Friday 6 October 2017

Siyasar Nigeria: Sabuwar Matemakiyar Gwamnan Babban Bankin Nigeria Tareda Takaitaccen Bayani akan Rayuwar Ta

Tura Wannan Zuwa Ga

- Tana da digiri har uku duk a harkar sarrafa
kudi

- Tana da aure da ’ya’ya biyu

- Ta rike manyan mukamai bankunan a Stanbic

IBTC da kuma Diamond Bank
Aisha Ahmad, ’yar shekara 40, hamshakiyar
ma’aikaciyar banki ce tun kusan shekaru 20. Ta
rike mukamai da dama a harkar banki wanda
suka hada da kula da hannayen jari, kula da
tattalin arziki, mai bada shawara a kan yadda ya
kamata a yi amfani da kudi, da sauran su.

An haifi Aisha a ranar 26 ga watan Oktoba, a
shekara ta 1977, a jihar Neja. Ta karanci
Accounting a digirinta na farko a jami’ar Abuja.

Sannan tayi digirin kwarewa (masters) a
Business Administration and Finance daga
jami’ar Legas.

Daga baya kuma ta kara sabon
digirin kwarewa a Finance & Management daga
jam’iar Cranfield dake Birtaniya.

Ta auri tsohon
brigediya-janar Abdallah Ahmad kuma suna da
’ya’ya biyu maza.

Kafin a bata mukamin maitamakiyar shugaban
babban bankin Najeriya (CBN), ita ce shugabar
bankin Diamond Bank Plc., kuma ita ce shugabar
majalisar mata shuwagabanni a ma’aikatu da
gwamnati (Women in Management, Business and
Public Service).

An kafa majalisar ne a 2001 don
hada kan mata shuwagabanni da kuma bunkasa
yadda zasu tafi da ma’aikatar da suke
shugabanta.

Aisha tayi aiki da NAL Bank Plc., Zenith Bank
Plc., da kuma Stanbic IBTC Bank kafin ta zama
shugaba a Stanbic din.

Tana cikin kungiyoyin
Chartered Financial Analyst, CFA, da Chartered
Alternative Investment Analyst, CIAI.

Aisha ta gaji kujerar, Sarah Alade, ce bayan da
tayi ritaya a watan Maris na bana.

Ita Sarah ita
ce mace ta farko data fara rike babban mukami
a babban bankin Najeriya.

An sanar da nada ta a wannan mukami daga
ofishin shugaban kasa a yau, kuma zata shiga
ofis din mataimakin gwamnan CBN da zarar
majalisar dattijai ta rantsar da ita.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: