Monday 18 December 2017

Kalli Yadda Ta tsattsaga hannun ’yar kishiyarta da reza-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa

Rose James, matar da ta tsage hannun yarinya
da reza.

Wata mata da ta yi yunƙurin halaka ’yar kishiyarta
’yar kimanin shekara 8, ta shiga komar ’yan
sanda.

Al’amarin ya faru a Unguwar Onofowokan da ke
Ogijo a Jihar Ogun, inda matar mai suna Rose
James ta yi wa yarinyar mummunan yanka da
reza a sassan hannuwanta biyu.

Mijin matar mai suna Micheal James ne ya
ankarar da ’yan sandan yankin, inda ya shaida
masu cewa matar tasa ta kira shi ta wayar
salula a lokacin da yake wajen aiki, ta shaida
masa cewa ’yarsa Blessing ta doki ƙaramar ’yarta
har ta yi mata rauni a ƙafa; don haka za ta ɗauki
fansa.

Sai ya ce mata ta yi haƙuri har ya dawo
amma sai ta ƙi jin maganarsa. Koda ya isa gidan
sai ya tarar da cewa ta yi wa yarinyar munanan
raunuka a hannayenta da reza, inda nan take
kuma ya sanar wa ’yan sanda.

Ya bayyana cewa DPO na yankin, SP Tijjani
Muhammad ne ya jagoranci tawagar ’yan sandan
da suka kame wacce ake zargin, inda ta amsa
laifinta, cewa aikin Shaiɗan, wanda ya rude ta ga
aikata haka.

Tuni dai aka garzaya da yarinyar zuwa Asibitin
Lenard da ke Ogijo, inda likitoci ke kula da
lafiyarta, yayin da Kwamishinan ’yan sandan jihar
Ogun Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin tasa ƙeyar
wacce ake zargin zuwa Sashen yaki da cin
zarafin ɗan Adam da cutar da yara domin zurfafa
bincike.

Ya ce ko kaɗan rundunar ’yan sandan ba
za ta saurara wa masu aikata miyagun laifuka a
jihar ba.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin aiki Tukuru don jin dadin ku

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: