Wednesday 18 October 2017

Rayuwa: TARIHIN WALI DAN MARINA

Tura Wannan Zuwa

Unguwar Masanawa a birnin katsina shahararriya
ce koba komai saboda anan ne manyan Waliyai
masu karamomi suka wanzu a karni na goma sha
bakwai.

Wadannan waliyai sune; Wali Dan Marina
da kuma Wali Dan Masani.

Ance cikakken sunan wali Dan Marina shine
Muhammad Ibn al-Sabbagh.

Mahaifinsa balarabe
ne wanda ya taso daga gabashi ya kuma sauka act
katsina a gidan wani malami kuma attajirin
Marini mai suna Kayaba.

Wannan marini ance
shine yake yiwa Sarkin Katsina na lokacin
Mamuda da iyalinsa rinin tufafinsu.

Ana nan sai wata rana mahaifin wali dan marina
yaga 'yar Sarki Mamudu wadda ake kira da
baraka, yaji kuma ta kwanta masa. Don haka sai
ya nemi aurenta, sai kuwa aka kuma aura masa
ita akan sadaki zinare shidda. Suka tare a gidan
kayaba.

Bayan kimanin wata biyu sai Mallam
Muhammadu mahaifin wali dan marina ya tashi
izuwa gabas, ya bar baraka da cikin wali dan
marina. Ita kuwa sai Allah yayi mata rasuwa
kafin ta haihu, sai kuwa akaje aka binne ta a
haka a kusa da wata bishiyar Marina.

Allah da ikonsa, sai ya Kadarta aka haifi Wali
Dan Marina acikin kabarin nan na kusa da marina
yana shan maman mahaifiyarsa a kabarin. Sai ya
kasance yana fitowa lokaci lokaci yana yin wasa
da dagwalon tukwanen baba, har wata rana
mutane suka faki idonsa aka dauke shi riko wurin
Wali Dan Masani, mai suna Mallam Abduljali.

Ance Wali dan Marina anan ya girma a inda ya
nuna karamomi masu ban mamaki.

A ciki akwai
karamar karatun alkur'ani mai girma, inda ya
kasance yana shan Kan malaminsa tun kafin a
koya masa. Akwai kuma wata takaddama data
tashi a gari game da watan azumin Ramadana,
wasu suna cewa watan ya kare, sai aje a duba
watan Sallah, wasu kuwa na cewa bai kare ba
sai washegari.

To, da aka taru sai ba'aga wata ya tsaya ba. Sai
Wali dan Marina ya fere fasasshiyar kwarya, yayi
mata siffar wata, sannan ya jefa sama. Sai kuwa
ta tsaya, ya nunawa mutane yace ga wata san.

Sai kowa ya yarda wata ya tsaya.
To shikuma Wali Dan Masani sai ya musanta,
yace wannan ba wata bane. Sai Yayi addua, ya
mika hannu sama, sai gashi ya riko watan. Ya
nunawa mutane, suka kuma yadda. Wannan itace
takaddamar data shiga tsakanin waliyyai biyu,
suka nunawa mutane karama.

Wali Dan Marina yayi rubuce-rubuce na littattafai
da wakoki da dama. Misalin su shine:-

1. Wakar Daliyya wanda yayiwa Sarkin Berber
Aliyu

2. Wakar Nuniyya wadda ta kunshi bayanin
iliminsa

3. Wakar Toba mai baiti dubu

4. Kasidat Mazjarat al fiyan

5. Wakar yabon shehun Barno Mai Ali ibn Al Hajj
Umar

Da wasunsu

(An ciro ne daga Kasidar da furofesa Dalhatu
Muhammad ya taba rubutawa).

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: