Monday 18 December 2017

Yadda gobara ta hallaka magidanci da matarsa da ’ya’yansa uku: Gawarwakin marigayi Adamu Yusuf da matarsa da yaransa guda uku

Tura Wannan Zuwa

Wani magidanci mai suna Malam Adamu Yusuf
da matarsa Maryam Abdu da ’ya’yansu uku Abdul
Adam mai shekara hudu da Ibrahim Adamu mai
shekaru uku da kanwarsu ’yar wata shida, sun
rasa ransu a gobarar da ta tashi a dakin da suke
kwance.

Wannan lamari mai ban tausayi, ya faru ne a
Layin Madaki da ke garin garin bukur a karamar
Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato cikin
dare a ranar Juma’ar da ta gabata.

Makwabtan marigayan, sun ce gobarar ta tashi
ne da misalin karfe 3:30 na dare a ranar Juma’ar,
bayan da aka dauke wutar lantarki.

Ana
tsammanin rawar da wutar lantarkin ta yi, kafin a
dauke ne ta haifar da tartsatsi a tsakanin
wayoyin wutar lantarkin da aka bar su a bude a
dakin, daga nan wutar ta tashi.

Wata makwabciyar dakin da wutar ta tashi, mai
suna Maryam Lawal da ta kubuta daga gobarar
tare da ’ya’yanta biyu, ta ce tana kwance sai ta
rika jin iska tana kada rufin dakin da take ciki.

Kuma tagar dakinta tana kadawa, sai ta rika
ganin hayaki na shiga dakinta, ta ce nan take ta
yi waje don ta ga daga inda hayakin yake fitowa,
inda ta yi ihu don ankarar da makwabta su fito
su ba da taimako.

Ta ce an yi duk kokarin da ya kamata don ganin
an balle kofar shiga dakin marigayin, don a fito da
Malam Adamu Yusuf da iyalansa amma abin ya
faskara, sai aka koma aka fasa bayan dakin,
amma kafin a kai gare su ta Allah ta kasance a
kansu.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kanen
mahaifin marigayin, mai suna Malam Ibrahim
Adamu ya ce suna kwance a cikin gida, sai suka
ji yarinya ta taho da gudu tana sallama tana
cewa su zo ga daki ya kama da wuta.

Da suka
zo sai suka tarar dakin a kulle da kyar suka samu
suka fasa dakin.

“Bayan da muka balle dakin sai
na shiga ciki, ina shiga sai na ga yaro daya ya
riga ya kone. Da na sake dubawa sai na gano
hannun kanwar yaron, na dauko ta na fito da ita.

Da na sake komawa cikin dakin, sai na gano
maigidan da uwargidan a jikin bangon dakin duk
sun rasu, da haka muka fito da gawarwakinsu su
biyar daga cikin dakin,” inji shi.

Malam Ibrahim Adamu ya ce bayan da suka fito
da gawarwakinsu sai aka kai su masallaci da gari
ya waye aka yi masu jana’iza.

“Mun mika
wannan lamari ga Ubangiji domin mun yi imanin
cewa Shi ne Ya kawo wannan lamari. Don haka
muna yi musu addu’ar Allah Ya gafatar musu,”
inji shi.

Mahaifin marigayin, Malam Yusuf Lantarki ya
bayyana matukar bakin cikinsa da aukuwar
wannan lamari, musamman ganin yadda ya shaku
da jikokinsa.

Ya ce yanzu ya rasa jikokinsa uku a
wannan gobara sai babbarsu Amina ta rage,
wadda a wannan daren ta kwanta ne a dakin
kakarta.

Ya ce babu shakka ya shaku da jikokin domin ko
a ranar da lamarin ya faru a gidansa suka wuni.

“Amma a matsayina na Musulmi na bar wa Allah
komai kan wannan lamari da ya faru.

Wannan
yaro nawa da matarsa da jikokina kwanansu ne
ya kare, kuma ni ma na san ko bade ko ba jima,

zan tafi wajen da suka tafi,” inji shi.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin aiki Tukuru don jin dadin ku

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: