Saturday 7 October 2017

Labari: MDD ta sa Saudiyya a sahun kasashe masu kisan yara

Tura Wannan Zuwa Ga

Majalisar Dinkin Duniya ta sanya Saudiyya a
jerin kasashen da za ta fitar wadanda ke kashe
yara a lokutan yaki, saboda rawar da take
takawa a gamayyar da take jagoranta wajen
yakin Yemen.

Sanarwar da MDD ta fitar ta ce ayyukan
gamayyar kasashen sun jawo mutuwar yara 638
a shekarar 2016, ta kuma zargi gamayyar da kai
hare-hare 38 kan makarantu da asibitoci.
Haka kuma MDD ta sanya dakarun gwamnatin
Yemen, wadanda gamayyar ke jagoranta da kuma
kungiyar Houthi a daftarin jerin wadanda suke
kashe yara lokutan yaki.
Sai dai gamayyar kawancen kasashen ta yi watsi
da batun cewa tana sane take kai hare-hare kan
fararen hula da kuma gine-gine.
An kashe fiye da mutum 8,530, wadanda kashi
60% daga cikinsu fararen hula ne, kuma hare-
haren sama sun jikkata mutum 48,800 tun daga
watan Maris din 2015, a cewar MDD.
Yakin na Yemen ya kuma bar mutum miliyan 20.7
cikin tsananin bukatar agajin gaggawa, al'amarin
da ya jawo tsananin bukatar abinci da ba a taba
ganin irin sa ba a duniya.
A ko wacce shekara, sakataren MDD na fitar da
rahoto kan yara da yake-yake wanda ke dauke da
jerin sunaye na wasu bangarori da ake zargi da
take hakki.
Daftarin rahoton na baya-bayan nan na cewa: "A
Yemen, ayyukan gamayyar kasashen da Saudiyya
ke jagoranta ya jawo kashe yara har 638, kuma
an samu wannan adadi ne bayan an tabbatar da
cewa ita ke da alhakin kai hare-hare 38 a
makarantu da asibitoci a shekarar 2016."

Su kuwa kungiyoyin Houthi da na al-Qaeda da
dakarun da ke goyon bayan gwamnati wannan ne
karo na biyu a jere da ake lissafa su a 'masu
wannan laifi.'
Haka kuma rahoton ya nuna karara cewa MDD ta
yi amanna gamayyar kasashen 'ta fara daukar
matakan da suka dace a lokacin da ake hada
daftarin rahoton don tabbatar da bai wa yara
kariya."
Wakilin Saudiyya na dindindin a MDD, Abdallah al-
Mouallimi, ya shaida wa kamfanin dillancin
labarai na Reuters cewa ba zai ce komai ba kan
rahoton har sai sakataren Majalisar António
Guterres, ya amince da shi a hukumance nan
gaba cikin wannan watan na Oktoba.
Sai dai a watan Agusta Saudiyya ta ce babu wani
tabbaci da zai sa a sanya gamayyar kasashen da
take jagoranta a jerin bangarorin da suke kisan
yara a lokutan yaki.
Shi ma mai magana da yawun MDD Stephane
Dujarric ya ki cewa komai kan daftarin rahoton.
Shugaban kungiyar Save The Children mai
fafutukar kwatowa yara hakkokinsu Helle
Thorning-Schmidt, ya ce, "Sakataren MDD ya yi
abin da ya dace don kwatowa yaran da suke
yankunan da ake yaki hakkokinsu.
"Hakan zai sa duk bangarorin da aka sanya a
wannan jeri da ma duk wani bangare da ke da
hannu a yakin Yemen shiga taitayinsu, da ma
kasashen da ke goyon bayansu da ba su
makamai."

A bara dai an cire gamayyar kasashen da
Saudiyya ke jagoranta daga jerin sunayen da aka
fitar na shekarar 2015, duk kuwa da korafin da
kungiyar Save The Children ta yi.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com
.
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: