Monday 2 October 2017

Nayi Alkawarin Samar da aikin yi ga Matasa 10,000 a kowacce Jiha-Buhari

Tura Wannan Zuwa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai
samar da ayyukan yi ga matasa marasa aiki
kimanin 10,000 a kowace jiha da ke kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a
jawabinsa na ranar bikin cika shekara 57 da
samun 'yancin kasar.
Najeriya ta samu 'yancin kai ne daga hannun
Turawan Birtaniya a shekarar 1960.
Ya ce zai yi hakan ne ta hanyar wani sabon shiri
da Babban Bankin Kasar (CBN) zai bullo da shi.

Sai dai shugaban bai fadi tsawon lokacin da yake
fatan cika alkawarin samar da ayyukan ba.

Har ila yau, shugaban ya ce ba zai taba
amincewa da kiraye-kirayen da wadansu 'yan
kasar suke yi na ballewa ba.

"A lokacin da nake matashin soja, na ba da
gudummuwata tun daga farko har karshen yakin
(Basasar Najeriya) wanda ya yi sanadiyyar
mutuwar mutum kimanin miliyan biyu, ya kuma
haddasa asara da barna mai yawa," in ji Shugaba
Buhari.

Ya ci gaba da cewa wadanda suke kiraye-kirayen
maimaita hakan (a yanzu), "ba a haife su ba
lokacin yakin don haka ba su da masaniya game
munanan abubuwan da yakin ya jawo wa
al'umma."

Hakazalika ya bayyana rashin jin dadinsa kan
yadda wadansu jagorori a yankin da ke son
ballewa "ba sa jan kunne matasan da suke ci
gaba da ke son a raba Najeriya."
Daga nan shugaban ya ce sulhu shi ne mafita
kan duk wani al'amari.

Sai dai ya bukaci "duk wanda yake da wani korafi
game da kasar da ya gabatar da shi ga majalisar
dokoki ta kasar da kuma majalisun dokoki na
jihohi."

Shugaban ya yi hannunka mai sanda ga masu
neman ballewar, inda ya ce ba mutum ya kai
kokensa ga wadansu kungiyoyi "marasa kan gado
ba."

Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da
tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Neja-
Delta don samun dawwamanman zaman lafiya a
yankin.

"Muna da niyyar magance sahihan matsalolin
al'ummomin yankin," in ji shi.
Kan batun tsaro
Shugaban ya yaba da wa dakarun kasar kan
galabar da suke samu a kan mayakan Boko
Haram.

"Dole mu gode wa zakakuran sojojinmu kan
yadda suka fatattaki 'yan Boko Haram, suka
samu nasara a kansu, kuma aka rage yawan
hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba,
ba su gani ba."

Daga nan ya ci gaba da cewa "ba za mu yi kasa
a gwiwa ba," inda ya ce an fara fadada aikin
rundunar Lafiya Dole da take aiki a yankin arewa-
maso- gabashin kasar.

Har ila yau ya gode wa makwabtan kasashe da
sauran kasashen duniya game da taimakon da
suke ba "kasar a fagen yaki da ta'addanci."

Hakazalika ya ce gwamnatinsa tana "aiki ba dare,
ba rana" wajen ganin an 'yanto sauran 'yan
matan Chibok da sauran mutanen da ke hannun
'yan Boko Haram.

"Gwamnati za ta taimakawa dakarun kasar nan
ba kawai a yaki da ta'addanci ba, amma har da
matsalolin satar mutane don neman kudin fansa
da fashi da makami da kuma rikicin makiyaya da
manona," a cewarsa.

Tattalin Arziki

Shugaban ya bayyana shirye-shiryen da
gwamnatinsa take yi wajen ganin kasar ta rage
dogaro kacokan kan man fetur.
Hakazalika ya bayyana irin taimakon da
gwamnatinsa take bayarwa a fannin aiki gona.
Daga nan ya tabo batun matsalar wutar lantarki,
inda ya ce kasar tana da burin samar da Mega
Watt 10,000 nan da shekarar 2020 daga adadin
7,001 da ake samarwa yanzu.
Shugaban ya ce wata bakwai ke nan a jere da
hauhawan farashin kayayyaki yake ci gaba da
raguwa a kasar.

Ya kuma tabo batun yadda darajar kudin kasar
wato Naira take farfadowa idan aka kwatantata
da dalar Amurka.

Sai batun yadda kasar take fitowa daga matsin
tattalin arziki.

Cin hanci

Shugaban ya ce a shirye yake ya ga bayan
matsalar cin hanci da kabar rashawa, kamar dai
yadda ya saba shan alwashin yin hakan a baya.

Daga nan ya zayyana shirye-shireyen
gwamnatinsa wajen magance matsalar.
Har ila yau shugaban ya yaba wa majalisar
dokoki ta kasar game da ayyukan kwamitocinsu
na sanya ido.

Ya kuma bukace su da su yi dokokin magance
cin hanci.

A karshe ya bukaci daukacin 'yan kasar da su
"yaki cin hanci ta hanyar kin ba da shi, da kuma
karbarsa."

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: