Monday 2 October 2017

Shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafra, Nnamdi Kanu, na neman sulhu da shugaba Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga

Lauyoyin Kanu sun bayyana cewar a shirye
suke domin jagorantar tattaunawa tsakanin
gwamnatin Najeriya da Nnamdi Kanu

- Lauyoyin sun nisanta Kanu da kungiyar
tsagerun Neja-Delta

Daga karshe dai shugaban kungiyar masu
fafutukar kafa kasar Biyafra, Nnamdi Kanu,
wanda ake zargin ya tsere, na neman sulhu da
shugaba Buhari. Kanu ya bayyana haka ne ta
bakin lauyoyinsa, Ifeanyi Ejiofor, da Ameobi
Nzelu.

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, yayi
hasashen cewar ya tsere zuwa kasar Ingila
bayan ya sulale zuwa Malaysia bayan ya bayyana
cewar Kanu, da goyon bayan wasu mutane, yayi
kokarin tursasa shugaba Buhari hakura da yankin
kudu maso gabas domin su kafa kasar Biyafra.

Bayan gwamnati ta bayyana aniyarta ta sakin
mayakan kungiyar ta IPOB ne, lauyoyin Kanu sun
bayyana cewar a shirye suke domin jagorantar
tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da
Nnamdi Kanu domin a cewar su matsalar na
bukatar tattaunawa.

A karshe lauyoyin sun nisanta Kanu da kungiyar
tsagerun Neja-Delta bayan 'yan kungiyar sun ce
suna tattaunawa da gwamnati a madadin Kanu.
Lauyoyin sun ce Kanu bashi da wata alaka da
kungiyar.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Muhammad Mubarak Bala

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: