Friday 29 December 2017

Kalli Yadda Dan Shugaba Buhari ya karye a sanadiyyar hatsarin babur

Tura Wannan Zuwa Ga

Yusuf Buhari, dan shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari ya yi mummunan hatsarin
babur din tsere a Abuja, babban birnin tarayyar
kasar.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar
shawara kan harkokin watsa labarai Garba Shehu
ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a unguwar
Gwarimpa da ke birnin ranar Talata da daddare.

A cewar Garba Shehu, "Ya karye a kafa sannan
ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika
an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja
amma yanzu yana samun sauki".

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Buhari da
mai dakinsa Aisha suna godiya ga 'yan Najeriya
bisa addu'ar da suke yi wa dan nasu.

'Ya'yan masu hannu da shuni kan yi wasan
tseren babura akai-akai a wani yanki na kwaryar
birnin Abuja, lamarin da ake gani na cike da
hatsari.

A shekarun baya, hukumar birnin tarayyar ta
haramta yin irin wannan tsere bayan wasu
rahotanni da aka samu na tukin ganganci da
masu tseren ke yi.

Karin Haske Akan Labarin da Shafin Al'umma ta Wallafa

Yusuf Buhari, da namiji daya tilo ga Shugaba
Muhammadu Buhari ya samu mummanan rauni a
kayinsa tare da samun karaye a bangarorin
jikinsa daban-daban bayan da hadarin mashin ya
rutsa da shi a daren jiya a Abuja
Majiya mai tushe ta tabbatarwa da jaridar DAILY
NIGERIAN cewa, hadarin ya afku a daren jiya a
lokacin da Yusuf ke tseren mashin din nan da ake
kira da Power Bike shi da wani abokinsa.

Sitiyarin mashin ya kwace a lokacin da Yusuf ya
yi yunkurin wuce abokin tseren nasa, inda daga
nan ne ya bar kan titi ya yi cikin dajin da ke
gefen titin ya kuma fadi ba cikin hayyacinsa ba
Wani makusancin gidan Shugaban Buhari wanda
ya nemi da kar a ambaci sunansa ya shaidawa
Daily Nigerian cewa, sai daga baya ne aka
sanarwa da mai dakin shugaban kasa, Hajiya
Aisha Buhari lamarin da ake ciki, inda nan take
ta bayar da umarnin da a kai shi asibitin
Cedarcrest inda a can ne yake karbar kulawa a
halin yanzu
Wata majiya a asibitin da Yusif ke kwance ta ce
“Mun fi damuwa da raunin da ke kansa sama da
karaya da ya samu”

“Alamu na nuna cewa za a fitar da Yusuf wajen
Nijeriya don samun kulawa daga kwararru”

Har zuwa lokacin da aka wallafa labarin nan, mun
kasa samun mataimaki ga shugaban kasa kan
harkokin yada labarai, Femi Adesina domin
samun tabbacin halin da Yusuf ke ciki

Source By ©Bbc Hausa and Al'ummata

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: