Monday 18 December 2017

Labari KARANCIN MAI: NNPC ya fitar da gangan mai lita miliyan 50 domin rabawa a gidajen mai da kanshi-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa Ga

Hukumar kula da kamfanonin mai na Nigeria,
(NNPC) yace ya fara tura mai da rarraba shi awa
24 a ko ina domin kawar da wahalar mai da
dogayen layukan mai da ake fuskanta
musamman a Abuja, da Lagos da wasu jihohin
kasar nan.

Shugaban kula da mai na kamfanin NNPC Chief,
Dr. Victor Babatunde Adeniran, ne ya bayyana
haka a jiya Laraba lokacinda yayi rangadi a wasu
wajaje domin gani da ido kan karancin mai da
ake fuskanta a Abuja.

Yace bayan ganin halin da ake ciki yanzu
kamfanin ya yanke shawarar dibar man da kanshi
tare da rarrabashi a duka sassan kasarnan awa
24 ba kakkautawa don magance wahalar man
cikin gaggawa.

Yace an samu wahalar man ne sakamakon jita-
jita da wasu suka rika yadawa cewa ana shirin
kara kudin farashi Man. Yace yan Nigeria suyi
watsi da zancen domin bashi da tushe bare
makama

Hausa Times ta ruwaito Daraktan mai na
kamfanin, NNPC, Mr. Umar Ajiya din yana bayanin
cewa a jiya Laraba kadai sai da suka dibi gangar
mai Lita miliyan 50 domin rarrabawa

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source: ©Hausa Times

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: