Wednesday 20 December 2017

KARANTA LABARIN SOYAYYAR KHALIFA DA SAUDAT - LABARI MAI TABA ZUCIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa
Assalamu’alaikum Abokaina Maza Da Mata A
Yau Na Sake Zuwa Muka Da Wani Sabon Labarin
Soyayya Mai Dauke Da Abin Al’ajabi da Tausayi
Acikin Sa.

khalifa da Saudat sun fara soyayya tun a
makaranta ne inda daga baya har iyayen su suka
san suna soyayya.Khalifa da Saudat sunyi matukar shakuwa da
juna sosai,domin kusan duk kowane lokaci a tare
zaka gan su,ko makaranta ko a kasuwa basu
yarda su rabe sai dai kwanciya da raba su.
Wasu Lokuta hatta da hutun makaranta idan aka
basu,tsabar soyayyar dake tsakanin su a tare
suke ida hutun makarantar.

A Soyayyar dake tsakanin Khalifa da
Saudat,soyayyarSaudat tafi karfi sosai
Saudat tana matukar masifar san Khalifa aranta
tamakar ace ta bashi zuciyar ta.
Aduk Lokacin da Saudat da Khalifa suka rabu
makaranta bayan an tashi,ko minti 2 ba;ayi da
rabuwar su Saudat zata fara turawa Khalifa da
sakonnin soyayya da kalamai masu dadi.
Sai dai kuma shi Khalifa baya san wannan hali na
Saudat na yawan tura masa sakonni da kira koda
yaushe,harma yana ganin cewa kamar hakan
takura masa take yi.

Akullum sakonnin Saudat a wayar Khalifa basu
wuce wadannan kalmomi kamar haka..:

“INA SANKA”
“INA KAUNARKA”
“INA BEGENKA”
“INA KEWARKA”

Wadannan sune mafi yawan sakonnin kalaman
soyayya da Saudat take yawan turowa Khalifa
Kullum.

Watarana da daddare Khalifa ya kwance akan
gado, sai yaji wayar sa tayi kara alamar shigowar
sabon sako a wayar sa,sai dai a wannan lokacin
Khalifa bai duba sakon ba,balle ko zai iya sannin
waye ya turo saboda alokacin shi bacci ne kawai
a gaban sa.

Khalifa ya share ya jayo bargon sa ya lulluba
abun sa,ashe Saudat ce take turo masa sako shi
kuma saboda da dabi’ar sa haka take bai damu
ba,bayan Khalifa yayi bacci sakonnin Saudat sun
cigaba da tururuwar shigowa wayar sa babu
adadi har ta gaji ta daina.

Washe gari da sassafe Khalifa yana kwance ko
farkawa baiyi daga bacci ba,sai can yaji an kira
wayar sa,bayan Khalifa ya farka daga bacci yayi
yunkura zuwa kan wayar sa don ya duba wanda
ke kiran sa, ashe mahaifiyar Saudat ce take kiran
Khalifa.

Bayan Khalifa amsa kiran Mahaifiyar Saudat sai
yaji ta fashi da kuka,sannan can cikin wata
tattausar muryar mai cike da tausayi da kashe
jiki,Mahaifiyar Saudat ta fara fadawa Khalifa
Abinda yake faruwa kamar haka:….
” Mahaifiyar Saudat ta cigaba da cewa Khalifa
daman nakira ne in fada maka cewa Allah yayi
wa budurwarka Saudat Rasuwa sanadiyyar
hadarin mota akan hanyar ta dawo daga wajen
sayayya a kasuwa,mota ce ta kade ta kan titi
sannan mai motar bai tsaya ba, sannan babu
kowa a wajen gashi kuma lokacin mahaifin ta
baya kusa balle yayi kokarin ceton rayuwar
ta,sannan lokuta kadan da faruwar hakan ALLAH
yayi mata cikawa ”

A wannan daren da Saudat ta turowa Khalifa
sako a waya,ashe daman a lokacin tana bukatar
taimakon sane,amma shi kuma yaki duba sakon
balle ya karanta.

Jin haka yasa Khalifa yayi matukar firgita acikin
dan takaitaccen lokaci bayan Mahaifiyar Saudat
ta gama fada masa abinda ya faru,Khalifa ya
tuna da lokacin da sakonnin Saudat keta shigowa
wayar sa.

Nan take Khalifa yayi hanzari ya ciro wayarsa
daga cikin aljihun sa,ya bude ‘INBOX’ nashi
sakon farko da Khalifa ya fara cin karo dashi da
Saudat ta turo masa shine kamar haka…!

” Masoyina Dan Allah Kazo Ka Taimake Ni Ina
Cikin Matsanancin Hali,Mota ce Ta Kade Ni Nan
Kusa Da Gida Amma Gashi Babu Kowa Da Zai
Taimake Ni GashiI Kuma Mai motar Ya Gudu ”

Bayan Khalifa ya gama karanta sakon kawai sai
ya fashe da kuka nan take idanuwa sa suka kade
sukayi ja jajir,tamkar wanda aka sanya wa
barkono a ido.

Sai dai kuma kash!! kukan da Khalifa yake kuka
ne mara amfani saboda Saudat ta riga tabar
gidan duniya.
Yakai mai karanta wannan labari kasani cewa a
rayuwa Allah ne yake chusa soyayyar wani acikin
zuciyar wanda yaso,saboda haka a rayuwa kada
ka taba wulakanta mutumin dake kaunarka
aransa sannan kuma ya damu dakai,saboda
watarana zaka fara kirga rashin sa kusa dakai
kamar yadda kake kirga kwanakin wata ko
shekara.

Alhamdulillahi Anan labarin Soyayyar Khalifa da
Saudat yazo karshe,Allah ka bamu ikon riko da
soyayyar masu son mu da gaskiya ameen.

DAGA NAKU HARUNA SP
DANSADAU,WHATSA
PP LAMBA 07035169818.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


FARIN CIKIN KU SHINE FARIN CIKIN MU

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: Mujallar Mu and Muryar Hausa24

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user