Thursday 26 October 2017

Na Tuba Bazan sake Aikata irin abinda na Aikata ba-Rahama Sadau

Tura Wannan Zuwa Ga

Shahararriyar jarumar fina-finan Kannywood,
Rahama Sadau, ta fito fili ta nemi gafarar duk
wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar
da ta yi a wani bidiyon waka tana "rungumar"
wani mawaki.

Wannan batu ne ya jawo kungiyar masu shirya
fina-finai ta kasa reshen jihar Kano, MOPPAN, ta
koreta daga masana'antar a watan Oktoban bara.

A wata wasikar da ta aike wa MOPPAN, wacce
BBC Hausa ta samu kwafi, Rahama ta nemi
afuwa kan abin da ta yi, tana mai cewa "kuskure
ne," kuma za ta "kiyaye gaba".

Jarumar, wacce korar tata ta sa ta koma fitowa
a fina-finan Nollywood , ta kuma tabbatarwa da
Nasidi Adamu Yahaya cewa hakika ta nefmi
gafara" kan rungumar mawaki Classiq da ta yi.

Sai dai wannan wasika da Rahama ta rubuta
tamkar ta yi amai ta lashe ne, saboda ko a
watan Yulin da ya gabata ta shaida wa BBC
cewa babu wanda ya dakatar da ita daga
Kannywood.

Shugaban MOPPAN Kabiru Maikaba ya shaida
wa BBC cewa kungiyar za ta sanar da matsayin
da ta dauka a kan afuwar da jarumar ta nema
bayan sun tattauna a hukumance.

Amma ya ce kungiyar za ta yi kokarin kwatanta
adalci ga Rahama kan duk wani mataki da za su
dauka.

Abin da wasikar ta kunsa

Ta rubuta cewa: "An kai shekara daya kenan tun
faruwar wannan lamari, na yi iyakar kokarina don
na nutsu sosai ta yadda ba za a bai wa
kalamaina wata ma'ana ta daban ba kamar
yadda kafofin yada labarai da wasu mutane suka
dinga yi a baya."

"Ni 'yar adam ce wacce ba ta kubuta daga aikata
kuskure ba, kuma ni 'ya ce wadda za a iya yi wa
gyara, ina rokon abokan aikina, da mambobin
kungiyar masu shirya fina-finai, da dukkan
al'ummar arewacin Najeriya da ma dukkan masu
kallo da su gafarce ni," in ji Rahama.

Kazalika, jarumar ta yi magana a wasu gidajen
rediyo na jihar Kano, inda ta jaddada neman
gafarar musamman ga Sarkin Kano Muhammadu
Sunusi II da kuma gwamnan jihar Dr Abdullahi
Umar Ganduje.

A karshen wasikar dai Rahama ta yi alkawarin
bin dokokin da kungiyar ta shimfida.

Karanta wasikar neman gafarar da Rahama
Sadau ta rubuta

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: