Thursday 12 October 2017

Sauyin Rayuwa: TARIHIN TSOHON BIRNIN GANGARA DA YADDA GARIN MALUMFASHI YA FITO DAGA GARESHI

Tura Wannan Zuwa

Kirarin Garin: Gangara Ta Naturɓe, idan kaji ina
kwana bako ne.. Sai dai Nyalli Jam.

Wannan gari tsoho ne, jimawarsa kuma har takai
wasu na ganin ya girmewa tsoffin birane misalin
Malumfashi, Getso, Baɗari da birnin Kano.

Fulani kabilar Natirawa ne akace suka kafa garin
lokaci mai tsawo daya shuɗe, sannan labari na
gaskiya ya dusashe dangane da tsohon birnin, ko
kuma lokacin kafuwarsa, wanda a yanzu ya zama
kufai, amma dai zuwa yanzu an iya gane sashen
ganuwar tsohon birnin. Haka kuma marinar garin
da tsoffin kukoki nanan a inda tsohuwar rayuwar
Natirawan ta auku shekaru ɗaruruwa da suka
gabata.

Babban limamin Garin mai suna Mallam Adamu,
ya bayyana mana cewar an samo sunan garin
'Gangara' ne daga kalmar 'Gagara', ko kuma ace
garin daya Gagara acishi da yaki, domin tunda
wannan birni yake babu wani sarki daya taɓa
cinsa da yaki.

An samu cewa garin Gangara na usuli shahararre
ne, mai zagaye da ganuwa, mai ɗauke da tarin
mutane kuma.

Mutane na zuwa fatauci daga
sassa daban daban na kasar hausa. Har ma ance
akwai zamanin da saida gidaje suka cika birnin,
har ma wasun suka rinka yin gidaje a bayan
ganuwa.

Sannan kasancewar garin na fulani ne, akwai
tsohuwar al'adar nan ta sharo da kuma wankan
amarya da aka ruwaito tana wakana tsakankanin
mazauna birnin, amma dai ance musulunci ya
samu karɓuwa tun kafin zuwan Mujaddadi
Usmanu ɗan fodio, don haka abubuwa irin na
maguzanci basu yawaitaba.

A batun yake-yake, garin Gangara yayi zarra,
tunda ance akwai wani K'aton kada mai suna
'Nabogaji' wanda yake cikin wani tafki dake kusa
da garin, wanda kuma yake rura kuka yayin da
wani bala'i ya tunkaro garin domin sanar da
mazauna birnin suyi shiri.

Dukkan maruwaitan tarihin garin Gangara sun
haɗu akan cewa babu wanda ya taɓa cinye garin
da yaki.

Wasu sunce da zarar Nabogaji yayi ruri,
sai idanuwan mahara ya rufe, ya zamo basa iya
ganin birnin da abinda ke cikinsa.

Yayinda wasu
ke ganin tsabar jarumtar sadaukan birnin ke basu
ikon mayar da keyar mahara baya.
Ance Gangara ta taɓa kaiwa garin Getso hari,
taci nasara akan garin, har saida ta kori maza da
mata dake garin.

Haka kuma gangara tayi yaki da garuruwan
matazu, kurkujan na musawa, da malumfashi a
baya-bayan nan, kuma duk ta samu nasara.

Liman Mallam Adamu ya faɗa mana cewar
asalin garin malumfashi Gangara ne. Domin kuwa
zamani mai tsawo daya wuce, an taɓa yin wata
annoba ta ciwon ciki wadda mutanen birnin
Gangara suka rinka mutuwa.

Don haka sai mutanen suka tashi izuwa gefensa
suka kafa sabon gari, yayinda waɗansu suka
fantsama sassan duniya.

To ance daga irin waɗannan mutanen ne wani
banatire mai suna Dano (ko Dunu ) ya riski garin
malumfashi a lokacin yana jeji. Sai ya sauka
sannan ya sari gona domin yaɗan taɓa noma.

Da amfanin gona yazo, sai ya zamana ya samu
alheri, don haka ya shiga godiya ga mai sama
yana faɗin "Yanzu Na-numfasa"

Daga nan kuma sai labari ya iso garinsu
Gangara, inda mutane suka rinka tafiya inda yake
da zummar suje suyi noma su samu riba da
kuɓuta daga waccan annoba. Don haka sai suma
suka rinka cewa "zamu tafi inda Dano yake
Munumfasa" watau mu huta daga wannan
annobar. Daga baya aka maida sunan garin ya
koma 'mulumfashi' ko 'Malumfashi'.

A cewar Liman, babbar hujja akan haka shine
unguwar Gangarawa dake garin malumfashi.
Wadda babu wata tsohuwar unguwa data girme
mata.

Sunan sarautar garin Gangara shune 'ɗan-saka',
ance ta samu ne daga wani sarkinta mai sakawa
duk waɓda aka yiwa zalunci daga talakawansa.
Hak kuma kasancewar sunayen tsoffin
sarakunanta sun ɓata, amma dai an samu cewar
a baya bayan nan sarakuna irinsu:-

Dan saka Atiku, Dan saka Babba, Dan saka Nani,
Dan saka Isiye, Dan saka Bello zarɓe magajin
tunkuɗa, ɗan saka sarki ya-musa, ɗan saka
yuguda, da ɗan saka muhammadu magajin daɗi
duk sun mulketa, sai kuma dagacin dake mulkinta
ayau mai suna Magaji Alh Bala ɗan muhammadi
majidaɗi.

Koda yake, ance yanzu sarautar ɗansaka ta
koma garin Gora bisa tashin tsohom ɗan saka
Muhammadu majidaɗi daga Gangara zuwa garin
na Gora saboda tsangwamar natirawa, don haka
da aka turo ɗansa sai ake masa lakabi da
Magaji.

Saboda hak yanzu sunan sarautar garin
'Magaji'.

Sannan kuma har gobe mutanen garin Gangara
suna fahari da cewar Mujaddadi Shehu Usmanu
ya sauka a garin akan hanyarsa ta zuwa kano
daga sokoto, harma ya sahale aka soma sallar
juma'a a garin, a lokacin da duk yamma da kano
daga Rimin Gado, sai malumfashi ake zuwa yin
sallar jumu'a...

Zuwa yanzu dai, garin yana nan a kusa da garin
Dayi, kuma yana karkashin karamar hukumar
malumfashi ne ta jihar katsinan Nigeria.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: