Thursday 26 October 2017

Internet: Daga Yau duk wanda yayi ba dai-dai ba Za'a Hukunta Shi

Tura Wannan Zuwa

An yi ta watsa sanarwar gwamnati a shafukan
sada zumunta jim kadan bayan da shugaba
Robert Mugabe ya sanar da kafa wata ma'aikata
da za ta maida hankali wajen samar da tsaro a
harkar Internet.

Al'ummar Zimbabwe dai sun yi ta raha kan
wasikar wacce ke dauke da sa hannu da kuma
adireshi na boge na sabon ofishin ministan samar
da tsaro a harkar Internet, Mr Patrick Chinamasa
wanda ke umurtar duk masu amfani da WhatsApp
a matsayin dandali da su yi rijista a ma'aikatar
nan da watan Nuwamba.

Sai dai yanzu an rage yawan raha da ake yi kuma
'yan kasar Zimbabwe sun maida hankali wajen
nazarin tasirin sabuwar ma'aikatar musamman
kan batun da ya shafi 'yancin fadin albarkacin
baki.

'Barazana ga Kasa'

Gwamnatin Zimbabwe dai na dari-dari da yadda
ake amfani da shafukan sada zumunta tun bayan
da a shekarar data gabata, wani Fasto Evan
Mawararire ya jagoranci wani gangami da aka
rika amfani da maudu'in #ThisFlag movement.

Ta hanyar shafukan sada zumunta na Twitter da
Facebook an shirya gangami na zama a gida,
gangamin da shi ne mafi girma na kin jinin
gwamnati da aka taba shirya wa a 'yan shekarun
nan.

Kakakin shugaban kasar Mr George Charamba,
ya ce shugaba Mugabe ya yanke shawarar kafa
ma'aikatar ce don shawo kan sabuwar barazanar
da kasa ke fuskanta wanda ya ce ''ana tsara wa
da kuma daukar nauyi don aikata ayyukan da ba
su kamata ba".

Da alamu dai shafukan sada zumunta su ne
hanyoyin farko da al'ummar Zimbabwe ke amfani
wajen mu'amala tare da samun labarai.

Wannan hanya dai ta na cigaba da bunkasa duk
kuwa da dokokin takaita fadin albarkacin baki.

A cikin shekaru 16 da suka gabata, amfani da
Internet a kasar ya karu daga kashi 0.3% zuwa
kashi 46%, kamar yadda kididdiga daga hukumar
sadarwa ta nuna.

Gidajen talbijin da kuma jaridu na Internet har da
wadanda suke aiki daga wasu kasashen waje na
amfani da Internet don watsa labarai da
gwamnati ba ta da iko akai.

A lokacin da gidajen sayar da man fetur suka
rasa mai a watan daya gabata, an yi ta ganin
dogayen layukan a manyan shagunan Zimbabwe
inda 'yan kasar ke rige-rigen sayen abinci don
kaucewa karancin sa.

Gwamnati dai ta yi zargin cewa an yi amfani da
shafukan sada zumunta wajen yada sakonnin
karya da suka firgita jama'a.

'Kokarin hana fadin ra'ayi'

Sai dai wasu na ganin cewa matsayin gwamnati
kan wannan batu tamkar barazana ce ga 'yancin
fadin albarkacin baki da kuma walwala.

Wata kungiya kan yancin sadarwa a Zimbabwe ta
reshen cibiyar yan jaridu a ynkin kudancin Afrika
a wata sanarwa, ta ce wannan sabon bincike kan
kafafen sada zumunta ya sabawa kundin tsarin
mulki da kuma yancin fadin albarkacin baki.

Sanarwar ta kara da cewa, ''abun takaici
barazanar da ake yi ta janyo mutane na takaita
yadda suka tattauna al'amurran da suka shafi
kasa."

Kungiyar ta kuma suko takunkumi da ake sanya
wa kafafen yada labarai a Zimbabwe saboda
kawai suna ba jama'a damar fadin ra'ayin su a
shafukan Internet kan rahotanni da kafafen suka
gabatar.

A nata bangaren, gamayyar jam'iyyun adawa a
Zimbabwe, Movement for Democratic Change
(MDC) ta ce sabuwar ma'aikatar tsaro a harkar
Internet da gwmanati ta kafa, wata hanya ce ta
rika yi wa jama'a leken asiri.

Jagoran gamayyar jam'iyyun adawar Morgan
Tsvangirai ya yi amannar cewa an kafa
ma'aikatar ce don takaita 'yancin fadin
albarkacin baki yayin zabubbukan 2018.

Ya ce "Shugaba Mugabe... zai yi duk abun da zai
iya yi don dakile shafukan sada zumunta saboda
ya hana tasirin korafin da jama'a ke yi kan
gwamnatin sa,".

"Koda yake a cewar sa, babu yadda gwamnati
zata yi don dakile shafukan sada zumunta."
Za'a tsare mutane nan gaba?

Yayin da wa su kasashen duniya da dama su ke
da hukumomi wadanda ke yaki da masu aikata
laifuffuka ta shafin Internet, Zimbabwe ce kasa
ta farko a duniya da ta kafa ma'aikata sukutum
da guda don kula da hakan.

A yanzu dai ana cigaba da yada sakonni na
gargadi a shafukan sada zumunta.
Misalin irin wadannan sakonni shi ne daga wani
mutum mai suna "Mr Chaipa", wanda ya bukaci
'yan Zimbabwe da suka rika yada labaran da za
su iya kare kansu a gaban kotun ne kadai a
shakukan sada zumunta.

Mr Chaipa ya ce yana da sauki gwamnati ta sa
ido kan sakonni da ake watsawa inda ya lissafa
jerin ayyuka ta Internet da za'a iya dangantawa a
matsayin manyan laifuffuka.

''Nan da wa su watanni ma su zuwa za'a kame
mutane da dama don su zama abun misali da za
su sa mutane suk guji wuce makadi da rawa a
lokacin da su ke amfani da shafukan sada
zumunta gabannin zabe," in ji shi. "

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: