Monday 2 October 2017

Shin ko kasan Abubuwa 10 masu muhimmanci daga jawabin Buhari a sakon bikin murnar ‘yancin kai

Tura Wannan Zuwa

Wasu daga cikin abubuwa masu muhimmanci a
jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari a
sakon murnar ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya a yau
Lahadi, 1 ga watan Oktober.

1. Ranar 1 ga watan Oktoba ta kasance kwanan
wata na musamman ga dukan 'yan Najeriya

2. A cikin shekaru da dama kasar ta shiga cikin
wani halin kakani kayi da kuma matsaloli, amma
kowane ranar 1 ga watan Oktoba wata rana ne
na biki a kasar

3. Ranar 1 ga watan Oktoba na kowane shekara
ranar ce ta tunawa a Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

4. Dole ne a daidaita arzikin kasar don kada mu
dogara ga man fetur kadai

5. Dole ne mu yaki cin hanci da rashawa wanda
yake shi ne na farkon makiya ga Najeriya

6. Kira na kwanan nan game da sake tsarin
mulkin Najeriya, wanda ya dace, amma kungiyoyi
a wasu yankunan kasar na amfani da wannan
dama wajen neman raba kasar. Ba za mu
amince da haka ba kuma ba za mu bari irin
wannan ya ci gaba ba

7. A matsayin matashi na soja, da ni aka fara
yakin basasa daga farko har zuwa ƙarshen ta
wanda ta yi sanadiyar mutuwa kimani mutane
miliyan 2.

8. Wadanda ke neman haddasa sabuwar yaki
yanzu, ba a haife su ba ne a 1967, kuma ba su
da masaniya game da mummunar tashin hankalin
da kasar ta fuskanta.

9. Gwamnati na iya kokarin ta kowane lokaci
domin tabbatar da saki sauran 'yan matan Chibok
da suke hannun ‘yan Boko Haram

10. Tare da yawan ruwan sama a bara da
wannan shekara, aikin noma a kasar ta samu
taimakon Allah

NAIJ.com ta tattaro cewa, shugaba Muhammadu
Buhari ya bayyana cewa yayin da aka shiga rabi
na wa’adin gwamnatinsa, za a hanzarta ci gaba
da kuma magance matsalolin da kasar ke ciki.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Abdulazez Abdul

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: