Saturday 7 October 2017

Gargadi: Kar wanda ya kuskura yakuma cin Naman Biri Ciki harda Naman Dabbobin Daji

Tura Wannan Zuwa

Hukumomin lafiya a Najeriya sun gargadi
al'ummar kasar da su kiyayi cin naman biri da
sauran naman dabbobin daji, bayan da aka samu
barkewar annobar cutar kyandar biri a jihar
Bayelsa da ke kudancin kasar.

A kalla mutum 10 ne ma'aikatar lafiya ta kasar
ta tabbatar da cewa sun kamu da cutar, kuma
tuni a ka kebe su don gudun kada ta yadu.

A wata sanarwa da ya fitar, ministan lafiya na
kasar Isaac Adewole, ya ce ana bincike kan abin
da ya jawo cutar, wadda ake samun ta daga jikin
birrai da bera da kurege da kuma barewa.
Sai dai ministan ya ce, duk da cewa ba a san
takamaimai maganin cutar ba, al'amarin ba na
daga hankali ba ne sosai saboda cutar ba mai
tsanani ba ce.

Sai dai ya yi kira ga jama'a da su kiyaye bin
hanyoyin kamuwa da cutar, "kamar cin naman
biri da sauran naman daji su kuma kiyaye shiga
waje mai taron jama'a sosai."

Mista Adewole ya ce kwayar cutar na daga cikin
dangogin cututtuka kamar karanbau da bakon-
dauro.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daga cikin
mutum 10 da aka kebe akwai wani likita, kuma a
kalla mutum 49 ake nema don a kebe su
wadanda ake zaton sun kamu da cutar.

Ba a faye samun annobar cutar kyandar biri ba
amma kuma ba ta faye hallaka mutane ba.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com
.
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: