Wednesday 4 October 2017

TUNA BAYA: NIGERIA INJI MARIGAYI SA'ADU ZUNGUR KARANTA WAKAR KA YANKE WA BAHAUSHE HUKUNCI

Tura Wannan Zuwa Ga
MAGANAR SHI TA TABBATA BAYAN SHEKARA
50
DATTIJO MARAR KWADAYI ALLAH GAFARTA
MASA.




Marubuci: Lawal Ali Reseacher

"Matukar a arewa da karuwai,
yan daudu dasu da magajiya.

Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.

Matukar yayan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.

Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.

Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai tanyonsu da dukiya.

Babu shakka yan kudu zasu hau,
Dokin mulkin Nijeriya.

In ko yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai sha wuya.

A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.

Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen,
Malaman karya yan damfara.

Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.

Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.

Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.

Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.

Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.

Wagga al'umma mai zata yo,
A cikin zarafofin duniya.

Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
Zaya sha kunya nan duniya ".

"Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko kuyi dariya.

Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.

Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.

Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya".

Marigayi Sa'adu Zungur a cikin waken sa
mai suna

"Arewa Jamhuriya ko Mulukiya"

MAGANAR SHI TA TABBATA BAYAN SHEKARA
50
DATTIJO MARAR KWADAYI ALLAH GAFARTA
MASA.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode




TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user