Sunday 17 December 2017

Karanta Wannan Muhawara- Kora Da Aka Yi Wa Firdausi Don Saka Hijabi ko me ye dalili???

Tura Wannan Zuwa

Firdausi Amosa daliba ce da ta karanci dokoki
watau Law kuma ta kwashe shekaru shida tana
karatun wannan fanni sai dai a ranar karshe
wajen tabbatar da ita a matsayin Lauya an kore
ta saboda rufe kanta da ta yi.

Sun bukaci ta cire dankwalin kanta ko hijabi
kamar yadda sauran mata Musulmi suka cire
kafin su shiga dakin tabbatar da su amma
Firdausi wacce shugaba ce ta kungiyar mata
Musulmi ta jami'arsu ta Ilorin ta ce, kai da fata
ba za ta cire abinda tun ta ke karama ta ke sa
wa ba.

Manya da sauran 'yan'uwanta Musulmi duk sun
taru ana ba ta magana kan kar ta yi asarar
shekaru shida da ta yi a jami'a amma Firdausi ta
sa tsakuwa a baki ta ce in duniyar nan za a ba
ta don ta cire hijabinta ba za ta cire a ga mata
gashin kai ba.

A yayin da aka hana ta shiga sai abin ya jawo
cece-kuce, wasu har da Musulmi 'yan'uwanta
suna zaginta a kan ta cika tauri kai da
tsautsauran ra'ayi inda aka yi ta zaginta.

Wasu kuma har da mahaifinta da wasu abokansa
wadanda masu ilimi ne har matakin dakta da
lauyoyi sun ce ta yi musu daidai inda mahaifin
nata ya ce haka ya ba ta tarbiya.

Ya ce bai damu ba don ta rasa shekaru shida a
jami'a in dai saboda kare mutuncinta ne ko hijabi.

Rubutawa ©Mairo Muhammad Mudi

Ban Ji Dadin Korar Dalibar Lauya Da Aka Yi Ba

Daga ©Abdullahi Muhammad Maiyama

Zahirin gaskiya, bayanin da wasu kafafen yada
labarai suka dinga fitarwa, na korar dalibar lauya
ya yi matukar girgiza ni da kuma bata min rai.

Duk da cewa yarinyar nan ban san ta ba, amma
gaskiya na ji takaicin lamarin da ya faru da ita!

Ya kamata mu sani cewa kowa yana da damar
saka suturar da ya ga dama, kamar yadda
Kiristoci suke fito da gashin kansu waje,
Musulmai ma suna da damar rufe gashin kansu,
da dukkan jikinsu kamar yadda addinin Musulunci
ya tanada.

Nijeriya kasa ce da ta bai wa kowa damar yin
addininsa, ba tare da muzgunawa ba, a wani
mataki na kawo daidaito da zaman lafiya.

Godiya ta tabbata ga mahaifin Firdausi, wanda ya
jajirce tun tana karama don ganin ya bata
wannan kyakkyawar tarbiyya.

Sannan jinjina zuwa ga Firdausi, wacce daliba ce
kuma ta nuna dattako, da kuma yin aiki da
abinda addinin Musulunci ya tanada.

Shawarata zuwa ga Firdausi ita ce, shakka babu
kin yi kokari, wurin bijirewa maganar mutane na
cire dan kwalinki.

Wannan babbar alama ce da ta
nuna matsayinki, da tarbiyya, da kuma aiki da
abinda ki ka karanta a musulunce.

Zan so iyayenki, da ke kanki ku kara zage
damtse wurin kara baki tarbiyya ta gari, ke kuma
zan so ki kara zage damtse wurin aiki da
kyakkyawar tarbiyyar da iyayen ki suka baki.

Ta
haka ne za ki cimma burinki a rayuwa.

Allah ya kara daukaka addinin Musulunci da
Musulmai baki daya. Allah ya kara dora
Musulunci kan kafirci.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin aiki Tukuru don jin dadin ku

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: