saturday 21 October 2017

Dole Ne a Yabawa Muhammadu Buhari-Atiku Abubakar

Tura Wannan Zuwa

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan umarnin day a bayar na a biya tsofaffin jami’an tsaro da suka yi yaki a matsayin ‘yan Biyafara wadanda aka yi wa afuwa.

BBC ta ruwaito cewa Atiku Abubakar ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter, inda ya ce, abin da Shugaba Buhari ya yi na nuna cewa akwai hadin kai a Najeriya.

A ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya amince da biyan fanshon ga jami'an 'yan sandan da gwamnatin Najeriya ta yi wa afuwa tun a shekarar 2000 lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Wadannan jami’an sun yi aiki ne a 'haramtacciyar' kasar Biyafra a lokacin yakin basasar Najeriya da aka shafe watanni 30 ana yi. Amma tun da da aka musu afuwar ba a biya su komai ba.

A wata sanarwa da wata hukuma wadda ke kula da biyan fanshon ta fitar ta ce, za a biya mutum 162 yayin da mutum 57 kuma iyalansu ne za su karba a madadinsu a biyan farko da za a yi.

Hukumar ta kuma ce za a fara biyan farkon ne ranar Juma'a 20 ga watan Oktobar nan a birnin Enugu da ke Kudancin Najeriya.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: