Thursday 26 October 2017

Kasashen Waje: Zan kakkabe tsattsauran ra'ayin addini a Saudiyya - Yarima

Tura Wannan Zuwa

Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya,
Mohammed bin Salman, ya ce dawo da
sassaukan ra'ayin addinin musulunci na daga
cikin shirye-shiryensa na zamanantar da kasar.

Ya shaida wa manema labarai cewa kashi 70
cikin 100 na al'ummar kasar 'yan kasa da
shekara 30 ne, kuma sun fi son rayuwa irin
wacce "addinin musulunci ya bayyana yadda za a
zauna da juna lafiya".

Yariman ya sha alwashin kakkabe duk wani abu
da ke da alaka da tsattsauran ra'ayin addinin
musulunci nan ba da jimawa ba.
Sai dai Yariman bai yi wani karin bayani kan abin
da yake nufi da 'tsattsauran ra'ayin addinin
musuluncin' da ya ke son kawar wa ba.

Wadannan kalaman nasa ka iya bude sabon babi
a muhawar da ake yi na irin salon da kasar ke
son dauka a nan gaba.

Ya yi wadannan kalamai ne bayan da ya sanar da
zuba jarin dala biliyan 500 don gina wani sabon
birni a kasar.

Birnin mai suna NEOM zai kasance ne a yankin
arewa maso yammacin gabar kogin maliya, kusa
da iyakar Masar da kuma ta Jordan. Girman
wajen kuma zai kai mita 26,500.

A Saudiyya dai yana daga cikin dokar kasar a
tabbatar da cewa mutane sun yi shiga ta kamala
kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

A shekarar da ta gabata ne Yarima Mohammed
ya kaddamar da wani faffadan shiri na samar da
sauye-sauye a zamantakewa da tattalin arziki a
kasar wanda aka yi wa lakabi da "Vision 2030".

A bangaren wadannan shirye-shirye dai, yariman
mai shekara 32 ya gabatar da bukatar sayar da
wani bangare na kamfanin man fetur na kasar,
Saudi Aramco, da kuma kirkirar asusun ajiyar
rarar kudi na kasa saboda bacin rana mafi girma
a duniya.

A watan Satumba ne kuma mahaifinsa Sarki
Salman, ya sanar da janye dokar da ta haramta
wa mata tukin mota daga shekara mai zuwa, duk
kuwa da kin goyon bayan hakan da wasu
malaman kasar suka yi.

Gwamnatin tana kuma son zuba jari a bangaren
shakatawa.

A yanzu haka ana sa ran nan ba da jimawa ba za
a sake bude gidajen rawa da gidajen kallo na
sinima a kasar.

Yarima Mohammed ya kare wadannan sauye-
sauye a wani taron tattalin arziki da aka yi a
Riyadh ranar Talata, wanda aka yi da masu zuba
jari da manyan mutane.

"Muna dab da komawa yadda muke a baya -
kasar da ke bin matsakaicin ra'ayin addinin
musulunci mai kyawun mu'amala da ko wanne
addini, da al'adu da mutane a duk fadin duniya,"
a cewarsa.

Ya kara da cewa: "Muna son mu yi rayuwa kamar
kowa.

Rayuwa wacce addininmu ya bayar da
damar yin kyakkyawar mu'amala da kowa."

"Kashi 70 cikin 100 na al'ummar Saudiyya 'yan
kasa da shekara 30 ne, kuma maganar gaskiya
ba za mu bata shekara 30 masu zuwa wajen
fama da akidun da za su rusa mu ba. Za mu
ruguza su a yau kawai."

Yariman ya kuma jadda cewa Saudiyya ba haka
take ba a shekarar 1979, lokacin da aka yi juyin-
juya hali na musulunci a Iran, kuma mayakan sa
kai suka mamaye Masallacin Harami na Makka.

Bayan wannan lokaci ne aka haramta duk wani
abu da ya danganci nishadi a Saudiyya, kuma aka
bai wa malamai damar kula da abubuwa kan
rayuwar al'umma.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: