Wednesday 4 October 2017

Magana Jari Ce: SHARRIN MATA LABARIN KALALA DA KALALATU

Tura Wannan Zuwa Ga

Akwai wani mutum wai shi Kalala, yana da
matarsa wadda a ke kira Kalalatu. Kalala Allah
ya yi shi wani irin mutumin da ne, ba abin da ya
fi da ki illa a yi masa abinci ya ci shi kadai. Da
suna ci tare da wani makwabcinsa, sai
makwabcin ya zama wani iri ne mai mita. Ya kan
rika cewa Kalalatu ba ta iya miya ba, wai kullum
miyarta daga ta cika gishiri sai ta cika ruwa.

Da Kalala ya ga tsegumin ya faye yawa sai ya
bar kai abincinsa wurin makwabcin. Ya rika fita
karauka yana nemo baki, yana kawowa gidansa
suna ci tare.

To, Kalalatu ba ta kaunar wannan dabi’a ta
mijinta, domin bisa ga misali, ran da Kalala ya
yanka kaji biyu, iyaka Kalalatu ta sami cinya,
domin duk Kalala zai kai wurin bakin da ya jawo
ne su cinye. Ta yi, ta yi ta hana shi wannan
tabi’a, ya ki hanuwa. Saboda haka sau da yawa
in ya ba ta dahuwa sai ta tsame rabi ta cinye, in
Kalala ya yi magana ta ce ya kone ne, ko kuwa
ta ce ta sauke ta shiga daki dauko kwano, kafin
ta fito ta tarar kyanwa ta cinye rabi.

Dalilai dai
irin wadannan marasa kan gado ga su nan kullum
Kalala na ta sha, amma saboda hakurin da Allah
ya zuba masa ba ya cewa kome.
Ran nan, ko ina Kalala ya sami kudi sai ya tafi
kasuwa ya nemo dakwalen kaji guda biyu ya
sawo. Ya yiwo cefane ya kawo gida, ya ce wa
Kalalatu ta soye kajin nan gaba daya. Ta tashi,
bayan ya fige ya gyara mata, ta sa tukunya ta
shiga suya. Abu ga dakwalen kaji, duk kitse ya
cika tukunya, sai wani abu su ke coi, coi, coi, in
tana juya su. Duk kuwa kwadayi ya kama ta, da
ma ga ta idonta idon nama sai ka ce kura sai
yawu ke zuba dalala. Ta sa dan yatsa ta
dandana ta ji ko gishiri ya yi daidai, sai ta ji abin
dadi ya kamo ta har ga keya, ta ce, “Kai,
wadannan kaji yau suna shirin ganin wata irin
gajerar suya. Amma dubi duk yawan kajin nan,
rabona bai fi cinya ba daga cikinsu. Ka san dai
halin mai gidan nan ya miskile ni.”

Ta ci gaba da suya kanshi na jifarta, ta yi kamar
ta jure ta kasa, sai ta fara tsame tana ci, wai ta
kau da mugun yawu. Kafin su soyu ta kusa cinye
rabin kaza. Da ta sauke sai ta je ta gaya wa
mijin sun soyu.

Kalala ya ce, “To, sai ki cire cinya guda, taki ke
nan. Saura kuwa a ajiye, har in je in samo
abokan ci.”

Kalalatu ta ce, “To.” Ta tafi ta cinye yar cinyar
da aka ce ita ce tata, ta tsuguna tana kallon
saura, sai mai ke zuba nash, nash.

Ta ruga wajen
kofar zaure ta leka ko ta hango mijin tafe da
bakin, ba ta ga kowa ba. Sai ta komo wajen kaji
ta kura musu ido. Sai ta ce, "Af, ashe ma fika
fikai guda biyu sun kone tun dazun, bari ma in
cinye na dayar don su zo daidai, kada mai gida
ya gane." Sai ta fiffizge ta lakwame. Ta sake
rugawa bakin zaure ta gani ko mijin na tafe, ba
ta ga kowa ba. Ta dawo ta tsaya bisa kwanon
kaji ta ce, “Shin mai gidan nan zai zo dai? Ga
kaji har sun fara yin sanyi. To, ni Kalalatu, yanzu
in ya zo ya tarar wannan kazar duk na fiffige ta,
ya tambaye ni in ce me? Ba abin da ya fi sai in
cinye ta gaba daya, in ya zo in ce kyanwar gidan
nan ta sace ta." Sai ta tsuguna ta cinye ta sarai,
ta kwashi kasusuwa ta kai masai ta zuba.

Ta koma kofar zaure ta hanga, ba ta ga mai gida
ba. Da ta ga haka sai ta dawo, ta ce, “A bari ya
huce shi ya kawo rabon wani. Bari in karkare
cinye guda, kowa ya huta, in ya so in ya dawo
kome ta tafasa ta kone.” Sai ta kama kazar guda
kuma ta lakume. Ta nufi randa ta debi ruwa ta
kora, ta yi gyatsa, ta ce, “Madalla, kome ta ke
zama ta zama.”

Ta zauna ke nan, sai ga mai gida ya shigo. Ya ce
wa Kalalatu, “Yi maza ki nika yaji ki barbada
musu, kin san yanzu lokacin sanyi ne, ba abin da
ya fi yaji amfani. Na manta ne in gaya miki ki
nika yaji dazun. Yi hakuri, yau dai kin sha aiki.”
Kalalatu ta ce, ‘‘Ai ba kome, ku dakata mini dai
kadan.” Ta shiga daki tana ta shawarwarin abin
da za ta ce wa mijin ya faru ga kaji. Tana can
cikin daki, sai Kalala ya dauki wuka ya nufi
manika yana wasawa kararas, kararas, wai don ta
yi kaifi ya sami ta yanka kaji kanana kanana, in
an kawo.

Kalala na can na ta fama da washin wuka, sai
Kalalatu ta ji ana sallama. Ta yi farat ta fita
bakin zaure wajen mai sallama, ta dube shi ta
rike baki, ta ce, “Kai bako, kai ne mai gidan nan
ya kirawo wai ku zo ku ci abinci?”
Bako yace, “I, Allah ya saka muku da alheri.”
Kalalatu ta ce, “Kai, tafi can, sakarai, ba ka san
abin da a ke ciki ba. Kana tsammanin mutum
mai hankali ya sa a yi masa abinci ya fita
karauka neman abokin ci? In kana kama gabanka
ka ruga, tun da wuri ka ruga. Ka ji shi can yana
washin wuka, kunnenka guda zai yanke. Kullum
haka ya ke yi, motsattse ne.”

Bakon nan, ko da ya saurara ya ji Kalala na
washin wuka sai ya dafe keya ya zura a guje.
Kalalatu kuma ta ruga wajen Kalala, ta ce, “Ga
irin jaye-jayen naka nan, ba ka san irin mutanen
da ka ke jawowagida ba.
Kalala ya ce, “E? Mahaukaci ne?”
Kalalatu ta ce, “Mahaukaci mana, ko ba
mahaukaci ba ne ai barawo ne, da barawo ko da
mahaukaci ai duk tafiyarsu ke nan. Kajin da na
barkada wa yaji, ko da ya gan su sai na ga ya yi
wuf ya fizge, ya shafa a guje da su. Ga shi can
ya mika, ya tasar wa kasuwa."

Kalala ya fusata, ya ce, “Allah wadan dan banza!
Mutanen duniya ba wanda ke iya musu. Da ma
ya bar mini ko da guda daya, ai da na sami ta
kalaci. Dakwalen kajin nan duk ya cinye shi
kadai? Bari in leka ko na hango shi, mu raba.”
Sai ya ruga wajen zaure ya hanga, sai ga bakon
nan can ya tattake da gudu kaca kaca kaca yana
korar iska. Kalala ya ce, “Kai abokina! Kai tsaya,
don Allah ko guda daya ka ba ni! Wallahi su ke
nan, mai dakina ko lasawa ba ta yi ba, ka
dauke.” Bako ya yi kamar bai ji ba.
Kalalatu ta ce wa mijin, “Bi shi mana, a guje dai
na san ba ya tsere maka. Duk wahalan nan da na
sha ta zama a banza, ko lasawa ban yi ba, ai ka
san ka dauki alhakina.”

Sai Kalala ya runtuma a guje da wukarsa a
hannu, ya bi bako yana kira, “Tsaya don Allah,
daya kadai na ke so, na bar maka daya!”
Bako tsammani ya ke Kalala na nufin kunnensa
daya kadai ya ke so ya yanka. Ya waiwaya sai
ya ga ya taso masa da wuka tsirara a hannu.
Saboda haka ya kara mai, ya dai yi wa Kalala
fintinkau yana ji yana gani.

Da Kalala ya ga abin ba girma, sai ya juyo ya
nufo gida da wukarsa a hannu, yana kutawa, yana
Allah ya isa. Da matar ta gan shi ya dawo yana
zage zage sai ta tarye shi, ta ce, “Ya ba ka? Ka
ga irin abin da na ke gaya maka nan tuni."

Kalala ya ce, “Ko tarad da shi na yi? Wannan
akwai dan banza da gudu! Ga shi kamar tsoho,
amma daya zura sai ganinsa a ke kamar ba ya
taka kasa. Bar shi ya je ya ci, ban dai yarda
masa ba duniya da lahira. Allah ya isa. Daga yau
ko sai yau, ba na sake kiran dan kowa ya ci
abincina, tun da duniya ta sake. Mts, Allah
wadai! Talaka dai ba aboki ne ba, ko ka so shi,
ran biki kwa Bata.”

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Waziri Aku

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: